Snack's 1967
Google69490f6862051cb8
google-site-verification: google69490f6862051cb8.htmlgoogle-site-verification: google69490f6862051cb8.htmlgoogle-site-verification: google69490f6862051cb8.htmlBasheer journalist sharfadi14

Basheer journalist sharfadi14.jpg6
Basheer journalist sharfadi 11 1
Maraba Da Zuwa Wannan
Shafi Mai Al-barka 1

☀ Zabi inda kake son shiga ☀
Menunks
→Home
→Akidojin Ahlussunnah
→Addinin musulunci (35)
→40 Hadith (50)
→Fadakarwa (120)
→Neman labarai (20)
→Shi'a Kafirci (50)
→Hadith (55)
→Khudubobi (24)
→Tarihin magabata (60)
→Raddi / Maida martani (99)
→Face book post (30)
→Monthly Archives (60)
→Tambaya da Amsa (20)
→Sahabban Annabi {s.aw} (50)
→Taskar maluman sunnah (25)
→Akidar Y'an Shi'a Dangane da Al'kur'ani
→Fassarar Usulussunnah (20)
→Sheik Ja'afar {Rahimahullah} (65)
→Sheik Abubakar Gumi {Rahimahullah} (30)
→Sheik Dr. Muhammad Sani R/Lemo
→Salafiyyah Network Nigeria (100)
→Adam Sani Abu-Umayrah (99)
→Salaf Ustaz (79)
→Malama Ummi Ahmad Katsina
→Malama Amina Saleh Mande
→Labarai (40)
→Nishadantarwa (10)
→Siyasar Nigeria (9)
→Vidio (33)
→Audio (66)
→Hotuna (120)
→Internet Cheat (90)
→Site Achieve
→Application (10)
→Games (8)
→About me (01)

Wannan shafin mallakarCoollogo com-1281358 3
Ne




SHAFI DON KARUWAR MUSULMI
Assalamu Alaikum wannan 6angare ze dinga zuwa muku kai tsaye daga dan uwan ku
Adam Sani Abu-Umayrah
Kuna iya binsa ta face book

Wanda ya tsara ya kuma shirya
Basheer journalist sharfadi
Asha karatu lafiya

→DUNIYAR MUTUWA (16)
→WA YA KASHE HUSSAIN r.a??
→DA GASKENE WAI BA'A SAUKAR DA QUR'ANI BA DON A HADDACE SHI BA?

**HAQIQA NA TSORATA** (Adam Sani Abu-Umayrah

A tsakar bincikena da nakeyi, yau na bude littafin MA'ARIFATUS-SAHAABAH na ibn Mundah, haqiqa na matuqar tsorata zuciyata ta kadu sosai da naga wani Hadisi na Saalim Maulaa Abi-Huzhaifah r.a, Saalim yake cewa:
Manzon Allah s.a.w yace:
"Wasu Mutane daga Al-Ummata zasu zo ranar Qiyaamah da ayyukan qwarai (yawan ayyukan nasu) kamar girman duwatsun Tihaamah ne, idan sukazo (filin hisaabi) sai Allah ya maida ayyukansu iska (ya laalata su). Saalim Yace: Fansanka Uwata da Ubaana ya Manzon Allah, ka Siffanta min su, domin naji tsoron kada na zamo daga cikinsu! Sai Manzon Allah s.a.w yace: Yaa Saalim: "Haqiqa sun kasance suna Sallah, Suna Azumi, suna Tsayuwar dare, sai dai a duk sanda #‎wani_abu_na_Haraamun‬ ya bijirowa dayansu, sai su afka masa, sabida wannan ne Allah ya sanya Ayyukansu a banza!!!!!!". ((Ma'arifatus-sahaabah ta ibn Mundah:1:716)).
Yan uwa abin kunsan Abin Tsoro anan? Shine fadin Manzon Allah s.a.w: "Haqiqa sun kasance suna Sallah, Suna Azumi, suna Tsayuwar dare, sai dai a duk sanda #wani_abu_na_Haraamun ya bijirowa dayansu, sai su afka masa".
Wannan fa ya hada duk wani abu da kukasan Allah ya Haramta shi, shin abinnan na ci ne, ko gani, ko magana, ko na saurare, ko tabawa, ko aiki! Duka yana qarqashin Haramci dai, idan na duba yanda ayau muke haba-haba da HARAAMUN muke bin Haram muna nemanta ido rufe, ruwa a jallo, sai inga to ya zamu zamo a filin qiyaamah? Qarin abin haushin ma, mu Bama aikin Qwarai, Sallar ma bayinta mukeyi yadda ya kamata ba, balle azumi, Balle Uwa-Uba QIYAAMUL-LAYLI! To kunga mu abin ya mana yawa, babuma aikin balle a laalata su bare har su zamo a banza!
Allah ya shiryar damu ya bamu ikonm gyarawa!


**MAHAIFAN ANNABI s.a.w** (1)

Assalamu alaikum, Yan uwa barkanmu da saduwa a wannan lokaci, haqiqa banso magana ba akan wannan Mas'alar, Allah ya sani, ina guje mata, to amma an tambayeni ne, kuma ya wajaba na bada Amsar abinda na sani, idan kuwa ban sani ba ince ban saniba, wannan ba laifi bane!

Dayawa daga Yan'uwa sukanyi tambaya kan abinda bashida Amfani garesu, maimakon suyi qoqarin kansu, sai sukoma neman wasu! Wannan haqiqa kuskure ne!
Ribar me zaka samu in kasan iyayen Annabi s.a.w suna wuta ko aljannah? Asaarar me zakayi? Me zai hana kai kayi qoqarin shiga Aljannah ka dena hangen wasu?

Kamar yanda na muku tsokaci a jiya, wata Baiwar Allah ta turon da Tambaya gameda Mahaifan Annabi s.a.w, inda tace taji wani Malami an tambayeshi, yace suna cikin wuta! Sai abin ya daure mata kai, shine sai ta turomin take Tambayata dagaskene hakan ne??

Alokacin sai nace mata Haka dai wasu daga magabata sukace, wasu kuma sukace A'A BASA WUTA, kuma a gaskiya ina tare dasu, Nafi yarda da Maganar masu cewa IYAYEN ANNABI S.A.W basa wuta! Kamar yanda nace:

Magabata a wannan Fatawar sun kasu gida 2 ne:

1: Daga Cikin masu cewar Iyayensa suna wuta, akwai: Imam Muslim, Ibn Maajah, Abu Dawud, Ibn Kathiyr, Ibn Jariyr Attabariy dasauransu.

2: Daga cikin masu cewar Iyayensa basa wuta akwai su Imamus-suyuwtiy, Imaamus-suhayliy, Imaam Fakhruddiyn Arraaziy, Shaikh Dr. Muhammadul Amin Ash-shanqiytiy dasauransu!.

Abinda ya kamata sauran Yan'uwana Almajirai da Malamai su Fahimta, wannan ba Mas'ala bace da Yan Izaala suka Qirqira, kamar yanda Dayawa ke cewa, sai dai, Wannan Matsala ce da tun a Zamanin Tabi'ai ake fama da ita, kuma hakan yasamo ne daga sabanin Fahimta, maganganu masu yawa sun gabata akan haka, da kuma hujjoji daga kowanne bangare!

Dukda haka basu kafirta junansu ba,don wannan ba Matsala bace ta kafirta juna ku Muzanta juna, matsalace mai sauqin warwarewa idan aka bita a ilmance kuma a tsanake ba tareda son Zuciya ba, domin Alhmdlh, Na tattauna wannan Mas'alar da wasu daga cikin Yan'uwa, inda bayan musanyan hujjoji, sun dawo daga waccar fahimta, Alhmdlh, wannan taimakone na Allah!

Inshallah, gobe zan kawo hujjojinda su masu cewar suna wuta, dakuma yanda Masu cewar Basa wuta suka warware maganganunsu sukai masu Raddi, da hujjojinda sukafi nasu qarfi.

Wanda wannan shine ra'ayina nima shine Fahimtata, kuma ina tare dasu akan Cewar IYAYEN ANNABI BASA WUTA!!!

Wallahu A'alam!

Adam sani Abu-Umayrah www.facebook.com/adam.abuumayrah

31/7/2014 eq 5/Shawwaal, 1435h.


**A INA ALLAH YAKE?** (1)

Assalamu alaikum, Nayi nufin wannan rubutu ne sabida yanda naga wasu Bayin Allah sun Zafafa Magana akan wannan Mas'alar, Haqiqa sun Munana Magana! Sunyi Magana akan Abubuwa da daama na AQEEDAH, wadanda Ahlus-Sunnah Wal Jamaa'ah suka Qudurcesu, har Suke Kafirtasu bisa wadannan Aqidu, Wal-iyaazhu billaah!

Lallai sanya Qiyayyar wani a cikin Harkar Addini matsala ce, wallahi Allah Ya sani, Bana qin wani kuma banawa wani Hassada, Gaskiya ko a ina take zan Fadeta, kuma ko wanene yazo da Gaskiya zan Karbeta, Formular din kawai itace: HUJJA MAI QARFI!

Haqiqa Dan Uwa Ka zalunci kanka idan kace Yan-Izaalah sune sukace Allah Yana Sama! Domin Qarya kake, wallahi Qarya kake! Kuma wannan Qaryar taka Ta zamo mana Daukaka, alokaci guda kuma ta Qaryata Zarge-Zargenka da na Shehunnanka na cewar A Najeriya aka Qyan-Qyashi Izaalah kuma akan idanunsu aka Qyan-qyashi Izaalah, sabida Zamuga Annabi s.a.w ya nuna Allah na Sama, Allah dakansa ya nuna yana sama, Dalilai na Hankali su kansu sun tabbatar da hakan, hakanan Magabata sun nuna haka, Ashe qarya kake kenan!

ALLAH s.w.a YANA SAMA NE BISA AL-ARSHINSA, wannan Shine Abinda muka karanta daga Qur'ani, Hadisi da kuma Maganganun Magabata na Qwarai (Salafus-saaleh), hakanan kuma Hujjoji na Hankali da Lafiyayyar qwaqwalwa ke tabbatar da hakan! Wannan Itace Aqidar Ahlus-sunnah, wannan Shine Abinda Annabi s.a.w ya koyar!

Ku biyoni gobe da Yardan Allah don shan Ruwan Hujjoji bisa wannan maganar!

Wassalamu Alaikum.


**A INA ALLAH YAKE?** (2)

Assalamu alaikum wr, a jiya nasoma matashiya gameda wannan Mas'alar, inda nai Bayanin Cewar Matafiyar Ahlussunnah wal-Jamaa'ah da Salaf gameda wannan Mas'alar itace:

ALLAH YANA SAMA BISA AL-ARSHINSA!

Dalilai Na Al-Qur'ani, Hadisi, Maganganun Salaf, Hankali Lafiyayye duk sun tabbatar da hakan! Kuma da Yardar Allah s.w.a yau zan kawo dalilai gameda Hakan daga Al-Qur'ani mai girma!

Dalilai daga Al-Qur'ani Gameda kasantuwar Allah madaukaki a sama zamu iya kasasu gida biyu:

1: Aayoyinda kai tsaye suke nuni da kasancewar Allah a sama.

2: Aayoyinda basa nuna Allah na sama kai tsaye, sai ka hadosu da yan'uwansu na sauran surori don bada cikakkiyar ma'ana.

AYOYINDA KE NUNA ALLAH NA SAMA KAI TSAYE:

Zan soma da Qabar Farko: ALLAH NA SAM, kafin muzo kan gaba ta biyu: A BISA AL-ARSHINSA.

1: (kuma shine marinjayi a saman baayinsa) (An-Aam:18).

2: (Sunajin tsoron Ubangijinsu daga samansu) (Nahl:50).

3: (shin kun amince cewa wanda ke cikin sama bazai iya shafe qasa ba tareda ku, sai gata tana girgiza) (Mulk:16)

4: (kokuma kun amince cewa wanda ke cikin sama bazai iya sakko muku guguwa ba?......) (Mulk:17).

5: (Shine na farko kuma na qarshe kuma Mabaiyani.....)(Hadid: 3).

Annabi s.a.w ya fassara wannan kalmar ta (Azzaahir/Mabaiyani) yace: ((kaine na farko ba komai kafin kai, kaine na Qarshe ba komai bayanka, kaine Mabaiyani ba komai a samanka, kaine boyayye ba komai baicinka)

(Muslim: Kitaabuzzhikr:61, Ibn Maajah: 3873).

Sannan Aayar cikin Suratul Kahfi tana qara fassara mana cewar Azzaahir na nufin FAUQ ne, inda Allah yake bamu labarin Katangar da Zhil-Qarnayn yayi tsakanin Ya'ajuj da Maajuj, yake cewa:

(Famastaa'u ayyazharuhu = Bazasu iya hayewa samansa ba).

6: Fir'auna ya Tabbatar da cewar Allah na sama ne, inda yake cewa:

((Kuma Fir'auna yace: Yaku yan-Majalisuna ban sanar daku wani abin bauta ba baicin ni, don haka yakai Haamaan ka huramin wuta akan laaka, sannan kasanya min bene don kozan haura ga Ubangijin Musa, kuma ni ina tsammaninsa yanadaga cikin Maqaryata ne)). (Qasas: 38).

Wani mai ciwon zuciya zai iya cewa wannan bata gamsar dashi ba, to muje gaba suratul Gaafir:

((Kuma Fir'auna yace: Yaa kai Haamaana ka gina min bene don in isa zuwa ga Hanyoyi * Hanyoyin -zuwa- sammai in haura ga Ubangijin Musa, kuma lallai ina zarginsa maqaryacine.....)) (Gaafir: 36-37).

Kunga Fir'auna ma ya tabbatar da cewa Allah na sama ne, dukda kafircinsa da Ta'addancinsa.

Da izinin Allah, zan ci gaba a darasi me zuwa, Wassalamu alaikum.


**A INA ALLAH YAKE?**(3)

Assalamu alaikum wr, A baya ga Ayoyin Qur'ani da na soma kawowa a jiya, wadanda ke nuna Kasantuwar Allah Madaukakin Sarki a Sama, da Izinin Allah madaukaki zan ci gaba da kawo hujjoji daga Al-Qur'ani kafin na koma ga Sunnah!

