Google69490f6862051cb8
google-site-verification: google69490f6862051cb8.htmlgoogle-site-verification: google69490f6862051cb8.htmlgoogle-site-verification: google69490f6862051cb8.htmlBasheer journalist sharfadi14

Basheer journalist sharfadi14.jpg6
Basheer journalist sharfadi 11 1
Maraba Da Zuwa Wannan
Shafi Mai Al-barka 1

☀ Zabi inda kake son shiga ☀
Menunks
→Home
→Akidojin Ahlussunnah
→Addinin musulunci (35)
→40 Hadith (50)
→Fadakarwa (120)
→Neman labarai (20)
→Shi'a Kafirci (50)
→Hadith (55)
→Khudubobi (24)
→Tarihin magabata (60)
→Raddi / Maida martani (99)
→Face book post (30)
→Monthly Archives (60)
→Tambaya da Amsa (20)
→Sahabban Annabi {s.aw} (50)
→Taskar maluman sunnah (25)
→Akidar Y'an Shi'a Dangane da Al'kur'ani
→Fassarar Usulussunnah (20)
→Sheik Ja'afar {Rahimahullah} (65)
→Sheik Abubakar Gumi {Rahimahullah} (30)
→Sheik Dr. Muhammad Sani R/Lemo
→Salafiyyah Network Nigeria (100)
→Adam Sani Abu-Umayrah (99)
→Salaf Ustaz (79)
→Malama Ummi Ahmad Katsina
→Malama Amina Saleh Mande
→Labarai (40)
→Nishadantarwa (10)
→Siyasar Nigeria (9)
→Vidio (33)
→Audio (66)
→Hotuna (120)
→Internet Cheat (90)
→Site Achieve
→Application (10)
→Games (8)
→About me (01)

Wannan shafin mallakarCoollogo com-1281358 3
Ne




SHAFI DON KARUWAR MUSULMI
"SARKIN MUMINAI MU'AWIYYA BN ABI SUFYAN [RA]"

Ya Musulunta kafin Fathu Makkah ,amma ya boye Musuluncin sa saboda tsoron Mahaifinsa.
Mu'awiyya na daya daga cikin sakatarori [marubuta] na Annabi[SAW]masu rubuta masa wahayi. Kai kasan koda a ma'aikatar ku akace wane sakatare ne to lalle yanada daraja, balle Fada irinta Annabi[SAW]wadda kaf duniya babu irinta.Ya kuma samu kyakkyawar addu'a a dalilin kokarin sa inda Annabi[SAW] ya roka Masa Allah ya sanya shi shiryayye mai shiryarwa.
Mu'awiyya na daga cikin mayakan Hunaini wanda Allah ya shede su da imani kuma ya ba da sanarwar saukar da nutsuwa a kansu a cikin Taubah 91. Yana kuma cikin mutanen da Allah ya yi wa alkawarin Al Husna wadda itace Aljanna saboda sun ciyar da dukiya saboda Allah bayan cin garin Makka. Ya kuma samu martabar kasancewa shugaba na farko da ya kaddamar da Jihadi a teku, kuma Annabi [SAW] ya yabama wadanda zasu yi yaki a teku, yayi murna da Allah yanuna masa su zazzaune kamar sarakuna a kan gadaje.

Zamu cigaba.
Umar Lajin Kofar wambai
19-4-2015

"JARUNTAKA DA SARAUTA A RAYUWAR MU'AWIYAH [RA]"

Bayan Musuluntar Mahaifinsa Abu Sufyan iyalan gidansu sunyi hijira tare dashi zuwa Madina wurin Annabi [SAW]. Don haka Mu'awiyah ya samu halartar sauran yake-yaken da suka biyo baya.
Game da sha'anin sarauta Mu'awiyah ya dade da tunaninta a ransa tun ranar da Annabi [SAW] ya ce masa, ya kai Mu'awiyah! Idan ka Jibinci wani Al'amari kaji tsoron Allah kuma kayi adalci.
Mutum na farko daya gabatar da Mu'awiyah a sha'anin Mulki shine Khalifa Abubakar Siddik a lokacin daya shugabantar dashi akan wata runduna da zata kai gudummawa ga dan uwan sa Yazid, daya daga cikin jagorori 4 da suke yaki a kasar Sham.
Mu'awiyah ya cigaba da yaki a karkashin tutar dan uwansa in da bajintar sa tasa aka rinka shugabantar dashi akan kananan rundunoni yana cin nasara. Daga baya a zamanin sarkin Musulmi Umar Bn Khaddab aka ba Yazidu umarni ya shugabantar da kanin nasa don cin garin kaisariyyah, ya tafi kuma Allah yabashi nasara a can.