**yan uwa kusani, wannan mas'alar kuna ganinta kamar wasa, kamar yanda a zamanin magabata aka sha faama da Mu'utazilaawa da sauran Firaq akanta, hakanan ayau ake fama!

Idan kai kayi karatu wani baiyi ba, sannan wajibine ka koyar da abinda ka koya, haka nan kasantuwar magabata sun warware mas'alar baisa muyi shiru akanta, domin ai nima daga garesu a littafansu nake dibowa, ba nawa bane! Allah ya mana jagora**

Daga cikin dalilandake nuna cewa Allah na sama ne, akwai:

1: Fadin Allah madaukaki: (Malaa'iku da Ruhi (Jibril a.s) suna hawa zuwa gareshi a cikin wani yini, wanda kwatankwacinsa shine shekaru Dubu 50)
-Ma'aarij:4-.

Kenan tunda Mala'iku suna hawa zuwa gareshi a sama yake kenan, domin da ba'asama yake ba mezaisa su hau?

2: (Gareshi Magana mai kyau da aiki kyakkyawa suke hawa.........)

-Faatir:10-.

3: Gameda Annabi Isa, Allah yace:

(....sai dai Allah ya daugoshi zuwa gareshi..)
-Nisaa'I:158-.

(-Ka tuna- sanda Ubangijinka yace: Ya Isa, lallai ni mai kashe ka ne kuma mai dagoka zuwa gareni.......)
-Ali'Imraan:55-.

Abin Lura shine Allah yayi Alqawarin dago Annabi Isa a.s zuwa gareshi, kuma Cikin Hadisin Israa'I da Mi'iraaji, Annabi s.a.w ya tabbatar da yaga Annabi Isa a.s a Sama.

4: Sakko da Alqur'ani, Dukkan Musulmai sun Yarda cewa Alqur'ani daga Allah aka saukar dashi, Malaa'ika Jibril shine yayi jigilar saukoshi ga Annabi Muhammad s.a.w, kuma dukkansu sun amince da cewar daga Sama Jibril a.s ke sakko shi, kamar yanda Allah ya bada labari:

(Sakkowar littafi (Qur'ani) daga Allah mabuwayi masani)
-Gaafir: 2-.

(Sakkowar littafi -Qur'ani- daga Allah mabuwayi mai hikima)
-Zumar:1-.

Da kuma aayoyin: Fussilat:2, 42. Nahl:102. Dukhaan:1-5.

Kenan tunda kowa ya yarda Qur'ani daga sama aka saukar dashi, sannan Kuma Allah yace daga wajensa aka sakko dashi, Allah Yana a Sama kenan!!!!

2: Allah yace: (Kuma wadanda ke sammai da qassai duk nasa ne, kuma wadandake wurinsa basa girman kai gameda bauta masa kuma basa gajiyawa)
-Ambiyaa'I:19-.

Dukkanmu munsa mala'iku sune ke tareda Allah, kamar yanda Annabi s.a.w ya fada mana, kuma aayoyin Qur'ani suka nuna mana, amma bari na kawo Aayoyin Qur'anin kada ace nayi son raina,

(Idan -Mutane- sunyi girman kai, to lallai wadanda ke wajen Ubangijinka sunai masa Tasbihi a dare da yini kuma basa Gajiyawa)
-fussilat:38-.

(Lallaine wadandake wajen Ubangijinka basa girman kai ga bauta masa kuma suna tsarkakeshi kuma gareshi suke Sujjada)
-Anfaal:206-.

To idan har ka amince Mala'iku matabbatarsu itace sammai, kamar Yanda Annabi s.a.w ya fada mana, kuma Allah madaukakin sarki ya ce mana sune suke wajensa, har ya siffantasu da siffofi na daukaka da cikar bauta, kuma ka amince da Hadisanda Annabi s.a.w ya fadi dubun dubatar mala'ikunda ya gansu a sammai, wasu na sujjada, wasu ruku'u, wasu tasbihi da sauran nau'ukan ibaadah! Me zai hana ka yarda da Kasantuwarsa a Sama???

Da izinin Allah a rubutu mai zuwa zan waiwaya Gaba ta biyu, wato: Bayani Akan Al-Arshi, gamida warware shubuhar da ake kawowa akansa!

Wassalamu alaikum.


**A INA ALLAH YAKE?**(4)

Assalamu alaikum, Kamar yanda a Farkon Rubutuna nace Aqidar Ahlussunnah wal Jamaa'ah da Salaf itace:

Allah yana SAMA NE, YA DAIDAITU AKANSA, DAIDAITUWARDA TA DACE DA ZATINSA!

A duk tsayin rubutuna na baya, na kawo hujjojine daga Alqur'ani gameda Gabar farko, wato ALLAH YANA SAMA! Yau kuma da Yardan ALLAH zan koma gaba ta 2:

YA DAIDAITU BISA AL'ARSHI:

Allah madaukaki ya bamu labari acikin Al-Qur'ani a wurare 7 cewar ya daidaitu bisa Al-Arshinsa!

1: (Lallai Ubangijinku shine Allah wanda ya halicci sammai acikin kwanaki 6 sannan ya daidaita akan Al'arshi) -A'araaf:54-.

2: (Lallai Ubangijinku shine Allah wanda ya halicci sammai da qissai sannan ya daidaita akan Al'arshi) -Yunus:3-.

3: (Allah shine wanda ya daga sammai batare da wani ginshiqi ba dake riqeta sannan ya daidata akan Al'arshi) -Ra'ad:2-.

4: (-Allah- Mai Rahama -wanda- ya daidaitu akan Al'arshi) -Taha:5-.

5: (-Allah- wanda ya halicci sammai da qassai da abinda ke tsakaninsu cikin kwanaki 6 sannan ya daidaitu akan Al'arshi.....) -Furqan:59-.

6: (Allah -shine- wanda ya halicci sammai da qassai da abindake tsakaninsu cikin kwanaki 6 sannan ya daidaitu akan Al'arshi) -sajadah:4-.

7: (shine wanda ya halicci sammai da qassai cikin kwanaki shida sannan ya daidaitu akan Al'arshi) -Hadid:4-.

Wadannan sune wurare guda 7 da Allah ya ambaci cewar ya daidaita akan Al-arshi, duk mai inkarin hakan, to ya Qaryata aayoyinnan mugani, ko ya kawo Ayarda ta qaryatasu! Don Allah kada ka kawomin shirmenka, don bazanbar wahayin Allah inkoma wahayin Shedan ba!!!!!!!

WARWARE SHUBUHOHI GAMEDA DAIDAITUWAR ALLAH BISA AL-ARSHI:

1: A duk sanda Ahlus-sunnah yace Allah ya daidaitu bisa Al-arshi, abinda Mu'utazilaawa da sauran firaq batattu ke kawowa na shubuha don kauda wannan Aayoyin shine: To ai Al-Arshi Halittane, kuma a aayoyinnan sun nuna cewar Allah sai bayanda ya halicci sammai sannan ya daidaitu akan al'arshi, to kafin ya Halicci Al'arshi, kafin ya halicci sama a A ina yake?

AMSA ITACE: Allah tun fil azal bai gushe a sama da komai ba, shine madaukaki bisa dukkan komai tun ba komai, tun kafin Halittar Al'arshi da sammai, kuma kasantuwar a da bai halicci sammai ko Al'arshi ba, bata kore kasantuwarsa Madaukaki bisa komai, sannan bayan Halittar sammai da Al'arshi, ya daidaitu akan Al'arshi, daidaituwa wacce ta dace da zatinsa, shine yasan yanda ya daidaitu! Wannnan itace Karantarwar Al-Qur'ani da Sunnah, kuma Matafiya ta Magabata na qwarai!

Da izinin Allah a rubutu mai zuwa, zan kawo Taawilin da Mu'utazilaawa keyiwa wadannan Ayoyi 7, da kuma rushe wannan tawili nasu! Sa'annan idan hali yayi, zan tabo bayani kan Menene ma Al'arshi tukunna!!!!!

Wassalamu alaikum wr.


**A INA ALLAH YAKE?**(5)

Assalamu alaikum, Yan'uwa barkanmu da saduwa a wannan lokaci!

A yaune da Yardan Allah zan magana akan AL-ARSHI, tunda dai Hujjojin Qur'ani sun Tabbatar mana da cewar Allah yana sama ne, kuma ya daidaita a kan Al-arshinsa! Yanada kyau Musan:

Allah madaukaki ya halicci Al-arshi tun gabanin halittar sammai da qassai, kuma abinda yafi baiyana shine, Allah ya halicci ruwa sannan ya halicci Al-arshi, sannan ya halicci Al-qalami, dalili kuwa shine:

1: Hadisin Abu-ruzayn, wanda ya tambayi Annabi s.a.w: A'ina Ubangijinmu yakasance kafin ya halicci sammai da qassai? Sai Annabi yace: ((Ya kasance bisa wani girgije wanda ba Iska a samansa kuma ba iska a qasansa, sannan ya halicci al'arshinsa a kan ruwa))

-Musnad Abiy-dawud Attayaalisiy: Hadis-1189-.

A hadisin nan mun samu amsar Masu tambayar: TO INA ALLAH YAKE KAFIN HALITTAR SAMMAI da AL-ARSHI, ga amsa nan a sama daga bakinda baya Qarya!

Hakanan zamu fahimci Allah yayi halittar Al-Arshine a kan Ruwa kuma ya daurashi akan ruwan! Kenan ruwan ya riga Al-arshi samuwa!

Hakanan Fadin Allah Ta'aala:

((Kuma shine wanda ya halicci sammai da qassai cikin kwanaki 6, kuma Al-Arshinsa ya kasance bisa ruwa....)) Wannan Aayar ta tabbatar da gabatuwar halittan Al-arshi akan sammai! Wadancan Ayoyindake nuni da cewar: Allah ya halicci sammai sannan ya dai daita akan Al-arshi, kalmar THUMMAS-TAWAA ALAL ARSH, THUMMA anan zata zama LIL HAAL ce bawai LIT-TARTIYB BA, domin idan LIL HAAL CE zai zamana ma'anarta: Allah ya halicci sammai da qassai yana mai daidaita akan Al-arshi! In kuwa kace LITTARTIYB CE, wanda wannan kuskure ne, ma'anar zata zama: sai da Allah ya halicci sammai sannan ya halicci al-arshi ya daidaita akansa!

Wannan kuskurene, Tunda Allah ya halicci Al-Arshi bai gushe ba yana mai daidaituwa a kansa!
Abinda zai qara baiyana maka wannan Ma'anar shine: Dogon Hadisin Imran Bn Husain wanda Imamul Bukhaari ya ruwaito, ciki yake cewa:

((Allah ya kasance kuma babu abinda yakasance kafinsa/baicinsa, kuma Al-arshinsa yakasance akan Ruwa, kuma ya rubuta dukkan komai cikin Ambato, kuma ya halicci sammai da qassai))

-Bukhari:3192-.

Wannan hadisai sun Amsa tambayoyinda Dayawa sukai min a baya nacewar: To Ina Allah yake in kafin Halittar Al-Arshi ko samma??? To ga amsarku can a sama daga Bakinda baya qarya!

Da izinin Allah a rubutu na Gaba zan kawo hujjojindake nuna cewar Lallai Allah na sama bisa Al'arshi daga Hadisai! Har yanzu Qofa abude take ga duk wanda ke inkaari, yazo da hujjarsa mugani, ammafa daga Qur'ani da Sunnah, idan ka kawomin ra'ayinka da wahayinda shedan ke maka, bazan aminta dakaiba balle in amsa! Hujja nakeso mai Inganci!

Wassalamu alaikum


**A INA ALLAH YAKE**(6)

Assalamu Alaikum wr, Barkanmu da saduwa a wannan lokaci! Yau da izinin Allah zan koma wajen Hujjojin Hadisai wadanda suka Nuna Samantakar Allah Madaukaki!

Daruruwan Hadisai sun Nuna cewar Allah madaukaki yana sama, bisa Al-arshinsa! Ya daidaita akansa, daidaituwar da ta dace da shi! Ba tareda siffanta daidaituwar ko kamantataba, Allah shiyasan yanda ya daidaita! Kuma ya fada mana Ya daidaita! Don Haka munyi Imani da Ubangijinmu Ya daidaita akan Al-arshi kamar yanda yace, daga cikin dalilai da suka nuna Allah na sama daga Hadisai akwai:

1: HADISIN ISRAA'I DA MI'IRAAJI: ISRAA'I: shine tafiyar Annabi s.a.w cikin dare daga Masjidul Haraam zuwa Masjidul Aqsaa.

MI'IRAAJI kuma shine: Tafiyar Annabi s.a.w daga Masjidul Aqsaa zuwa sama, inda ya hau sama tareda Aminin Wahayi Jibril a.s! Dogon Hadisi ne matuqa!

Mai so yaje ya duba: Muslim: 162 & 178 -kitaabul Iymaan-. Ahmad 3/22, Bukhaari: kitaabuttauhid: 7517. Da dai sauran Magabata da sukai magana akan Israa'I da mi'iraaji!

# ‪#‎ Tambaya‬: don Allah Mi'iraajin Annabi sama sukai kokuwa yawo sukaitayi ko ina? A sama ya je wajen Allah har ya shar'anta masa salloli 50 ko a ko'ina? A sama Annabi musa yace masa yakoma wajen Allah a rage sallah har ta dawo biyar ko walagigiya sukaitayi ko ina??

Amsa nakeso: (Famaa li'haa'ulaa'I'll qaumi la yakaaduna yafqahuna qaula????).

2: Hadisin Abi-Ruzain wanda ya Tambayi Manzon Allah s.a.w: shin Ina Ubangijinmu yake kafin Halittar sammai da qassai? Sai Annabi yace: (Ya kasance cikin wani girgije, wanda ba iska samansa kuma ba iska qasansa, sannan sai ya halicci Al'arshinsa bisa ruwa)

-Musnad Abi-Dawud Attayaalisiy: Hadisi na 1189.

3: Hadisinda yazo gameda Mutuwar Mumini da Kafiri, Inda Annabi s.a.w yace Mumini ana tafiya da ransane zuwa sama, har akaishi wajen Allah, sannan a dawo dashi! Kafiri kuwa Annabi yace ba'a budewa ruhinsa qofar sama, bayan mala'ikan mutuwa yayi sama, zai dawoda ran zuwa qasan sijjiyl!

Ku duba: IBN Maajah: 4262, Ahmad: 8551, Sahihul Jaami'I: 1968

4: Hadisin JAARIYAH (hadisin Baiwa): Hadisin kuwa shine: wanda Imam Maalik ya ruwaito daga: Umar bn Hakam, Muslim kuma daga Mu'awiya bn Hakam, dadai sauran Maruwaita daban daban ta hanyoyi Mabambanta:

""Annabi s.a.w ya Tambayi Baiwar: Ina Allah yake? Tace: Yana sama! Sai Annabi yace: Waye ni? Tace kai Manzon Allah ne, Annabi yace: Ka Yantaata domin Ita mumina ce""

**Wannan Hadisi Naji wata tace Hadisine Aahad kuma Mutrib, sabida Imam Muslim ne kadai ya ruwaitoshi daga Mu'awiya bn Hakam, to Alhmdlh QARYA KIKE! HADISINE MUTAWAATIR! Kince akawo wadanda suka ruwaito hadisin banda Muslim, kuma banda ruwayar Mu'ayiwa bn Hakam, to ga ruwayoyin Hadisin kaman Haka:

1: Muslim daga Mu'awiy bn Hakam: 5/23-24: Baabul Masaajid.

2: Muwatta Maalik Ruwayar Abi Mus'ab Azzuhriy, daga Umar bn Hakam: Baabu maa yajuwzu minal itqi firriqaab: hadis:2730.

3: Musnad Abi Dawud Attalisiy: Mu'awiya bn Hakam: Hadis 1201.

4: Musannif Abdurrazaaq Assan'aaniy, daga Ibn Taawus, daga Babansa: hadis16813, sai kuma daga: Yahya bn Abi kathiyr: hadis:16816.

5: Musnad Ahmad: Daga Shariyd, ki duba babin Hadisu shariyd bn Yusuf Assaqafiy: 17945. Sunan Darimiy, hadisi:2393.

6: Sunan Abiy Dawud: daga Abu-Hurairah: hadisi3284.

7: Sunanul Kubraa lil Baihaqi: daga Umar bn Hakam: 15266.

Kai ruwayoyine ma batata gasunan a littafai da yawa, amma tace wai Muslim ne kadai ya ruwaitoshi daga Mu'awiya bn Hakam! Allah ka mana jagora!

Akwai ci gaba bi'izniLLAAH!

Wassalamu alaikum!


**MATSAYAR SHEHU INYAAS GAMEDA BIDI'A**(1)

Assalamu alaikum, Yan'uwa indai A Babin Bidi'a ne, daga yau na dena kawo hujja da Malaman Ahlussunnah, Maganar Shehu INYAAS wallahi ita kadai ta wadatar!

Da Farko dai, Shehu yana Magana ne akan Gina Makarantu, inda wasu Watsattsu tambadaddu daga Dariqa ke cewa Bidi'a ne, shehu Inyas yace wannan Bidi'a bace mustahsanah, wannan (Gina Makarantu) Sunnah ne! Wannan shine magana mafi Inganci!

Shehu Inyaas bai tsaya anan ba, yaci gaba da Bude Baabin Bidi'ah, da kuma yanda yayi raga-raga da YAN MAULUDI da masu BIDI'A MUHASSANA! Shehu yace:

"Allaamah ibn Daqiq yace cikin Littafinsa (Umdah-Sharhu Bulugul Maraam) abinda yace: BIDI'AH: a Lugah itace: Abinda aka aikata batareda makamancinsa ya gabace shi ba.
Abinda ake nufi da bidi'a a nan (shari'ah): Abinda aka aikata batareda hukuncinsa yazo a Qur'ani ko sunnah ba. Malamai sun Rarraba Bidi'a zuwa gida BIYAR:

1: WAAJIBAH: kamar haddace karatu da rubuta littafai da raddi ga mulhidai bisa tsaida masu hujja.

2: MANDUWBAH -Mustahabbah-: kamar gina makaranta.

3: MUBAAHAH -jaa'izah-: kamar faadadawa wajen kalolin abinci, da tufafi na Alfarma.

4: MUHARRAMAH.

5: MAKRUHUHAH. Wadannan (Muharrama da Makruhah) sune Zahirin gaskiya, don Haka fadinsa s.a.w: (Dukkan bidi'a batace) Aamun ce makhsus -ta game dukkan bidi'a, amma kuma ta kebe wasu-. Haka Malamai suka ce:

SHEHU INYAS YA BAIYANA RA'AYINSA yana cewa:

''A Zahirin Gaskiya, Lafazin KULLU a wannan Hadisi da ire-irensa da suka zo da ma'anarsa, a haqiqaninsu suke (ba wani muhassana ko mubaaha), Rarrabe Bidi'a zuwa wadancan Gidaje da aka Ambata, da cewa wai Bidi'ah Hasana da sayyi'ah, WANNAN MAGANA BATADA WANI BARBASHI NA ILIMI! Domin babu wani dalili da ya nuna hakan, kuma babu wani hadisi da yazo da hakan koda dan qamshinsama! Kuma misalanda aka kawo (gina makaranta, sanya tufafi, kalolin abinci e.t.c) ba bidi'a bace kai tsaye! Domin Rubuta ilimi ya nuna Rubuta Qur'ani a Zamanin Annabi s.a.w, da zamanin Khulafaa'urraashidiyn, kuma hadisin (kurubutawa abu Shaahin) ya nuna haka, kitaabah shine Tadwin kai tsaye. Raddi ga Mulhidai kuwa Qur'ani ya nuna hakan, domin cikinsa akwai raddi ga Ahlul Kitaab da Mushrikai, ginin Makarantu da gine-gine anyi shiru akansu, duk abinku da shiri'a tayi shiru akansa rangwame ne!

Shikuwa sanya tufafi kyawawa da abinci kala-kala, zamu samesu a hadisin: (Allah naso yaga birbishin ni'imarsa akan bawansa), kuma Qur'ani ya nuna hakan (Kace waye ya haramta adon Allah wacce ya fiddawa bayinsa, da kyawawan abu na arziqi?) (Da kyawawan kaya da kuka sanyawa) (kuma gameda ni'imar Ubangijinka kabada labari). Sukuwa MUHARRAM da MAKRUHAH dama chan Haramtattu ne kamar sauran haramtattunda dalilai suka nuna Haramcinsu, su Haramtattune ababen Qi, basuda matsayi a Bidi'ah, DAHAKANE BIJIMAN MALAMAI DA SUKAI NITSO A ILIMI SUKAI INKAARIN RARRABA BIDI'A ZUWA WASU KASHE-KASHE, kuma sukai Raddi ga masu Rarrabawa, kuma suka tabbatar da dukkan Bidi'a bata ce kai tsaye, KODA MECECE KUMA YA YAKASANCE KO YA AFKU! Kuma dukkan Bidi'ah batace!

SHEHU INYAAS yarufe zancen yana me cewa:

"Wayyo Allah, abin mamaki ga mutane masana, sun ruwaici hadisi da makamantansa masu ma'anarsa, ingantattu sadaddu ga Annabi s.a.w AMMA SAI SUKA CHANZA MA'ANARSA, da kuma zahirin abinda aka ginashi, suka maidashi ga Abinda son ransu yake so ba tareda dalili ba, ba Qur'ani ba ba Sunnah ba! Ba ijmaa'I ba ba Qiyaasi ba lafiyayye be karban irinsa ma! Hadisin wannan Babi (hani daga Bidi'a) Hujjace tsayayya akan Duk me rarrabe bidi'a, DUK ME HUJJA KUMA daga Qur'ani da Sunnah wanda ta nuna Rarrabe Bida'a, SAI YA GABATO MANA DA DALILANSA!

Masana Qur'ani da Hadisi sunyi Ittafaaqi kan cewa: Dukkan Bidi'ah Bata ce, dukkan Bata tana wuta, Qarama ce ko babba, baiyananna ko boyayya, wace ta shafi aqida ko aiki! Ko mutum biyu basuyi sabani ba akan haka!!!!!!

Kuduba littafin Inyaas: Tabsiratul Anaam fi Annal ilma huwal Imam: shafi 70-72!

Wannan Itace Matsayar Shehu Inyas gameda Bidi'a, don Haka su Dahiru Bauci, Maqari, Dan Maraya d.s, ku da kukace akwai bidi'ah hasana Inyass ya qaryata ku, yace ku kawo hujja, don Haka muna jiranku! Ban kawo Maganar Ibn Taimiyyah da sauran Salaf ba, sabida kun Rainasu, yasa na kawo Babanku ko shima Kafirin ne??????


**GORON JUMA'A**

Imamush-shafi'iR.L, acikin Diwaaninsa yana Bada shawara kan zaban Aboki, yake cewa:

"Falaa Tas-hab Akhal Jahli # waiyyaaka wa iyyaahu.

Fakam min Jaahilin Ardaa # Haliyman hiyna Aakhaahu.

Yuqaasul Mar'u bil mar'i # Izhaa mal mar'u maashaahu.

Walish-shay'I alash-shay'i # Maqaayiysun wa ashbaahu"

MA'ANA: Yakai dan'uwana, kada kayi Abota da jahili, babu kai babu shi. Nawane daga jahilai suka halakar da mutumin qwarai sanda yayi Abota dashi? Ana kwatanta mutum da mutum idan yayi tafiya dashi.

Duk abinda ka ganshi da wani abu, to yanada kwatanci da kamanni dashi.

*Jahili bawai yana nufin Mutum Mara ilimine kadai ba, a'a, duk wani Mutum mara hali na qwarai, ko mara tarbiyya ta qwarai, to dukkaninsu suna shiga Qarqashin Ma'anar Jahili*.

Yasa Annabi s.a.w yace: (Al-mar'u ala diyni khalilhi, Fal yanzur ahadakum man yukhaalil) -Mutum na kan addinin abokinsa (dabi'u da halayya), don haka dayanku ya duba wanda zai abota dashi.-.

Udayy bn Zaid na cewa:

"Anil mar'I laa tas'al was'al an qariynihi # Fakullu qariynin bil maqaarini yaqtadiy.

Wa swaahib ulittuqaa tanil min tuqaahum # walataswhabil-ardaa fatarda ma'arradiy"

MA'ANA: Kada ka tambaya gameda waye mutum, karambayi abokinsa, domin dukkan aboki da abokinsa yake koyi. Kayi abota da ma'abota tsoron Allah sai ka rabauta da tsoron Allah-n-su, kada kai abota da lalatattu sai ka lalace tareda lalaatattu.

Na tuna Maganar Marigayiya Zeena Jazz take cewa:

**Kayi abota da wanda kake son maqobtaka dashi a Lahira**

lallai wannan Magana abar dubawa ce!

Suwaye Abokanka/ki?????



**SALATUL FAATI**

ABIN DARIYA, YARO YATSINCI HAQORI!!!!!

Assalamu alaikum, Yan'uwa yau da Asubah naji wata Tatsuniya mai ban dariya!

Wato Shahararren Malamin TIJJANIYYAH dinnan, qwararre wajen buga misali da kwatance, wanda zai maka Wa'azi na awa 4 (4hours) amma bazakaji QALALLAHU ba balle QAALAR-RASUL s.a.w! Dazu da asubahi a masallacin kusa da gidanmu, aka sanya Karatun Tarjamar Qur'aninsa da yakeyi duk ramadaana! Yana Tafsirin Aayar da Allah madaukaki yake cewa:

(WAL KAYLA WAL BIGHAALA WAL HAMIYRA LI TARKABUWHAA WA ZIYNAH, WA YAKHLUQU MAALAA TA'ALAMUN).

Sai bayan ya gama tarjama yace:

"Yanzu ku duba, Allah ya halicci Raqumi, don ahau kuma a dauki kaaya akansu masu nauyi, Bature ya Qirqiri Jirgin sama don Tafiya da kuma daukan kaya, to yanzu ka duba, idan aka ajiye RAQUMI da JIRGIN SAMA wanne yafi girma?

Akace JIRGI, yace wanne yafi tsada da Daraja? Akace JIRGIN sama!!!".

Kunsan Me SHEHU YACE?????

Kawai sai yace: "To yanzu menene Abin Mamaki don wani Mutum yazo da Salaatul Faatihi wacce tafi Salaatul Ibraahimiyyah (da Annabi s.a.w ya karantar) lada da daraja?

Meyasa baku Tambayi ya Abinda Bature ya Qirqira yafi abinda Allah ya Halitta daraja ba? Sai kuke Inkarin Abinda wani Mutum yazo dashi don Yafi na Annabi Daraja da Falala??"

Jama'a don Allah me zaku bawa Shehu Amsa dashi?