Zamu cigaba.
Umar Lajin kofar wambai
21-4-2015

"AYYUKAN SA A ZAMANIN SARAUTAR SA SARKIN MUMINAI MU'AWIYAH [RA]"

Sarkin Musulmi Mu'awiyah ya kula sosai da sha'anin tsaro a kasar musulunci, shine shugaba na farko a musulunci da ya fara sa matsara a dalilin yunkurin kisansa da khawarij sukayi. Yakuma kafa ma'aikatu da dama don cimma wannan manufa. A dalilin haka gwamnatinsa ta samu karfinda yasa tazamo babbar barazana ga duk sauran al'ummai na duniya a wannan lokaci.
Sannan shi ya fara kafa ma'aikatar kula da wasikun Sarki don gudun kar a sauya su.
Haka kuma Mu'awiya ya kula da sha'anin ilimi da jin dadin Malamai. A kan haka ne ya kafa cibiyar nazari da fassara wadda aka bata suna Baitul Hikmah. Ya kuma mayar da hankali ga inganta rayuwar talaka. Haka kuma ya mayar da hidimar alhazai kyauta.
A zamanin sa ne kuma yasa akayi magudanan ruwa a Madina, abinda yakawo karshen matsalar cushewar ruwa musamman a lokacin damina a cikin garin Madina a wancan lokaci.

Zamu cigaba
Umar Lajin Kofar Wambai
22-4-2015



SUHAIBUR RUMIY[RA]
.
.
Ya Musulunta tun da wuri, yana cikin wadanda aka dandana musu azaba saboda imaninsu ga Allah[SWT].
Suhaib sun Musulunta rana 1 da Ammaru.
.
Ammaru yace, "Wata rana na hadu da Suhaib a kofar gidan Arkam bn Abul Arkam, a lokacin Annabi[SAW] yana ciki, sai nace masa, "Me kazo yi? Sai ya amsa mini da cewa, "kai me kazo yi? Sai na ce, Nazo da nufin shiga wajen Muhammadu, sai Suhaib yace, Nima hakan ne ya kawo ni". Sai muka shiga wajen Annabi [SAW], Sai ya bijirar mana da musulunci. Sannan muka zauna a gidan har yamma tayi. Sannan muka fito muna boyewa domin tsoron mushrikan Makka.
.
Lokacin da zai yi hijra, mushrikai sun tsare shi cewa bazai yi hijrar ba sai ya bar dukkan dukiyarsa, sai kuwa yabasu dukkan abinda ya mallaka.
.
An ruwaito shi yana cewa, "Annabi [SAW] bai taba halartar wani guri ba sai na kasance na halarce shi, ban taba ganin wani abin tsoro a gaban sa ko bayansa ba sai na kasance na kare shi".
.
ALLAHU AKBAR
.
Ya Allah ka kara yarda da aminci ga Sahabbai.



ABDULLAHI BN MAS'UD [RA]
.
Yana cikin wanda suka fara musulunta tun kafin Annabi[SAW] ya shiga gidan Arkam bn Abul Arkam, sababin musuluntar kuwa shine a lokacin da yake kiwon dabbobi ne a Makka Annabi [SAW] yazo wucewa shida Abubakar [RA], sai ya tambaye shi yabasu nono. Sai yace,
.
"Dukkan dabbobin basu da nono". Sai Annabi [SAW] ya sanya hannun sa ya ambaci sunan Allah take nonon ya bulbulo, dukkan su suka sha suka koshi.
.
Wannan abu da Abdullahi ya gani sai mamaki ya rufe shi, ya ce da Annabi [SAW]
.
"koya min abinda ka fada haka ta kasance".
.
Sai Annabi [SAW] ya koyar dashi surori 70 daga bakin sa.
.
Yayi hijira sau 2, ya halarci yakin Badar da dukkan yakoki tare da Annabi[SAW].
.
Yana cikin manyan hadiman Annabi [SAW].
.
Shine gaba da kowa wajan iya karanta alqur'ani.
.
Shine Mutum na farko daya fara bayyanar da karatun alqur'ani a fili a gaban mushrikan Makka.
.
A zamanin Umar [RA] ya turashi kufa domin ya dinga karantar dasu alqur'ani da hukuncin shari'a.
.
Allah yakara masa yarda