**SHIN ANNABI S.A.W NE YA UMARCI IMAM ALI r.a DA YAQIN SIFFIN???**
.
SHIN WAI ABI DAWUD NE KADAI YA RUWAITO HADISIN QAYS BN UBBAAD?
.
Assalamu alaikum, wannan Naushine ga Mara kunyar Yaronnan, na hannun daman shugaban Yan-Kogo, wato Aliyus-sufiy aika-aika, aqoqarinsa na yiwa shehin Malami: Muhammadul Kabir raddi!
.
Da Kuma Shi kansa AUDU SARKIN KOGO a qoqarinsa na yiwa Dr. Sani R/lemu rashin kunya!
.
Bazan jaku da nisa ba, ga Abinda Nakogo kecewa:
.
"YARO BAISAN WUTA BA SAI YA TAKA! : RADDI GA KABIRU DAN
BASHIRU KOFAR WAMBAI...1
.
Akokarinsa na yanuna cewar sayyidi Ali (ra) yayi yaki batareda
Annabi yasashiba sai yaron kofar wambai yakawo wani
‪#Maudhuin‬hadisi (hadisin karya) wai sayyidi Ali yace (bayan
an tambayeshi akan yakin da yayi):
(( ﺍﻥ ﺭﺳﻮﻝ ﺍﻟﻠﻪ ﻟﻢ ﻳﻌﻬﺪ ﺍﻟﻴﻨﺎ ﻋﻬﺪﺍ ﻧﺎ ﺧﺬﻩ ﻓﻲ ﺍﻻﻣﺎﺭﺓ ﻭ ﻟﻜﻨﻪ ﺷﻲﺀ ﺭﺍﻳﻨﺎﻩ ﻣﻦ ﻗﺒﻞ
ﺍﻧﻔﺴﻨﺎ.))
MA'ANA:
(( Hakika Annabi baimana wani alkawari da zamu rikeshi kan
shaanin mulkinnanba, sai dai wani raayinmu (ko "wani abune"
bisa banbancin lafazi) da muke ganinsa a kashin kanmu ))"
.
‪#RADDI‬: Yaro kenan: Ai Malam Muhammad Basheer Hadisin Qais Bin Ubaad ya kawo, wanda yazo cikin Sunan na Abi-Dawud hadisi me lamba 4666!
.
Dake kai dodaddiyar basira gareka kaje ka dauko wani hadisi chan a bola kazo kana ihu akai!
.
Dalilinda yasa Malam Basheer yakawo hadisin shine: Audu na kogo yace: "Duk duniya in kace babu wanda ya kawo wannan Hadisi baicin Abi-Dawud, babu me qaryataka"! Allahu Akbar,
.
ABDUL-JABBAR NI YAU NA QARYATAKA KAI MAQARYACINE!
.
Zan kawo malamai sama da 20 da suka kawo Hadisin da lambobin hadisan, sai a Qaryatani nima!
.
Ga Lafazin Hadisin dauke da Isnaadinsa:
"4666 - ﺣﺪﺛﻨﺎ ﺇﺳﻤﺎﻋﻴﻞ ﺑﻦ ﺇﺑﺮﻫﻴﻢ ﻟﻬﺬﻟﻲﺣﺪﺛﻨﺎﺑﻦ ﻋﻠﻴﺔﻋﻦ ﻳﻮﻧﺲﻋﻦ ﻟﺤﺴﻦﻋﻦ ﻗﻴﺲ ﺑﻦ ﻋﺒﺎﺩﻗﺎﻝ: ﻗﻠﺖ ﻟﻌﻠﻲ ﺭﺿﻲ ﻟﻠﻪ ﻋﻨﻪ: ﺃﺧﺒﺮﻧﺎ ﻋﻦ ﻣﺴﻴﺮﻙ ﻫﺬﺃﻋﻬﺪ ﻋﻬﺪﻩ ﺇﻟﻴﻚ ﺭﺳﻮﻝ ﻟﻠﻪ ﺻﻠﻰ ﻟﻠﻪ ﻋﻠﻴﻪ ﻭﺳﻠﻢ ﺃﻡ ﺭﺃﻱ ﺭﺃﻳﺘﻪ ﻓﻘﺎﻝ: «ﻣﺎ ﻋﻬﺪ ﺇﻟﻲ ﺭﺳﻮﻝ ﻟﻠﻪ ﺻﻠﻰ ﻟﻠﻪ ﻋﻠﻴﻪ ﻭﺳﻠﻢ ﺑﺸﻲﻭﻟﻜﻨﻪ ﺭﺃﻱ ﺭﺃﻳﺘﻪ»
(Isma'I'll bn Ibraahim Al-Hazhaliy ya bamu labari, daga Yunus, daga Hasan, daga Qais bn Ubbaad yace: Nacewa Aliyu r.a: kabamu Labari akan wannan Tafiya taka (zuwa yaqin Siffin), shin wani Alqawarine Annabi s.a.w ya Alqauranta maka, kokuwa ra'ayinkane kayi? Sai (Imam Ali r.a) yace: (Manzon Allah s.a.w baimin Alqawarin komai ba, sai dai wannan ra'ayinane nayishiy!
.
Audu na kogo yace banda Abi-Dawud da yakawo wannan Hadisi A sunan dinsa, duk duniya ba wanda ya isa yakawo wani malami da ya kawo hadisin! To yau ga dan Primary zai kawo maka Malamai da littafai kusan 20, bayan Malaminsa dan Sakandare yakawo kusan sama da 5:
.
Kaje ka duba:
.
1: Musnad Ahmad: Hadisi na 1271.
2: Assunnah na Abdullahi bn Ahmad: hadisi na 1266.
3: Tasirut-Tabariy: 10/464 Qarqashin Suratul A'araaf: aya ta 152.
4: Aqdul Fariyd: Ya hakaito wannan Hadisi 5/53.
5: Mu'ujamul Ausat: Hadisi na 575.
6: Hadisu Shu'ubah bn Hajjaaj: 1/51 hadisi me lamba 46.
7: Mudihu Auhaamil-Jam'I wattafriyq: 1/401.
8: Jami'ul Usuwl: 10/76 hadisi me lamba: 7548.
9: Al-Ahaadisul Mukhtaarah, Mustakhrajah minal Ahaadisul mukhtaarah mimmalam yakhrijhul Bukhaari wa muslim: 2/326 Hadisi me lamba 704!
10: Tuhfatul Ashraaf bi ma'arifatil Atraaf: Hadisi me lamba 10258.
11: Manaaqibul Asadul Gaalib Aliyu bn Abi Taalib, na Ibn Jazari: Hadisi me lamba: 41.
12: It-haaful Muhrah, na Ibn Hajar: Hadisi me lamba: 14702.
13: Itraaful Musnadil Mu'utali bi atraafil Musnadil HanbaliHaadisi me lamba: 6381.
14: Jaami'ul Ahaadiys: Hadisi me lamba: 34187.
15: Jawaabu Ahlus-sunnah Annabawiyyah fiy naqdi kalaamish-shiy'ah: 1/219.
16: Al-Intisaar lis-sahabi wal Aal: 1/429.
17: Aljaami'us-sahih Lissunani wal masaaniyd: 9/790.
18: Assahihul Musnad min Aasaaris-sahaabah: Hadisi na 83.
19: Musnadul Jaami'I: Hadisi me lamba 10273.
20: Al-Iymaa'u ilaz-zawaa'I'dil Amaaliy wal ajzaa'I: Hadisi me lamba 4520
.
Jama'a wannan Hadisi gashi na kawoshi a littafai 20, Audu na kogo yace Babu wanda ya kawo bayan Abi-Dawud, inaso don Allah ku bincika min kugani, TSAKANINA DA AUDU NA KOGO WAYE MAQARYACI!!!
.
Kuma wannan hadisine SAHIHI



**RADDI GA Musa Umar Aliyu (1)**
.
Gameda Rubutun da yayi me taken: "guduma akan mai deploma sani rijiyan lemu akan karya da yayi nacewa wai jama'an mu'awiya dake sham masu natsuwa ne masu biyayya sukuwa mutanen syd ali yan hayaniya ne marasa biyayya"
.
Assalamu alaikum wr, nayi wannan rubutune yazama Raddi ga wani wai shi: MUSA UMAR ALIYU, bisa rubutun da yayi mai take asama!
.
Dafarko, Bama Raddi ga wani don yayi raddi ga Malaminmu ko ya zageshi, sai dai duk sanda mukaga wani na yunqurin yin wuru-wuru A Addini, to muna qoqari wajen ganin Mun dankwafar dashi da taimakawa Gaskiya, muna Raddine bisa tsayayyun Hujjoji ba Baragurbi ba!
.
Na Biyu, Yanada kyau ku gane, Bawai Ana Nufin Mu'awiyah r.a yafi Imam Ali r.a bane, wallahi ko kadan, Munsan Imam Ali yafi Sayyadi Mu'awiyah nesa ba kusa ba! Kuma Bawai ilaahirin Mabiya Imam Ali r.a sune masu hayaniya da rashin natsuwa ba, Aa'a, Abin nufi shina MAFI YAWANSU YAN JAGALIYA ne, Kamar Yanda Imam Ali yasha Aibantasu da tsine masu, kai hatta Ahlul Baitu sun TSINEWA MABIYANSU!
Wannan bai Hana a samu daidaikun masu Hankali da natsuwa cikin tawagar, sai dai basu da yawa kamar yanda suke a Rundunar Mu'aawiyah r.a, shi kansa Imam Ali ya Tabbatar da hakan a wurare da daama! Zan kawo wadannan maganganu directly daga Ahlul Baiti inshaa Allah!
.
Na 3: Hadisin da ka kawo wanda Imam Haakim ya Ruwaito:
.
4559 - ﺣﺪﺛﻨﺎ ﺃﺑﻮ ﺍﻟﻌﺒﺎﺱ ﻣﺤﻤﺪ ﺑﻦ
ﻳﻌﻘﻮﺏﺛﻨﺎ ﺍﻟﺨﻀﺮ ﺑﻦ ﺃﺑﺎﻥ ﺍﻟﻬﺎﺷﻤﻲﺛﻨﺎ
ﻋﻠﻲ ﺑﻦ ﻗﺎﺩﻡﺛﻨﺎ ﺃﺑﻮ ﺇﺳﺮﺍﺋﻴﻞﻋﻨﺎﻟﺤﻜﻢ ﻗﺎﻝ: « ﺷﻬﺪ ﻣﻊ ﻋﻠﻲ ﺻﻔﻴﻦ ﺛﻤﺎﻧﻮﻥ ﺑﺪﺭﻳﺎ
ﻭﺧﻤﺴﻮﻥ ﻭﻣﺎﺋﺘﺎﻥ ﻣﻤﻦ ﺑﺎﻳﻊ ﺗﺤﺖ ﺍﻟﺸﺠﺮﺓ«‏‎.‎
.
Wai: "mutane 80 daga mutanen Badr suka halarci yaqin Siffin tareda Imam Ali r.a, da kuma 250 daga wadanda sukai mubaaya'a a qarqashin bishiya".
.
#To wannan Hadisine Gurbatacce, Bari mubi sanadin Hadisin mugani:
.
1: mutum na biyu a sanadin Hadisin: KHIDR BN ABBAAN:
(A)"Abu Abdullaahi haakim da waninsa sun Da'afashi" -Al-mugniy fiddu'afaa'I: 1/210-.
(B): "Haakim da wasunshi sun Da'afashi, Daru Qutniy yayi suka akansa" -Mizaanul-i'itidaal/­ 1:654.
(C): Kaje ka duba Lisaanul Mizaan: 1/119, nan ma An da'afashi!
.
2: Mutum na 3 a Riwaayar: ALIYU BN QAADIM:
(A): Ibn Ma'iyn yace: Da'ifi ne. -Bayaanul wahm wal iyhaam fi kitaabil Ahkaam: 3/203.
(B): Ibn Sa'ad yace: Ma'abocin Hadisai munkarai ne. -Albadrul Muniyr: 5/166-.
(C): Aliyu Bn Qaadim, Animasa kinaaya da Abal Hasan, Ya mutu a Kufah shekara ta 213 a zamanin Khilaafar Ma'amun, ya kasance Ma'abocin Hadisai Munkarai mai tsananin shi'anci. -Tabaqaatul Kubraa: 6/371.
(D): Da'ifi ne shi. -Alkaamil fiddu'afaa'I: 6/345
(E): Aliyu bn Qaadim: Yahya da Ahmad bn Maisam sun da'afashi, hakanan daru qutniy. -Al-ilalul mutanaahiyah fil Ahaadiysul waahiyah: 1:111-, Addu'afaa'u wal matrukiyn:1/91. Mizaanul I'itidaal:1/160. Lisaanul Mizaan: 1/316.
.
3: Mutum na 4 a Hadisin: Abu Israa'il: cikakken sunansa shine: ISMAA'IL BN ISHAAQ ko ABI ISHAAQ: Dayane daga cikin Da'ifai. Mizaanul I'itidaal: 1/222. Kuma yana daya daga cikin GULLAAT a shi'a, daya daga cikin masu Kafirta SAYYIDNAA UTHMAAN r.a: Mizaanul I'itidaal: 4/490.
*An da'afashi, yakasance yana Kafirta Sayyidnaa Uthmaan r.a. Almugniy Fiddu'afaa'I: 2/770.
*Ba Siqah bane, Bahaz yace: Najishi yana zagin sayyidnaa Uthman yana cewa Ankasheshi ne yana Kafiri. Ibn Uday yace: mafi yawan hadisansa suna sabaswa hadisan siqah. Daru Qutniy yace: Da'ifi ne. -Addu'afaa'u walmatrukiyn: 1/116.
.
Wannan kenan, kasan Hadisan da zaka dinga kawo mana ba irin wannan ba! Hadisinda be inganta ba, Rijaal dinsa duk Raunanane, sannan cikinsu Harda masu Kafirta Sayyidnaa Uthmaan! Gashidai kowa yagani!
.
Akwai ci gaba!



**RADDI GA Musa Umar Aliyu** (2)

Gameda Rubutun da yayi me taken:

"Guduma akan mai deploma sani rijiyan lemu akan karya da yayi nacewa wai jama'an mu'awiya dake sham masu natsuwa ne masu biyayya sukuwa mutanen syd ali yan hayaniya ne marasa biyayya"

Assalamu alaikum wr, Yan uwa barkanmu da saduwa a wannan lokaci!

A rubutuna na baya, na ruguza wanchan Gurgun Hadisin da wannan Barafilen ya kawo!

Sanadinsa baida qamshin inganci ballantana makama a ilimi! Ayau kuma da yardan Allah, zan kawo maganganun Imamuna Aliyu R.A ga SHI'ARSA, inda ya dinga musu TOFIN ALA TSINE da ALLAH WADAI! Kai ba shi kadai ba, duk kusan Ahlul Baiti sun La'ancesu! Wannan zai tabbatar da cewa Mafi Rinjayensu yan JAGALIYA NE masra NATSUWA da LADABI! Kada dai na cikaku, bari kuji daga bakinsu:

1: IMAM ALI R.A: "Inda ka Tantance Shi'ata, da bazaka samesuba face a siffane kawai, da zaka jarrabasu da ka samesu masu ridda ne, da zaka tankadesu, da guda 1 daga 1000 cikinsu bai tsira ba" -Alkaafiy:8/338.

2: "Naso ace ban gankuba a rayuwata, kuma ace ban taba saninkuba, saninku wallahi yazamemin nadama, kuma ya qareminda ciwo, ALLAH YA TSINE MUKU kun cika zuciyata da amai, ku faadada qirjina da Baqinciki...........­. Kun baata min ra'ayina da SAABAWA da TABEWA, Har Quraishaawa ke cewa: Lallai Dan Abi Taalib mutumne jarumi, sai dai beda ilimin yaqi! BABU RA'AYI GA WANDA BA'A YI MASA BIYAYYA" Nahjul Balagah:70-71.

3: "Kun kasance Rundunar Mace, mabiya Raqumi, yayi kuka sai kuka Amsa, ansokeshi sai kuka gudu, Halayenku munana nen Alqawarinku sabawa ne, Addininku Munafunci ne, Ruwanku me gishirine, mai zama cikinku abin kamune da laifinsa, mai juya muku baya, mai riskar rahamar Ubangijinsa ne, kamar ina kallon masallacinku tamkar tsakiyar jirgin ruwa, Allah ya turo mata Azaba ta sama da qasa, duk na cikinta sun dilmiye" Nahjul Balaagah:8.

Daga cikin Abinda zai Qara tabbatar maka da cewa lallai Mutanen Imam Ali basuda biyayya, fadinsa: "Lallai ni ina zaton wadannan Mutanen (Mutanen Mu'awiyah r.a) zasu rinjayeku, da Hadin kansu bisa Batarsu, da rarrabuwarku bisa Haqqinku, da sabawarku ga shugabanku bisa haqqi, da biyayyarsu ga shugabansu bisa bata, da Isar da Amanarsu zuwaga shugabansu....... Har yake cewa:

"Ya Allah ka chanzamin mafi Alherinsu, ka chanza masu mafi sharri na, Allah ka narkar da zukatansu kamar yanda gishiri ke narkewa cikin ruwa, wallahi naso ache Abani dawakai 100 daga Bani Firaas bn Ganm a maimakonku" Nahjul Balaagah.

Kai Rashin Kunya sai Dan Shi'a, Nahjul Balagah cike yake da Tofin Allah tsine gareku, amma har kuna Qirqirar ku masoya Imam Aline, Bayan ya tsine muku? Nima dai bari nace TIR DAKU, ALLAH WADARANKU, MARASA BIYAYYA DA LADABI



** MAGANAR GASKIYA GAMEDA DARIQAR TIJJANIYYAH ** (1)
Via: Adam Sani Abu-Umayrah

Assalamu alaikum, Dubun salati su tabbata ga shugabanmu Annabi Muhammad s.a.w, Alayensa da sahabbansa, da duk wadanda suka bi tafarkinsa har zuwa ranar Sakamako!

Bayan Haka, Wannan wani qaramin bincikene da nayi, bisa karanta wasu daga littafan tijjaniyyah, da kuma abubuwanda na sani bisa mu'amalata da wasu daga Malamansu da kuma Yan'uwana Almajirai, Banyi nufin hakanba don cutar da wani, ko muzanta wani, nayi hakanne don tsage gaskiya, da kuma ankarar da Yan uwa hatsarinda ke tattare da wannan Aqidah, da kuma kaucewa Tsarin Musulunci da tayi! Allah nake roqo, ya Haskaka mana Gaskiya mu ganeta mu bita, ya kuma Nuna mana Qarya da Bata ya bamu ikon guje mata, ya shiryar damu tafarki madaidai ci.

TARIHIN SHEHU TIJJANI!

An haifi shehu Tijjani a wata Alqarya da ake kira (Aynu Maadi), a ranar 12 ga watan safar, shekara ta 1150 bayan Hijirar Annabi s.a.w, daidai da 1737 Miladiya.

Mahaifinsa Balarabe ne, sunansa: Sidi Muhammad bn al-Mukhtar bn Ahmad bn Muhammad bn Saalim, Mamarsa kuma itace Aisha bnt Muhammad bn Sunusi (Babanta shine wanda ya Assasa dariqar sunusiyyah), ita kuma Yar qabilar barbariyyah ce, wace akewa laqabi da TUJAANAH, wannan qabila na zaunene a kusa da garin Tilmisaan a Qasar Jazaa'ir (Algeria)! Kakan Shehu Tijjani na 4, wato Saalim shine farkon mutumin da ya kafa garin Alqaryar Aynu Maadi, bayanda (saalim) ya kafa garin, ya kafa Dariqarsa, sai yayi iqirarin cewa shi sharifi ne, wato jikan Annabi s.a.w, kuma Nasabarsa tana isa ga Alhasan bn Aliyyu r.a jikan Manzon Allah s.a.w, Ta hanyar Idris bn Idris wanda ya kafa garin Adaarisah dake Qasar Moroco, sabida hakane sai Masu bincike suka shiga tantaman gaskiyar wannan nasabar ta Kakan Shehu Tijjani, wanda ya jingina Kansa ga Annabi s.a.w. (Ka duba littafin: The Tijjaniyyah Asufi order in the Modern age, page 16 by Dr. Jamil Abu Nasr).

Mahaifin Shehu Tijjani ya rasu a shekarar 1166hijriyyah, daidai da 1753 miladiyyah, a lokacin Shehu yana dan shekara 16, dukda shehu yayi Aure kafin rasuwar Babansa, amma ya saki Matar sanda yayi nufin shiga gari neman ilimin sufanci, dakuma Haduwa da Jiga jigan Malamanta, domin samun kulawarsu da shiryarwarsu ga qoqarinsa!

Ya Haddace Alqur'ani tun yana dan shekara 7, sai yaci gaba da karance-karancen Fiqhu, Hadisi, Tajwidi, Usulul Fiqh, Nahwu da kuma Adab.

Shehu bayanda ya saki Matarsa ta farko, wacce bata haihu dashi ba, ya Sayi Bayi 'yan mata guda 2, sai ya 'Yantasu ya Auresu, ya sanyawa guda cikinsu Mabruwkah, dayar kuma Mubaarakah.

Mabruwkah ta Haifa masa dansa na Farko A duniya, ya sanya masa suna Muhammadul Kabiyr, an kashe Muhammadul kabiyr a shekarar 1832Miladiyyah,daidai da 1243Hiriyyah, a cikin wani bore ko tada qayar baya da nuna qin jinin gomanti, wanda ya shirya yashi ga Hukumomin Gomnatin Turkiyyah a Jazaa'ir (Algeria).

Ita kuwa Mubaarakah ta haifa masa dansa Muhammadul Habib, wanda ake kira da Muhammadus-sagiyr, shine ya zamo Khalidansa a jagorancin Dariqar Tijjaniyyah.

Zan tsaya Anan, ina mai roqon Allah ya datar dani da ku baki daya zuwa ga Shiriya, inshallah Gobe zan tashi daga Inda Na tsaya.

Wassalamu alaikum.


** MAGANAR GASKIYA GAMEDA DARIQAR TIJJANIYYAH** (2)
Via: Adam Sani Abu-Umayrah

CI GABA DA TARIHIN SHEHU TIJJANI 2

Assalamu alaikum, Barkanmu da saduwa a wannan lokaci, dafatan Allah ya karbi ibadunmu, ya kuma yafe kurakurenmu!

A jiya na soma tarihin shehu, inda lokaci ya mana halinsa, inshallah yanzu zan tashi daga inda na tsaya:

"Haqiqa, shehu Tijjani a farkon rayuwarsa, ya bata lokaci mai yawa wanda baza'a kauda kai ba gareshi ko a wulaqantashi, cikin tafiye-tafiyen neman ilimi, daga wannan zaawiyah zuwa waccan, daga wannan garin zuwa wancan, a tsakankanin Magrib (Morocco) da Jazaa'ir (Algeria) don haduwa da manyan Malaman Sufanci, Farkon Malaminda Shehu tijjani ya soma haduwa dashi a tafiye tafiyensa, shine Shaikh Tayyib bn Muhammad bn Abdullahi bn Ibrahim Alyamlahi, a wani gari mai suna WAZAAN, sannan ya hadu da wani Shaikh Muhammad bnl Hasan Alwanjaliy, hakanan ya ziyarci Shaikh Abdullahi bn As-sayyidl Arabiy bn Ahmad Al'andalasiy a birnin Faas.

Haqiqa shehu Tijjani ya hada Dariqu 3 a zamansa a Morocco (Magrib), sune:

1: Dariqar Qaadiriyyah.
2: Dariqar Naasiriyyah.
3: Dariqar Abil Abbas,

Ahmadul Habib bn Muhammad, wanda akewa laqabi da Al-Gamaariy, to amma sai shehu ya bar dukkan wadannan dariqu, sannan ya karbu wasu Azkar daga Shaikh Abil Abbas Ahmad Attawaash attaaziy, hakanan suma wadannan Azkar din ya watsar dasu.

Sannan shehu yayi Qaura daga Magrib (Morocco) zuwa Qasashen sahara, da nufin Haduwa da Zaawiyar Shaikh Abdulqadir bn Muhammad Al-Abyad, sai ya zauna a nan tsawon lokaci, sannan yayi qaura zuwa TILMISAAN, sannan yayi Qaura daga TILMISAAN yayi nufin aikin Hajji, dakuma Ziyartar Qabarin Annabi s.w.a, akan hanyarsa ta aikin Hajji, ya ziyarci wani gari mai suna IZWAAWI, inda Shaikh Abi Abdullah Muhammad bn Abdur-rahman Al-Azhariy yake, kusa da birnin Jazaa'ir, ya karbi Dariqar Khaluwtiyyah a wajensa, hakanan ya biya ta Tunusiya akan hanyarsa ta Hajji, wannan duk a shekarar 1186hijriyyah ne,
1773miladiyyah, a Tunusiya ma, ya hadu da malamai masu yawa, kamar su: Shaikh Abdus-samad Arrahwiy, sai ya zauna anan shekara guda, yana kai-komo tsakanin Tunusiya da susah!

Ya kwashe lokaci yana karatu anan, inda ya karanci littafin AL-HUKMUL ATAA'IYYAH da wasunsa, har saida Amir din Tunusia yayi mamakin hazaqarsa, sai ya bashi kyautar gida, yakuma yanka masa Albashi duk wata, duk wannan, abisa yardar Sayyid Aliyu Harazimi ne!

To bayanda shehu ya lura cewar Amir nason zaunar dashine A tunusiya zaman din-din-din, sai shehu ya sulale zuwa Misrah batareda sanin kowa ba, ya sauka a Al-qahirah, inda anan ya hadu da Malaminsa Mahmudul Kurdiy, sannan ya miqe da tafiyarsa har ya isa Birnin Makkah a shekarar 1187 hijriyyah.

Nan zan saka Aayah, inshallah, gobe zan tashi daga yanda Shehu ya kasance A birnin Makkah (Allah ya kareta).

Wassalamu alaikum wr wb.

Adam sani Abu-Umayrah.
7/7/2014m, 10/9/1435h.


** MAGANAR GASKIYA GAMEDA DARIQAR TIJJANIYYAH** (3)

CI GABA DA TARIHIN SHEHU TIJJANI 3

Assalamu alaikum, a jiya na tsaya ne akan inda Shehu Tijjani ya isa Birnin Makkah, inshallah zan ci gaba yanzu:

"A birnin Makkah, shehu Tijjani ya hadu da Sheikh Ahmad bn Abdullahi Al-Hindiy, ta hanyar dalibinsa (dalibn Al-hindiy), sai shi wannan Malami (Ahmad Al-hindiy) ya aikawa shehu tijjani busharar cewa shine zai gaaji iliminsa da kuma sirrikansa.

Bayanda ya gama aikin hajjinsa, sai yatafi zuwa Madinah, ananma ya hadu da Sheikh Muhammad bn Abdulkarim Assimaan, wanda yayiwa shehu Tijjani guzirin Sirrikansa wadanda suka kebanci sunaye.

Sai shehu ya baro yankin Hijaz, inda ya komo Misrah, inda ya sauka wajen Malaminsa Mahmudul kurdiy, Bayanin Mahmudul kurdiy ya gabata a darasi na 2, shine wanda yaba shehu Tijjani dariqar Khaluwtiyyah.

Sannan ya tashi daga Misrah ya kama hanyar Garin Magrib (moroco), inda ya kama hanya daga Tunusiya, har ya aje sandar tafiyarsa a Tilmisaan, ya tsaya anan yana mai Ibaadah dakuma shiryar da mutane zuwa ga Allah, sannan yayi tafiya zuwa birnin Faas don Ziyarar qabarin Maulaa Idris, Kakan Sharifai Aliwiyyai mazauna Magrib (moroco) a shekarar 1191hijriyyah/1777miladiyyah.

A wannan tafiyar ne ya hadu da Dalibinsa mai biyayya Aliyu Harazimi, a birnin Wajdah, shima yana kan hanyarsa ne ta Zuwa Faas, sai suka tafi tare zuwa Faas, inda Shehu Tijjani ya bashi Dariqar Khaluwtiyyah, yabarshi anan Faas, shikuma ya koma Tilmisaan.

TO ANAN AKASOMA TUFKA DA WARWARA! Tsakanin Aliyu Harazimi da Malaman Tarihi na Magrib, wadanda sukai rubuce-rubuce gameda Tafiye-tafiyen Shehu Tijjani a wannan lokaci.

Sanannen Malamin Tarihin nan, Muhammad bnl Qaasim Az-zayyaaniy yace: Bayanda SHEHU TIJJANI yakoma Tilmisaan, ya soma wani kasuwancine da ake kira IKSIYR/KIYMAA'U, wannan wata sana'ace ta Algush, inda ake hada baqaqen qarafuna da wasu sinadarai, sai sukoma kamar Zinari. Shehu tijjani bai tsaya anan ba, Har saida ya soma buga kudaden Jabu (Fake money/NUQUWDUZ-ZAYF). Inda aka Kama shi aka kaishi kotu, anan akai masa Bulalai kuma aka sanyashi a Bursinah (Prison/SIJN), qarqashin Shugaba Muhammad bn Uthmaan At-turkiy, wanda yayi shugabanci a tsakanin shekarun 1766-1791Miladiyyah/ 1180/1206Hijriyyah. Bayanda shehu Tijjani ya gama zaman gidan Kaso, sai aka koreshi daga Garin Tilmisaan, aka hana masa zama a dukkan yankin dake qarqashin mulkinsa,

Da haka Shehu ya koma Zuwa Shilaalah, sannan aqarshe yazauna a wata Al-qarya mai suna: Abiy Samguwn, a tsakar sahaara, tayanda hukuma bazata isa gareshi ba.

Ku duba Littafin Dr Jamil Abu-Nasr mai suna: The Tijjaniyyah Asufi order in the Mordern Age, Page 19.