SA'AD BN ABI WAKKAS
.
Yana 1 daga cikin wanda suka fara karbar musulunci,
.
kuma yana cikin mutane 10 da aka yiwa bushara da aljannah tun a duniya, kuma 1 daga cikin mutane shida masu zaben khalifa, kuma 1 daga cikin yardaddu a wajen Annabi [SAW].
.
Ya halarci yakin Badar da dukkan yakoki tare da Annabi [SAW].
.
Yana cikin jarumai maharba na Annabi [SAW], Shine ya fara harba kibiyar sa saboda Allah.
.
Annabi [SAW] yayi masa addu'ar dacewa a duk lokacin da yayi harbi,da kuma amsawar addu'a a wurin Allah, yace,
.
"Ya Ubangiji ka datar da harbin sa, kakuma amsa addu'ar sa".
.
Sa'ad shine ya jagoranci musulmi a zamanin khalifancin Umar wajen rusa Daular Farisa, shine ya bude babban birnin Farisa Mada'in, yakuma kafa garin Kufa.
.
Sa'ad yayi rayuwa mai tsawo cikin tsananin biyayya ga Allah da gudun duniya, ance shi mutum ne mai tsananin tsoron Allah da yawan kuka musamman ma idan Annabi [SAW] yana yimusu huduba da wa'azi.
.
Ya Allah ka kara masa yarda da aminci bisaga aikin da yaiwa musulunci.



ABUBAKAR AS-SIDDIK
.
kashi na 1
.
An haifi Abubakar As-siddik a garin Makka. Yataso cikin nagarta da kyawawan halaye,tarihi yanuna tunda yake baitaba yin sujjada ga gunki ba,
.
kuma baitaba shan giya ba tun a Jahiliyya.
.
Lokacin da Manzon Allah (SAW) ya bayyana kiran musulunci shine mutum na farko daya fara karbar musulunci,
.
wannan kuwa bai rasa nasaba da aminci da kyakkyawar dangantaka da alakarsa da Manzon Allah (SAW).
.
Tun bayan daya amsa kiran musulunci,sai ya mika rayuwar sa da duk abinda ya mallaka wajan cigaban musulunci.
.
Babu tantama cewa Abubakar shine mafificin dukkan Sahabban Manzon Allah (SAW) kamar yadda Aliyu dan Abi Dalib ya tabbatar.
.
Kasancewarsa hamshakin attajiri, ya saukakawa addinin musulunci ta hanyar bayar da dukkan abin daya mallaka wajen ganin yunkurawar addinin musulunci.
.
Manzon Allah (SAW) yana cewa,
.
"Babu wata dukiya data amfane ni, kamar yadda dukiyar Abubakar ta amfane ni".
.
Cikin halin takura da aka jefa raunanan musulmi musamman bayi na cutarwa da gallazawa.
.
Zamu cigaba