Kash....... Laifin dadi Qarewa, Jama'a kubiyoni gobe inshallah dan jin Yanda ta kasance da Shehu bayan zaman kaso da kuma korarsa da akai. Dakuma maganganun Masana tarihi gameda wannan Badaqalar ta shehu Tijjani.

Wassalamu alaikum wr.

Adam sani Abu-umayrah.
8/7/2014m dai dai da 11/9/1435h.


** MAGANAR GASKIYA GAMEDA DARIQAR TIJJANIYYAH ** (4)

CI GABA DA TARIHIN SHEHU TIJJANI 4

Assalamu alaikum wr, yan uwa barkanmu da saduwa a wannan lokaci, a darasin jiya, munji bayani kan dalilinda yasanya aka kori shehu Tijjani daga Yankin Jazaa'ir, to amma yana da kyau muyi wai-waye, wanda hausawa sukace:

Adon Tafiya!

Sanin Shehu Tijjani da sana'ar juya baqinqarfe zuwa Zinari, da kuma buga kudaden jabu, bai kamata ya zama abin jayayya ba da kai ruwa rana, domin musun wannan juyawa gaskiya baya ne, sabida wannan batu arubuce yake tarihi ya riqe shi har shudewar zamani!
Kuma wannan magana sananna ce a bakin Dalibansa da wadanda sukai zamani dashi!

Al-Qaadiy Sukairaj Al-iyaashiy yana cewa, yana mai kariya ga shehu tijjani akan tuhumarsa da Algush da buga kudin jabu: Lallai masu Jingina wannan harka ga Shehu Tijjani dayan biyu ne su:

1: kodai Almajirinsa (Muridiy) jahili, ya jingina hakan ga shehu a matsayin karaamah, kuma a matsayin shehu yasan kan wannan harka. Amma batun aikata Algush da kudaden Jabu, wannan qage ne akai masa, AMMA KUMA GAMEDA SANIN TA, SHEHU YASAN YANDA AKEYINSU, KUMA JIGA JIGAN MASU AIKATA WANNAN SANA'A SUN SANSHI, wannan ba baqon Abu bane, kuma muma mun tabbatar da yasan wannan harka!

*Jama'a ku duba kuga tufka da warwara*

2: Ko kuma wadanda ke jingina wannan Badaqalar ga shehu sune masu adawa dashi, domin su sanya shakku gameda shi.

To Amma, idan Muka duba wannan Maganar ta Qaadiy Sukairaj, zamu samu abubuwa kaman haka:

1: Ana jingina sanin Harkar KIYMIYAA'U (juya baqin qarfe zuwa zinari ta hanyar amfani da sinadarai) da kuma buga kudaden Jabu, kuma mabiyansa suma sunsan hakan,

2: Mabiyansa sun rabu gida 2 gameda jingina masa Ilimin Kiymaa'u:

A: Bagarenda suke Jahilai gameda jingina masa wannan sana'a, sabida tsammaninsu na cewar wannan karaamah ce gareshi, sai suke hadawa da buga kudin jabu.

B: Bangarenda suke masu ilimi, suna jingina masa ilimin amma suna kore masa buga kudaden jabu.

3: Lallai Shehu Tijjani yana daga Manya-Manyan a cikin Harkar Kiymiyaa'u (juya baqin qarfe yakoma kamar zinare), sabida haka ba baqon abu bane don yasanta, dalili kuwa shine maganar Qadiy Sukairaj: ((Amma saninsa -shehu- ga wannan harka, wannan yana daga ilmummukanda yasani, kuma jiga-jigan masu harkar sun san shi a harkar)). Abin nufi anan shine: shima yana daga Manya Manyan a harkar, domin da ace shi Sukayraj baya cikin manya manya a harkar, da yace: (sabida haka muke kore sanin harkarnan kwatakwata ga shehu) to amma sai yace: (bama mamakin sanin shehu ga wannan harka).

Inshallah nan zan tsaya, gobe da yardan Allah zan ci gaba!

Adam sani Abu-Umayrah.
9/7/2014 daidai da 12 ramadan, 1435hijr.


**MAGANAR GASKIYA GAMEDA DARIQAR TIJJANIYYAH**
(5)

CI GABA DA TARIHIN SHEHU TIJJANI 5:

Assalamu alaikum wr, yan uwa barkanmu da saduwa a wannan lokaci, dafatan Allah ya karbi Ibadunmu, kamar yanda dayawa suke min kiran in dinga sanya Marja'a (reference) na maganganun da nakeyi, inshallah zan dinga sanyawa qarqashin kowanne bayani!

"2: Malamin Tarihin nan na Magrib, Muhammad bnl Qaasim Azzayyaani, wanda ya rubutu qissar Kama shehu Tijjani a Tilmisaan, da kuma kaishi kotu bisa Laifin Sarrafa Zinari na Jabu da kuma buga Kudaden Bogi, sannan aka masa hukuncin DUKA, da zaman Gida Prison sannan aka koreshi a qarshe daga garin,

wannan Malamin yayi zamani da shehu Tijjani, kuma sun rayu tare a yanki daya, shehu Tijjani ya mutu gabaninsa da kusan shekaru 18. Ku duba littafinda shi Muhammad bn Qaasim din ya rubuta, inda ya kawo wannan labarin: 1: At-Turjimaanil Kubraa.

2: Ar-Raudatus-sulaymaaniyyah fi mulukid-daulatul ismaa'iyliyyah waman taqaddamahum minadduwal Al'islaamiyyah.da kuma Littafin Dr. Jamil abun-Nasr (The tijjaniyyah a sufi order in the Modern Age).

Hakanan Labarin koran da Muhammad bn Usman Al-Baayi At-turkiy yayiwa shehu tijjani daga Tilmisaan, inda shehu ya koma wani yanki mai suna Abu-Sangon, wannan labari ya tabbata a littafin Malamin Tarihin nan na Magrib Sheikh Ahmad Khaalid Annaasiriy, cikin littafinsa: Al-istiswqaa'ulakhbaarul magrib Al-aqsaa. Inda a ciki yake cewa: ((a wannan shekarar ce 1211H, shehun Sufanci Abul-Abbas Tijjaniy ya isa Faas, inda ya zauna anan, Bayanda Baye Muhammad bn Usman shugaban Wahran ya koreshi daga Tilmisaan, zuwa Yankin Abu-Sango, ya zauna anan, mutanen garin suka amsheshi, sannan bayan rasuwar Baye Muhammad bn Usman, dansa Usman bn Muhammad ya gaje shi, sai ya samu Labarin Shehu Tijjani, sai Ya aika zuwa ga mutanen Abu-Sangon yana mai jaa masu kunne da su gaggauta koran Shehu,

sanda shehu yaji wannan bayani, sai ya fice da iyalansa da kuma wasu daga Almajiransa zuwa Faas). Ku duba Littafin: Al-Istiqswaa'ulAkhbaarul Magrib Al-Aqsaa, Vol 8 page 105.

Wannan Bayani kenan, inshallah Gobe zamuji Bayanin Shehu Harazimi, wanda shima ke tabbatar da cewar shehu dai Ya Tafka Ta'aasa, shehu Ya Aikata Algush, yana sanyawa baqin Qarfe sinadarai su koma kamar zinare, sannan yana buga kudaden Jabu!

Allah ya mana Tsari daga Al-Gush da Cuta, Allah ka bamu ikon haqura da Halal.

Fi Amaanillah.

Adam sani Abu-Umayrah
10/7/2014 eqvlnt 13/9/1435h


**MAGANAR GASKIYA GAMEDA DARIQAR TIJJANIYYAH**(6)

CI GABA DA TARIHIN SHEHU TIJJANI 6:

Assalamu alaikum, Barkanmu da saduwa a wannan lokaci, sannan Ina mai sanar Maku da cewar: Ina karanto Wannan Bayanai ne daga littafin: TUHFATUS-SANIYYAH BI TAUDIHI DARIYQATUT-TIJJAANIYYAH, wanda: Muhammad Tahir Me-Gari Al-barnawiy, Lakchara a jami'ar Bayero, a bangaren Karatun Islamiyyah ya rubuta.
Masu son Littafin suna iya Tuntubata, ko kuma su bincika cikin Birnin Kano.

"Koma dai menene gaskiyar zancen, Shehu Tijjani dai yabar garin Tilmisan. Ashekarar 1196h, inda ya koma Sahara har ya sauka a Shalaalah, sannan a qarshe ya zauna a Abi-samgon, sannan yayi tafiya zuwa Tuwaat, inda ya hadu da Malamai anan, sukai Musaayar ilimi da fa'idoji, sannan yakoma Abi-Samgon karo na biyu, bai sake fita daga cikinta ba har saida Fatahi yazo masa, inda yace wai Annabi s.a.w ya tantance masa wuridi wanda ya amince masa ya dinga Laqqana shi ga Jama'a, dakuma Tarbiyantarsu dashi, hakan kuma ya farune ido Farke ba a barci ba, kamar yanda Aliyu Harazimi ya riya, a shekarar 1196h. Wannan wuridin shine istigfaari, da salaatin Annabi s.a.w a karon Farko, amma sanda Hira takai 1200h, sai Annabi s.a.w ya cike masa Wuridin da Laa'ilaaha illallaah. (Jawaahirul ma'aani:51).

Shehu tijjani yaci gaba da zama a Abi-samgon, dalibansa makusantansa suka dinga ziyartarsa nan, irinsu Sayyid Aliyu Harazimi, Sayyid Muhammad bn Mashriy da ire-irensu a shekarar 1203h. A haka suka dinga yawaita ziyartarsa lokaci bayan lokaci, har suka zauna a wajensa a qarshe. Sannan yai qaura daga Abi-Samgon Jamhoriyar jazaa'ir zuwa Birnin Faas a Masarautar Magrib Al-Aqsaa, tare dashi akwai Goma daga Manyan dalibansa. (Istisqaa'il akhbaaril Magrib al-aqsaa vol 8/pg: 105).

To amma anan Sayyid Aliyu Harazumi ya tuqe akan dalilin Qaurar Shehinsa daga Abi-Samgon, wanda ya halarci wannan lamarin da idanuwansa. Sai dai Sayyidil Arabiy ibn Saa'ikh wanda yazo daga bayansa yace: ((Sannan bayanda Lamarin wannan Dariqar Muhammadiyya ya yadu, kuma ta bazu cikin Garuruwan Magrib da gabashinta, da kuma bazuwar Lamarin Shehu Tijjani cikin cikar daukaka da kamaala, sai abinda ya bayyana agareshi ya baiyana na yin qaura, sai yayi qaura daga Abi-Samgon zuwa Faas. (Bug'yatul mustafiyd: 134).

Amma kuma, Malamin Tarihin nan Magrib Azzayyaaniy, wanda yayi zamani da shehu tijjani, ya Ambaci dalilin Qaurar shehu, ya tabbatar da cewa dalilin Qaurar itace: Bayanda shugaban Jazaa'ir Usman ya korai daga Tilmisaan zuwa abi samgon, dayawa daga Qabilar Baraabira, suka dinga qaruwa kadan-kadan suna yawa, sai Shugaban Wahran Usman bn Muhammad Mahukuncin Jazaa'ir wanda ya korai daga Tilmisaan, zuwa nan, ya Umarci mutanen Abi samgon da su kori shehu tijjani daga Al-qaryarsu, kuma ya ja kunnensu idan har basu korai ba, sai shehu tijjani yayi qaura ya koma Faas tareda 10 daga Almajiransa.

Koma dai menene, Shehu Tijjani ya Zauna a Birnin Faas, inda Sarki Sulaiman Sarkin Magrib yayi Maraba da zuwan shehu Tijjani, kuma ya baashi kyautan Gida, inda yazauna cikin wannan gida Har rasuwarsa a shekara ta 1815m/1231h, bai bar Birinin Faas ba tunda ya komata sai sau daya a shekarar 1813m/1227h inda ya ziyarci Mahaifarsa Ayn Maadi.

Inshallah gobe zamuji Halinda Shehu ya shiga bayan komawarsa Faas, dakuma irin Makircinda ya hadu dashi.

Fi amaanillah.

Adam sani Abu-Umayrah
11/7/2014 eqvlnt 14/9/1435h.


**MAGANAR GASKIYA GAMEDA DARIQAR TIJJANIYYAH**(7)

CI GABA DA TARIHIN SHEHU TIJJANI 7:

(Domin Karanta wannan Rubutu daga na 1 zuwa na 6, ka shiga wannan Rariyar:
https://m.facebook.com/notes/?id=100005773392985&refid=21)

Baayan Garqame Shehu Tijjaaniy daga #Tilmisaan bisa laifin #Buga_Jabun_kudade da Damfara, aka yanke masa hukuncin Bulaala da zaman gidan Maza, sannan aqarshe a koreshi!

Da aka koreshi bayan shan wancan horo ne sai ya koma Abu-Samgon, anan ma Sarki Usman bn Muhammad shugaban Jazaa'ir, ya sake Umarta da a Koreshi daga wannan Gari! Anan ne Shehu Tijjani ya koma Birnin FAAS cikin Qasar Magrib (Moroco).

To Baayan isar sa Faas, ya hadu da turjiya daga Manya Manyan Malaman wannan Birni, amma Allah ya masa gyadar doguwa bisa samun Goyon Baayan Sarkin wannan gari da yayi.

A karon Farko: da isarsa Birnin Faas, yana sallah ne a Masallacin Maulaa Sulaimaan, Sannna yake komawa gidansa don wazifa tareda Almajiransa da suka zo tare! Sai yayi nufin gina Zaawiya (Tsangaya) taashi ta musamman a wani wuri da ake kira HAUMATUD-DARDASI, amma mutan gari sukai masa chaa, don ganin baiyi wannan aiki ba, amma sai Sarki ya shiga Lamarin a qarshe akai ginin.
Abinda zai qara baiyanar da tsabullar Qiyayya da wannan Mutumi ya fuskanta daga wadannan malamai da suka san Halinsa shine, Shugaban Majalisar Malamai ta Shuwra, ta Sarkin Moroco, Sheikh Tayyib bn Kairaan ya Chachchaki Tijjaani, wanda da zuwansa Sarki ya sanyashi cikin Mambobin wannan Majalisi, yace: Da'awar wannan Mutumi ta cewa shi Shehin Sufanci ne, kuma shi ya karbi dariqarsa ne daga Annabi s.a.w kai tsaye kuma a Farke, wannan Qarya ne kuma Qaage ne!!

Kai sai da takai da Shehu Tijjani ya fuskanci irin wannan Qalu bale mai nauyi, da kuma tuhumarsa bisa Qaryar Karbar dariqa daga Annabi s.a.w, ya soma shirin Gudun Hijira zuwa #Syria.
Amma dukda wannan Shehu Tijjani ya samu daamar Rayuwa cikin Lagwada! Domin kuwa yayiwa Duk wanda ya Masa Hidima koda ta kwabo 1 ce, kai koda Lomar Abincine Alqawarin Shiga Aljannah ba tareda Hisabi ba ko wahala! Hakan yasanya Mabiyansa suka dinga kwararo masa Kyaututtuka na kudade da abubuwan Rayuwa, dukda cewa basuda yawa, saidai Gaalibinsu Masu Hannu da Shuwni ne! Qaari bisa Albaashi da Sarki
Sulaimaan ya yanka masa duk wata yana karba,

(Al-istiqsaa'u:105),

Da kuma kyaututtuka da yake taatsa daga Almajiransa daga Abu-Samgon da Tilmisaan!
(The Tijjaniyya Asufi Order in the Modern age, na Dr Jamil Abu-Nasr:20-22).

Kuma fa, Shehu Tijjani ana qirgashi cikin Masu Kudi na wannan Lokaci, domin ba qananun kudade yake taarawa ba, Sai da takai yanada Yan-aike da yake aikawa gari-gari don karbo kyaututtuka!

Amma sabida Rainin Hankali irin na Shehu Aliyu Haraazimi, acikin Jawaahirul Ma'ani, yake cewa:

"Taarin dukiya da shehu Tijjani ke ciyarwa ga iyalansa da Mabiyansa, da kyaututtuka da yakewa Mabiyansa da abokansa, da kuma wadanda yakeson ribata, duk wannan Uba-Uban Dukiya na zuwa masa ne ta Hanyar Karaamah, domin bai mallaki komai ba, kuma bai karbar komai daga Kowa"

-Jawaahirul-Ma'aani:95.

Jama'a kunga inda aka soma, Domin kowa yasan Annabawa Kasuwanci suke, kuma kowa yasan Yanda Nana Khadijah r.a da Sayyadina Abubakar r.a Umar suka ciyar da Dukiya ga Manzon Allah s.a.w da Da'awarsa, Allah bai bude masa Taska daga sama ba, amma Shi Shehu sabida shi na Musamman ne, Allah ne ke Bubbugo masa Dukiyar iya son ransa, inda sai da yazamo Dangoten Zamaninsa!

Mu hadu a rubutu na gaba.


**MAGANAR GASKIYA GAMEDA DARIQAR TIJJANIYYAH**(8)

CI GABA DA TARIHIN SHEHU TIJJANI 8

To koma dai ya abin yake, Abu sananne shine: Shehu Tijjani har ya Mutu bai rubuta koda qwayar Takarda ba da sunan littafi, wanda a iya komawa garai ya zama ginshiqi ga wannan Da'awar dariqanci da yayi!

Sai dai Manya Manyan Almajiransa sun rubuta littafai a matsayin sa, domin cike suke da Umarce Umarcensa, da kuma karantarwarsa, wadannan Littafai guda 3 sune Ginshiqi na wannan Dariqa ta Tijjani, littafan kuwa sune:

1: JAWAAHIRUL-MA'AANIY WA BULUGUL AMAANIY FI FAYDI ABIL-ABBAAS ATTIJJAANIY. Wanda Sayyid Aliyu Harazimi ya rubuta.
Wannan Littafi ana daukansa a matsayin kundi na Tarihin Shehu Tijjani, domin shine ya dinga Karantowa Aliyu Harazimi wasu daga tarihinsa, shikuma Harazimi na rubutawa, Duk da cewa: Ba duka littafin ne Aliyu Haraazimi ya rubuta ba, ko kuma Shaftar Tijjaani, Kawai dai Yayi nufin wani littafine rubutacce:

(Al-Maqsadul Ahmadi Fit-ta'ariyfi bi sayyidnaa ibn Abdullaahi Ahmad) wanda Sayyid Muhammad bn Abdus-salaam Al-qaadiriy ya rubuta cikin Tarjamar Malaminsa Ahmad Ma'an bn Abdullahi Al-andalasiy, wanda ya rasu a shekara ta 1130H/1708M!

Sai Shi Aliyu Haraazimiy ya Saci wannan littafi ‪#coppyright‬, inda ya kwafe Muqaddimar Littafin Harafi da Harafi ba chanji, sannan Ya dauki Tsarin Babukan Littafin yajerosu yanda suke ba chanji, ya dinga Goge sunan Ahmad Ma'an yana mayeshi da Shehu Tijjaani a duk wurarenda shi Wancan Almajirin ya kwarzanta gwanin nasa baqaadire!

Kai Hatta Qasiydu da Baitoci da wannan Baqaadire ya Yabi Malaminsa Ahmad dasu, hakanan Harazimi ya kwafosu sai ya chire sunan Ahmad ya sanya Tijjani!

Hakanan bai tsaya anan ba, sai da ya dibo Amsoshinda shi wannan Shehi Ahmad Ma'an ya ba wa Almajirinsa Muhammad bn Abdus-salaam, ya lanqwasasu a matsayin shine yayi Tambayar Tijjani ya Bada Amsa!.

Bayan gama wannan aiki ne, yaje ya karanta wannan abu dayayo gaban shehu Tijjani ranar 28/sha'aban 1216H, a Masallacin Diwaan dake Faas. Amma sai shehu Tijjani ya Waffaqa wannan littafi, dukda yasan cewa bashi ne yayi wadannan fatawowi ba, bashida Taguwa ciki balle raqumi! Ya dinga jingina littafin ga kansa!

Kai abin bai tsaya nan ba, saida shehu Tijjani yace: ai Annabi s.a.w ne ya baiyana gareshi a farke zaahiri yace masa: WANNAN LITTAFI (Jawahirul ma'aani) LITTAFINA NE. Wato Annabi ne ya rubutashi da hannuwansa.

A rubutu na gaba zakuji Yanda aka Bankado wannan Badaqala da saatar Fasaaaha tun A wancan Lokaci, gamida yanda Ahmad Sukairaj ya tabbatar da wannan saatar Fasaaha! Amma dukda haka Shehu Tijjani yace nasu ne, Kuma Annabi s.a.w yace Littafinsa ne!!!!!!!

Yan-uwa kunji yanda abin ya soma!

Ga duk wanda bai yarda da bayaanan nan ba, qofa bude take domin Tattaunawa!!!!


**MAGANAR GASKIYA GAMEDA DARIQAR TIJJANIYYAH**(9)

CI GABA DA TARIHIN SHEHU TIJJANI 9

Hakanan Wannan Saatar fasaaha ta kasance a boye har zuwa shekarar 1347H/1921M inda aka Wallafa wannan littafi na Jawaahirul Ma'aaniy.

Riskar wannan littafi keda wuya, sai Manyan Malaman Moroco sukai Chaa akansa, irinsu Maulaal-Arabiy Al-Alawiy, Babban Maalamin Salafiyyah a Moroco a wannan lokaci, da Sayyid Abdul-Hayyil Kitaaniy! Suka hadu don bankado lamarin Aliyu Haraazimi tare da Malaminsa, inda suka buga littafin "Al-Maqsadul Ahmad" shekarar 1351H/1932M, domin ya kasance ba a wallafe yake ba, da nufin tono Asirin Tijjaniyyah da Makafinta, don ankarar da mutane illarta da kuma nusar da mabiyanta game da ita.

A Haka shehu Tijjani ya soma Raba Dariqarsa da bada izinin wurdodinsa gamida izinin Karanta Jawaahirul Ma'ani da cewa Littafinsa ne! Kamar yanda ya rubutawa daya daga cikin Almajiransa Sayyid Muhammadut-Tihaam bn Sayyidil Makiy bn Rahmuwn.

To amma dukda haka, sanda Alhaji Ahmad Sukairaj babban dan Chakaren Tijjaniyya qwal a Moroco ya riski wannan Tonon Asiri da kuma Zigidir da akaiwa Dariqarsa da Malamansa, gamida Tuhumarsu da Satar Fasaaaha, sai ya rasa yanda zaiyi ya wankesu daga wannan Zargi, don bai isa ya qaryata su ba, sai yace:

"Haqiqa Mutane masu bibiyan kusakurai a littafin Jawahirul Ma'aaniy sunyi suka akansa, wanda Babban Khalifah Sayyid Alhaaji Aliyu Harazimi ya rubuta, da cewar Saatar Fasaaha ce daga littafin "Al-Maqsadil Ahmad" wanda Allaamah Abit-tayyib Alqaadiriy ya rubuta, ya rubutashi ne akan Waliyyi Saalihi Abil-Abbas Sayyid Ahmad bn Abdullahi Ma'an...............

Haqiqa na samu bugu 3 na wannan littafi, kuma na gwada su da littafin Jawaahirul Ma'aaniy, sai na samu Khutbarsa irin tashi ce, hakanan mafi yawan Jerin Baabukan Jawaahirul Ma'aani, irin naasa ne, amma abinda ya danganci Dariqanci da Mas'aloli na ilimi, na Hadisi da Fiq-hu da maganganun shehu Tijjani da matsayarsa, ba abinda yake dayane tsakaninsu anan in baicin wadanda wadannan Malamai suka hadu akansu, har ya zamana sai kaga tamkar wannan ne wancan, wannan kuma ba abunda za'aqi yarda dashi bane ga kowanne mawallafi.......................

AMMA IDAN YA ZAMANA MANYAN MALAMAI NA CIRATO LITTAFAI DAGA ASALINSU ZA'A JINGINA MASU SU NE (su da suka cirato su) DUK DA CEWA ANSAN WADANDA SUKA RUBUTA LITTAFIN ASALIN, DON ALHMDLH, BA MATSALA A KWAIKWAYON JAWAAHIRUL MA'AANIY A (Al-maqsadul ahmad)".

Wannan kai tsaye na shi kansa Ahmad Sukairaj ya yarda cewa ‪#Saatar_Fasaaha‬akai a Jawaahirul Ma'aniy!

Amma sai dai kash, ya kaasa ya Fada mana Malami guda 1 a duniyar ilimi da Adabi, da yaje yayiwa Littafi ‪#Naqlul_Harfiy‬(kwafa ta harafi bisa harafi) sannan yazo yace wannan littafin, nasa ne!
Balle kuma yace wai Na Annabi s.a.w ne, to idan Photo-Coppy din na Annabi ne, shi kuma Master-Coppy din na waye????

Mu hadu a rubutu na gaba don jin littafi na 2!


**MAGANAR GASKIYA GAMEDA DARIQAR TIJJANIYYAH**(10)

CI GABA DA TARIHIN SHEHU TIJJANI 10:

Littafi na 2 da zamu duba bayan Jawaahirul Ma'aani shine:
2: "الجامع للعلوم الفئضة من بحر الخطبالمكتوم"
Wanda Sayyid Muhammad Mashariy ya rubuta, wanda ya rasu a shekara ta 1224H, wannan Mutumi Almajirin Shehu Tijjani ne shim, kuma duk abubuwandake rubuce cikin littafin nan, suna qarfafan wadanda ke cikin Jawaahil Ma'aani ne! Amma sai dai har yanzu ba'a buga wannan littafi ba, yana a rubuce ne kawai.
3: "الإفادة الأحمدية لمريد السعادة الأبدية"
Wannan littafi Sayyid Muhammad Tayyib Assufyaaniy ne ya rubuta shi, wanda ya rasu a 1259H!
Assufyaaniy yazamo nakusa da shehu Tijjani a Birnin Faas, yana rubuta dukkan Maganganun shehu tijjani, sannna ya jerasu a tsarin haruffan larabci, sannan sai yake masu ta'aliqi gwargwadon saninsa!

Wannan Littafi dukda qanqantarsa, shine mafi girma a wadanda suka Qunshi Tsantsar Karantarwar Tijjaaniyyah! Wanda Shehu Tijjani ya koyar da makebantan Almajiransa, domin Jawahirul Ma'ani kamar yanda mukai bayani, ba dukkansa ne na shehu Tijjani ba, Kwafe akai da "Al-maqsadul Ahmad".

Wannan Littafi sabida qanqantarsa, yayi sauqin yaaduwa a Moroko baayan Mutuwar Tijjaani, hakan ya sauqaqa yaaduwar Aqidun Tijjaaniyanci, wanda ya janyo hankalin Malamai inda suka dirar mata da Malamanta sabida muninta! Abun ya tsananta garesu, sai Manyan Dariqar suka yanke shawarar Karbe littafan daga Hannun Muridansu suna laalata su.
Don Hakane ma Al-Haafizul Jazaa'iriy yayi nufin rage kaifin wannan matsin lamba, inda ya shiga littafin nan ya dinga cire abubuwanda yake gani sune masu matsala, yabar masu daama-daama, inda ya dinga masu taawili irin nasa, kamar yanda yake a Ta'aliqinsa a littafin, hakan ne yasa bazamu iya samun asalin littafin ba ko abinda ya qunsa, sai dai a cikin Manya Manyan tsoffin Littafan Tijjaniyyah, Kamar irinsu Ramaahu na sheikh Umarul Futiy!

MAKOMAR MAGABATAN TIJJAANI A IDONSA da kuma FALALAR MABIYANSA:
Yana cewa:
"أعمار الناس كلها ذهبت مجانا إلا أعمار أصحاب الفاتح لما أغلق, فقد فازوا بالربح دنيا وآخرى, ولا يشغل بها عمره إلا السعيد"
(Rayuwar Mutane dukkanta ta tafi a #Banza in ba ta ma'abota salaatul Faati lima ugliqa ba, domin sun rabauta da ribar duniya da lahira, babu wanda zai shagaltar da rayuwarsa da ita face shiryayye/Dan Aljannah) -Fat-hur-rabbaani:22-, Ramaahu:2:5.