AL-HASSAN BN ALIYU
.
Mahaifiyar sa itace Fadimatu 'yar Annabi [SAW]. Yayi kama da Annabi [SAW].
.
Haka kuma shi da dan uwansa Hussain Annabi [SAW] yafiso cikin jikokin sa.
.
An ruwaito daga Usamatu dan Zaid yace: Annabi [SAW] yana cewa,
.
"Alhassan da Hussain jikoki nane ya Ubangiji ni ina sonsu, kaima kaso su, kaso dukkan mai sonsu".
.
Alhassan ya kasance kyakkyawa ne kuma mai kyawun hali.
.
Yayi kyakkyawar rayuwa yana tare da Annabi [SAW] har yayi wafati, bayan wafati ya kasance tare da khalifofi.
.
Yana cikin wadanda suka kawo dauki domin kare Khalifa Usman lokacin da makiya suke kokarin kashe shi.
.
Haka kuma ya kasance tare da Baban sa a matsayin mashawarci.
Anyi masa mubayi'a a matsayin Sarkin Muminai, amma bayan kankanin lokaci sai ya kirawo Mu'awiyya Bn Abu sufyan yabashi jagorancin musulmi.
.
Wannan kuwa gaskata fadin Annabi [SAW] ne da yake cewa
.
"Lalle wannan jika nawa shugaba ne kuma ina fatan ta dalilin sa Allah zai sulhunta wasu bangarorin musulmai masu girma".
.
Allah ka kara masa yarda.



AL-HUSSAINI BN ALIYU
.
Shima dai kamar dan uwansa yayi kama da Annabi [SAW].
.
Hussaini da dan uwansa sun sami albarkar kasancewa Sahabban kakansu duk da suna yara yabar duniya. Haka kuma Abubakar, Umar da Usman suna girmama su da kuma nuna tsananin soyayya a garesu.
.
Bayan rasuwar Mu'awiyya, aka yiwa dansa Yazid mubayi'a. Wanda a wannan lokaci Hussaini bai amince ba. A wannan lokaci sai mafi sharrin wannan al'umma mutanen kufa suka yi ta yimasa wasiku suna kiransa yazo su yimasa mubayi'a. Da farko yaki amincewa saboda 'yan uwansa da kuma wasu daga cikin Sahabbai suka hanashi. Amma daga baya suka yaudare shi yaje.
.
Daga karshe dai sun kashe shi Hussaini, yayi shahada a karbala kasar Iraki, ranar Ashura goma ga watan Muharram.
.
ABIN LURA ANAN:
Annabi [SAW] bai ware wani daga cikin jikokin nan nasaba da yafi so, dukkan su yanuna musu soyayya ba bambanci, hakama Sahabban sa sun so su. Bakamar yarda wasu sukafi nuna soyayyar su ga Hussaini ba.
.
Ya Allah ka kara musu yarda da aminci.



MUS'AB BN UMAIR
.
Ya taso a cikin jin dadi, gashi dan gata kuma kyakkyawa mai iya ado, dukkan wani taro baya cika idan babu Mus'ab a cikinsa.
.
Yana cikin wannan hali ne ya sami labarin kiran musulunci ta bakin amintacce Muhammadu[SAW],bai yi jinkiri ba wajen amsa kiran duk da sanin irin matsin da zai fuskanta.
Mus'ab ya hakura da dukkan jin dadin duniya, ya maye shi da dandanar kuda da azabtarwa daga mutanensa.
.
Wata rana mus'ab ya taho gurin Annabi [SAW] sahabbai sun kewaye shi, lokacin da suka hango Mus'ab sukaga irin halin da ya shiga na kunci da takura sai suka sunkuyar da kawunan su suna kuka saboda tausaya masa.
.
A ranar yakin Badar shine yake rike da tutar Annabi [SAW] babbar ta Muhajirun hakama a yakin Uhudu inda a ranar yai shahada.
.
An ruwaito Annabi [SAW] ya tsaya a gaban Mus'ab da sauran wanda sukai shahada a Uhudu yana cewa:
.
"Lallai zanyi muku shaida cewa ku shahidai ne a gurin Allah ranar Alkiyama".
.
Ya Allah ka kara yarda da amincinka a garesu