Anan wurin kunga a baiyane take, Ya gama cin Mutuncin Manzon Allah s.a.w da Sahabbansa, ya gama cin mutuncin Annabwa r.a gabaki dayansu da dukkan wadanda suka gabace shi! Domin yace #Rayuwar_Mutane_ta_tafi_a_banza_sai_ta_Mabiyansa_kawai! Anan Tambaya: Shin Annabi s.a.w yana cikin Ma'abota Salaatul Faatih? Annabawan Allah gaba dayansu suna cikinsu? Sahabbai r.a suna cikinsu?
Amsar da mutum 2 bazasuyi sabani a kanta ba itace: BASU CIKIN YAN-DARIQAR-TIJJANI! Ashe kenan #Sunyi_Rayuwar_Banza kenan? Don Allah wane cin mutunci yakai wannan? Wane zagi ya kai wannan muni?

Yanzu don Allah idan Babanka ya Mutu sai nace: Babanka Yayi Rayuwar Banza, ya zaka ji a ranka?

To Balle ace Annabi s.a.w da dukkan Annabawa da Sahabbai??????????

A Rubutu na na Gaba zamu tsantsagoron maganganun Tijjani din, da kuma Aqidunsa, kafin daga bisani mu daura da ta Sauran Malaman Sufaye!


**MAGANAR GASKIYA GAMEDA DARIQAR TIJJANIYYAH**

(11)

HAQIQANIN AQIDUN SHEHU TIJJAANI (2) (ci gaba daga rubutuna na 10).

Sanannen Abu ne, akullum iqiraarin Tijjanwa shine Girmama Manzon Allah s.a.w da kusanci zuwa ga Allah, Ta hanyar Qaunar Manzon Allah s.a.w, da kuma Hailala, Istigfaari da sauran Ayyukan Tsarkake Zuciya!
To ammafa duk wanda ya bibiyi Littafan nan na Tijjaanawa zai samu:
1: Allah da suke Magana shine Shehu Tijjani, domin shima Allah ne kamar yanda zan kawo inda ya fadi haka da kansa!
2: Babu wani Annabi bare a kusanceshi, inma akwai bai wuce Inyaas ba!

Domin sun bi sunyi Dumu-Dumu da Darajojin Fiyayyen Halittu s.a.w, zan taqaita da Maganganun Tijjaani din domin abin yafi fitowa fili, baayan Kammala wannan, zanyi na sufaye a dunqule:

1: Yazo cikin Littafin Ramaahu:
"إن الفيوض التي تفيض من ذات سيد الوجود صلى الله عليه وسلم تتلقاها ذوات الأنبياء, وكل ما فاض و برز من ذوات الأنبياء تتلقاه ذاتي, ومني يتفرق على جميع الخلائق من نشأة العالم إلى النفخ في الصور, ويدخل فيه جميع الصحابة رضوان الله عليهم, فيكون أفضل من جميع الصحابة رضوان الله عليهم".
"Lallai kyauta dake kwararowa daga Zatin shugaban Halittu s.a.w Zaatin Annabawa ne ke amsar su, duk abinda ya kwararo kuma ya baiyana daga Zaatin Annabawa, #Zaatina ne ke amsarsa, daga Zaatina ne kuma (Kyautar) Take Rabuwa zuwa #Dukkan_Halittu, tun daga Halittar duniya zuwa hura qaho! Sahabbai r.a dukkansu zasu shiga cikin wadannan, sai (Shehu-Tijjani) ya zama shine mafi Falala daga dukkan Sahabbai r.a" Ramaahu:2:5.

2:ya ce:
"لا يشرب ولي ولا يسقى إلا من بحرنا, من نشأة العالم إلى النفخ في الصور"
(Babu wani waliyi da zai sha, ko ya shaayar face daga Raafinmu, tun daga halittar duniya har zuwa hurar qaho) -Ramaahu:2:5.

3: ya kuma cewa:
"إذا جمع الله تعالى خلقه في الموقف, ينادى مناديا على صوته, يسمعه كل من في الموقف: يا أهل المحشر هذا أمامكم الذي كان مددكم منه"
(Idan Allah madaukaki ya taara halittu a matsaya (filin qiyaamah), mai kira zai kira a bisa #Sautinsa, dukkan wanda ke filin zaiji shi: "Yaaku ma'abota filin qiyaamah, wannan a gabanku (tijjani) shine wanda madadinku (taimako/qarfafawa) ke zuwa daga gareshi"
-Ramaahu:2:5-.

BAYAANI:
*A lamba ta Farko zamuga cewa ya nuna cewa Annabawa na samun kyautane daga Zaatin Annabi s.a.w, hakanan shine yake kwankwada daga Annabawa! Kunga anan wanda bai san kan tsiyar ba zai zaci cewa ya Yabi Annabi s.a.w, to amma #Zaginsa yayi! Dalili kuwa:
-----Bai fada mana inda shi Annabin s.a.w ke kwankwadar kyautar ba, sai a qarshe yake cewa Daga Gareshine dukkan Zaatoci ke kwankwadar kyauta, tun daga Halittar duniya har zuwa tashin duniya! Kunga anan ya hada ya raba!
Don Zatin Annabi s.a.w ya shiga cikin Zatin sauran Halittun nan, hakanan zaatin sauran Annabawa yana cikin wannan zaatocin, a qarshe abinda zamu fahimta kawai shine:
Dukkan Halittu daga Zatinsa (Tijjani) suke kwankwadar Kyauta da ilimi, tun daga Halittar duniya har zuwa taashinta, tun daga Annabawa har sauran Waliyyah (wannan ma'ana zata fito a jerin bayananda zanyi nan gaba!!!!!

* A Lamba ta 2 kuwa, da yake cewa: "Babu wani waliyyi dake sha ko shaayarwa face daga Tafkinmu tun daga halittar duniya har tashinta"!
Abinda ya kamata ku sani shine: wai WAYE WALIYYI? A dunqule shine: duk wani wanda yayi Imani da Allah s.w.a sannan yake jin tsoron Allah! Annabawa dukkansu waliyyai ne, kamar yanda zamuga a tafiyar sufanci Annabi Adam ba Annabi bane waliyyi ne cikin waliyyai!
So kunga a dunqule dukkansu ya tabbatar da cewa suna diban ilimi ne da duk wani abu da suka zo dashi, daga cikin Tafkin-sa!

* A Lamba ta 3 kuwa nan ne Kafircin yake:
1: Yace Allah baayan ya taara mutane a filin qiyaamah, wani mai kira zai yi kira #Da_Sautinsa!!!!!
Anan tambayar itace: Waye wannan Mai kiran?????
Sannan sautin waye? Lamirin dake kan kalmar #Saut yana komawa zuwa ga wa kenan? Wannan babu shakka yana Nufin #Allah madaukakin Sarki ne!
Yaci gaba da cewa: idan wannan mai kiran yayi kira, dukkan wadanda ke filin Qiyaamah zasu ji kiransa, zaice: YAAKU MA'ABOTA FILIN QIYAAMAH, WANNAN DAKE GABANKU SHINE WANDA MADADINKU KE ZUWA DAGA GARESHI!

Jama'a ku sanifa, a wurin nan akwai Annabawa da Malaa'iku da Sahabbai, kuma sun shige jerin wadanda aka kira, dukkansu zasu saurara suji abinda wannan mai kira zai
Ce, shehu Tijjani yana a gaba ne, gaban duk wadanda ke filin Qiyaamah, #To_Annabawa_suna_ina??? Sannan waye wannan mai kiran? Da sautin wa yake magana??
Saqon-da wannan mai kirari zai isar shine na cewar: daga Shehu Tijjani ne Taimako da Qarfafawa ke zuwa ma duk wadanda ke filin qiyaamah! Kunga Annabawa duk sun shiga ciki, kuma suna chan qasa baayan Tijjaani suna kallo suna saurare! To tambayar da zan saake yi itace: wai wanene keda #Hurumin magana a filin qiyaamah?

Jama'a me yakai wannan Wulaqanci? Ashe annan bai wulaqanta Manzon Tsira Baban Nana s.a.w ba?????? Ashe bai wulaqanta Allah madaukaki ba? Ashe bai jinginawa kansa Allantaka ba?


**MAGANAR GASKIYA GAMEDA DARIQAR TIJJANIYYAH**

(12)

HAQIQANIN AQIDUN SHEHU TIJJAANI (3) (ci gaba daga rubutuna na 10).

4: Ya ce:
"روحه صلى الله عليه وسلم وروحي هكذا, مشيرا بأصبعيه السبابة والإبهامة, روحه صلى الله عليه وسلم تمد الرسل والأنبياء, وروحي تمد الأقطاب والعارفين والأولياء من الأزل إلى الأبد"
(Ruhinsa (Annabi) s.a.w da ruhina tamkar haka ne suke, sai ya nuna yaatsunsa Manuniya da babbar yaatsa, Ruhinsa s.a.w shine ke qarfafan Annabawa da Manzanni, Ruhina kuwa ita ke qarfafar Qutubai da Aarifai da waliyyi, tun azal zuwa abada) -Ramaahu:2:5-.

*A qarqashin wannan Jumlah akwai abubuwa da zamu Fahmta kaman haka:
1: Ya daidaita Kansa da Annabi s.a.w, dukkansu dayane, dukda yana nuna cewar yafi Annabi s.a.w.
2: A qaa'idar kwatance irin wannan, ba'a kwatanci da danyaatsa Manuni da Babba, sai in yaa zamana 1 yafi daya, fifikon ma kuma mai yawan gaske, don hakane ma ya kwatanta kwatantashi da Annabi s.a.w da hakan.
3: Anan ya kamata a Tambaya: Wanene Dan Yaatsa manuni wanene babban yaatsa? Abinda Manufarsa ke nunawa idan muka waigi sauran maganganunsa irin wadannan shine: Shine Yaatsa manuniya, Annabi kuma Babbar yaatsa. Dalili na kuwa shine: Yaace Annabi s.a.w shi ke jagorantar Annabawa da Mursalai, kunga abu 2 kawai yake jagoranta.
Shi kuwa Tijjani yana jagorantar Qutubai, Masana Allah da kuma Waliyyai, kunga anan abu 3 kenan! Sannan sanannen abu ne a Sufanci cewar: #Wilaaya (musamman ta shehunnansu) tafi Annabta! Ballanta kuma #Qutubanci! Wanda Qutubi matsayin Allah yake a wajensu, sabida yana juya duniya da tasrifinta yanda yaso, Lamarinsa kawai #Kun_fa_yakun ne kamar yanda Inyaas ya fadi!

5: Sannan Yace:
"إن قدماي هاتان على رقبة كل ولي الله من لدن آدم إلى النفخ في الصور"
(Lallai ne duga-dugaina wadannan suna kan wuyar dukkan waliyyan Allah tun daga Annabi Aadam har zuwa tashin busar qaho -kenan ya takesu duka-) -Ramaahu:2:5.

Anan kai tsaye yana nuna cewa Matsayinsa ya daqile Matsayin waliyyai tun daga Aadamu har zuwa taashin duniya, Annabaawa dukkansu Waliyyai ne, sannan nan kai tsaye ya ce ya take wuyar su! Kuma idan har baaya nufin Annabi Adam na ciki, me yasa ya sanyashi, bai ce #Munzu_nash'atil_aalami ba kamar yanda yake fadi a wasu wurare, sai ya sanya Aadam? Anan abin a fili yake!

6: A qarshe yake cewa:
"إن مقامنا عند الله في الآخرة لا يصله أحد من الأولياء, ولا يقاربه, من كبر شأنه ولا من صغر"
(Lallai matsayinmu wajen Allah a lahira ba wani daga cikin waliyyai da zai kaishi ko ya kusance shi, wanda lamarinsa ya girmama (yakai ga Annabta) ko kuwa wanda lamarinsa ya qanqanta (ya tsaya a waliyattaka) ). -Ramaahu:2:5-.

Nan ma bata sake zani ba, domin ya fifita matsayinsu na Wilaayah kan dukkan wani waliyi, shin matsayinsa yaa girmama (ya kai ga Annabta) ko bai kai ba, to su su Tijjaani sun wuce shi!

Don Allah ina darajanta Annabi ko Annabta anan?


Koma saman shafi

→Labarai

KAR KUCE : RAMADAN KAREEM! KUCE RAMADAN MUBAARAK! (Anas Assalafiy Fagge)

KAR KUCE : RAMADAN KAREEM! KUCE RAMADAN MUBAARAK! (Anas Assalafiy Fagge)

Domin Ramadan bashine yke bada abinda ake samu na falala a cikinsa ba, balle a kirashi KAREEM.

Allah ne ya sanya masa wannan falalar kuma ya sanyashi wata.

Don haka Allah ne KAREEM shi kuma Ramadan shine MUBAARAK.

Duba Fataawa ibn uthaimin 20/254.

Anas Assalafiy Fagge (Turakin Sa'in Fika).

Back to posts
This post has no comments - be the first one!

UNDER MAINTENANCE

Share|

Kaima shiga a tattauna da kai
* No boards.

Online: Guests: 1


→Ra'ayin jama'a game damu

 IDAN KANA BUKATAR A TALLATA MAKA HAJAR KA A WANNAN SHAFIN DA SAURAN SHAFUKAN MU KANA IYA TUNTUBAR MU TA WADANNAN HANYOYIN KAMAR HAKA:


Email: bjournalist55@hotmail.com

Phone No: 09035830253

Facebook: Basheer Journalist Sharfadi

Address: Ittihad Computer Centre,  No 92 Daneji Kano


MAI TALLA SHI KE DA RIBA


*Bayanan ka*
Browser din da ka hawo Mozilla

Kasar da kake

Adadin Maziyarta 322332

Adadin Wadanda Sukayi Comment 65691

A Wadanda Suka Shiga Tattaunawar Mu 54


Follow @bjournalist55
→Yi Adding Dina Ta Facebook
→Yi Like Na Dakarun Sunnah Page
→Yi Like Dina Ta Facebook

*Shafuka Masu Alaka Da Mu*

→Basheer Sharfadi wordpress
Basheer Sharfadi Blog Spot
UP
→Home

Basheer Journalist Sharfadi (Abu Hafsah)
ISLAMIC DATE
  • phpimg2.php?it&ic=yellow



  • Click to Sms
    Click to Call


    Basheer journalist sharfadi3
    Coollogo com-1281358