SALMANUL FARISI [RA]
.
Ana kiransa Salmanu bnil Islam, ana kuma yimasa lakabi da Salmanul Khair, ana kuma yimasa alkunya da Abu Abdullahi.
.
Asalinsa Mutumin Asbahan ne ta kasar Farisa. Ya sami labarin za a aiko Annabi [SAW], sai yayi shiri ya fita nemansa, domin ya kasance cikin wadanda suka yi Imani dashi.
.
A hanya ne wasu suka sayar dashi a matsayin Bawa, bayan tsananin wahala da yasha har yazo Madina.
Ya sadu da Annabi [SAW] daf da lokacin yakin khandak, ya halarci yakin, shine ya bawa Annabi [SAW] shawarar a haka ramin gwalalo domin hana kafirai haurowa su shigo Madina.
.
Ya halarci dukkan yakokin da suka biyo bayan Khandak. Khalifa Umar [RA] yanada shi Gwamnan Birnin Mada'in.
.
Abu Burdah ya ruwaito daga Baban sa cewa, Annabi[SAW] ya ce,
.
" Lallai Allah yanason mutum 4 daga Sahabbai na daga cikin su akwai Salmanu".
.
Mutum ne shi mai tsananin tsoron Allah da gudun duniya da kaifin kwakwalwa, tsantseninsa kuwa ana kwatantashi da Khalifa Umar [RA].
.
Allah yakara masa yarda da aminci.





Koma saman shafi

→Labarai

WAI ZA'A KAWAR DA KABARIN MANZON ALLAH???

WAIwannan zancen ya game kafafen yanar gizo cewa gomnatin kasar saudiyya tana shirin kaurar da kabarin fiyeyyen halitta daga inda yake zuwa gefen masallacin!!..
.
wannan zancen KARYANE..zancenya samo asali ne daga jaridar Independent ta Burtaniya..duk daga nan aka samu labarin..ita kuma jaridar ta samu labari ne daga wassu 'YAN SHI'A 'yan asalin kasar saudiyya..Makaryata..wadanda basa jin kunyan karya..kuma basu tunanin cewa ba kowane wawa ba..
.
Hukumomin kasar saudiyya sun tabbatar da karyar wannan labarin, kuma sunce kabarin manzon Allah s.a.w yana nan a yanda yake har ranan kiyama, kuma kungiyar Tarbiyya da Ilmi da wayewa ta duniya (ISESCO) ta nemi cewa lallai kasar saudiyya karta yadda ta bar wannan babban kazafi da jaridar ta mata tare da hadin bakin 'yan shi'an.
Mukam ai an shamu mun warke game da sanin karairayin 'yan shi'a, wadanda suka dauki karya a matsayin addini..don haka jama'a sai muyi hattara wajen yada labarin da bamu da tabbas a kansa..Allah ka mayar musu da sharrinsu kansu ka hada kan musulmi.

Back to posts
Comments:
[2016-09-15 12:35:44] Allah Kasa Mudace :

Daga Abdullahi Muhammad

[2016-12-27 12:23:43] Zubairu sale lawan :

09075176846

[2017-04-30 14:32:29] usama magani soro :

abindabazaiyobanedomin allah baze bariba


UNDER MAINTENANCE

Share|

Kaima shiga a tattauna da kai
* No boards.

Online: Guests: 1


→Ra'ayin jama'a game damu

 IDAN KANA BUKATAR A TALLATA MAKA HAJAR KA A WANNAN SHAFIN DA SAURAN SHAFUKAN MU KANA IYA TUNTUBAR MU TA WADANNAN HANYOYIN KAMAR HAKA:


Email: bjournalist55@hotmail.com

Phone No: 09035830253

Facebook: Basheer Journalist Sharfadi

Address: Ittihad Computer Centre,  No 92 Daneji Kano


MAI TALLA SHI KE DA RIBA


*Bayanan ka*
Browser din da ka hawo Mozilla

Kasar da kake United States

Adadin Maziyarta 318208

Adadin Wadanda Sukayi Comment 65691

A Wadanda Suka Shiga Tattaunawar Mu 54


Follow @bjournalist55
→Yi Adding Dina Ta Facebook
→Yi Like Na Dakarun Sunnah Page
→Yi Like Dina Ta Facebook

*Shafuka Masu Alaka Da Mu*

→Basheer Sharfadi wordpress
Basheer Sharfadi Blog Spot
UP
→Home

Basheer Journalist Sharfadi (Abu Hafsah)
ISLAMIC DATE
  • phpimg2.php?it&ic=yellow



  • Click to Sms
    Click to Call


    Basheer journalist sharfadi3
    Coollogo com-1281358

    pacman, rainbows, and roller s