Old school Swatch Watches
Google69490f6862051cb8
google-site-verification: google69490f6862051cb8.htmlgoogle-site-verification: google69490f6862051cb8.htmlgoogle-site-verification: google69490f6862051cb8.htmlBasheer journalist sharfadi14

Basheer journalist sharfadi14.jpg6
Basheer journalist sharfadi 11 1
Maraba Da Zuwa Wannan
Shafi Mai Al-barka 1

☀ Zabi inda kake son shiga ☀
Menunks
→Home
→Akidojin Ahlussunnah
→Addinin musulunci (35)
→40 Hadith (50)
→Fadakarwa (120)
→Neman labarai (20)
→Shi'a Kafirci (50)
→Hadith (55)
→Khudubobi (24)
→Tarihin magabata (60)
→Raddi / Maida martani (99)
→Face book post (30)
→Monthly Archives (60)
→Tambaya da Amsa (20)
→Sahabban Annabi {s.aw} (50)
→Taskar maluman sunnah (25)
→Akidar Y'an Shi'a Dangane da Al'kur'ani
→Fassarar Usulussunnah (20)
→Sheik Ja'afar {Rahimahullah} (65)
→Sheik Abubakar Gumi {Rahimahullah} (30)
→Sheik Dr. Muhammad Sani R/Lemo
→Salafiyyah Network Nigeria (100)
→Adam Sani Abu-Umayrah (99)
→Salaf Ustaz (79)
→Malama Ummi Ahmad Katsina
→Malama Amina Saleh Mande
→Labarai (40)
→Nishadantarwa (10)
→Siyasar Nigeria (9)
→Vidio (33)
→Audio (66)
→Hotuna (120)
→Internet Cheat (90)
→Site Achieve
→Application (10)
→Games (8)
→About me (01)

Wannan shafin mallakarCoollogo com-1281358 3
Ne




SHAFI DON KARUWAR MUSULMI
FASSARAN USULUSSUNNAH NA IMAM AHMAD DAN HANBALI Kashi na (3) Daga Abu Jareer Ameer bn Hamza - Basheer journalist sharfadi
Assalamu Alaikum wannan 6angare ze dinga zuwa muku kai tsaye daga dan uwan ku
Adam Sani Abu-Umayrah
Kuna iya binsa ta face book

Wanda ya tsara ya kuma shirya
Basheer journalist sharfadi
Asha karatu lafiya

**DA GASKENE WAI BA'A SAUKAR DA QUR'ANI BA DON A HADDACE SHI?**
(1)
.
Assalamu alaikum wr, Haqiqa Allah ya saukar da Al-Qur'ani mai girmane don a Haddace shi, kuma ayi Zurfin Tunani a cikinsa, amma dayake Haddace Qur'ani ba abune mai sauqi ga kasalalle Rafkananne ba, kuma ba abune mai yiwuwa ga Munafuqi ba, ya sai Aka wayi gari ana mana ALFAHARI DA JAHILCI DA KASALA! Wai Allah bai saukar da Al-Qur'aniba don A haddace shi! Subhanallah! Ba mamaki don ka fadi haka, tunda baka Haddace Qur'anin ba, ga Dalilai kan Haddace Qur'an daga Qur'ani da Hadisi:
.
1: DALILAI DAGA ALQUR'ANI: Allah yace: "Kada ka motsa harshenka dashi don kayi gaggawa dashi, lallai hadashi (a qirjinka) da karantashi na garemu * duk sanda muka karantashi to kabi karatunsa * sannan bayaninsa na garemu (zamu sanar dakai)" -Suratul Qiyaamah: 16-19-. Manzon Allah s.a.w yakasance duk sanda Wahayi ya sakko masa, yana gaggawa wajen karanta Qur'anin a sanda Jibril a.s ke karanta masa, sai Allah ya Umarceshi da ya daina Gaggawa, zai tsare Qur'anin a Qirjin Manzon Allah s.a.w, ya zama a haddace kenan! Don ka gane cewa Haddace Al-Qur'ani shine matakin Farko wajen saninsa, sai Allah ya soma kawo Haddarsa (JAM'INSA) a farko, sannan Tilaawa, sannan sai sanin Tafsirinsa (BAYAANAHU), wannan ne sirrin dayasa Allah ya jero abin daki-daki!
.
2: Allah yace: "Lallai mu muka saukar da Ambato (Alqur'ani) kuma mune masu kariya gareshi" -Hijr:9-. Haqiqa kuwa Allah ya tsare Qur'ani ne ta hanyar mahaddatansa, tun daga Zamanin sahabbai har zuwa yau, domin ba Allah ne zai sakko ba ya dinga Gadin Qur'ani, kuma ba Mala'ikune zasu tsareshi kada a tabashi ba, a'a, Mahaddata Haziqai Jaruman mazaje da Mataye sune Allah yayi Amfani dasu wajen kare Al-Qur'ani, kamar yanda Hadisi ya Tabbata gameda Rubuta Al-Qur'ani a zamanin S. Abubakar r.a! Munga rawar da Mahaddata suka taka wajen Rubuta Qur'ani!
.
3: Don ka tabbatar da Cewar Lallai Qur'ani Haddarsa ake, sai mu jaka zuwa suratul Ankabut Inda Allah ke cewa: "Baka kasance kana karanta wani littafi ba gabaninsa (Qur'ani) bakuma ka rubutashi da hannunka, Ai da sai masu barna suyi shakka * A'a (Shi Qur'ani) AAYOYINE BAIYANANNU A QIRAZAN WADANDA AKA BAWA ILIMI, kuma babu masu jayayya da Ayoyinmu face azzalumai". -Ankabur: 48-49-.
.
Ashe kenan Ma'abota ilimi na haqiqa sune ke Daukeda Aayoyin Qur'ani a Qirjinsu! Kamar yanda Allah da kansa ya fadi, Yasanya duk wani Malami a Duniya, a da ko a yau, zakuga tun yana qaramin yaro ya haddace Qur'ani, shine ginshiqi na farko a duniyar karatu! Amma shi kuwa akasin haka! Qur'ani bai zama a Qirjinsa, don Qur'ani be haduwa da akasinsa a zuciya daya.
.
Babbar Ni'imar da Allah yayiwa wannan Al-ummah tun farkonta zuwa yau itace ni'imar HADDACE QUR'ANI, in muka duba zamuga adadi mai yawa daga cikin Sahabbai sun haddace Qur'ani, har a yaqin BI'IRU MA'UWNAH mahaddata 70 ne sukai shahada, hakanan ya yaqin YAMAAMAH, mahaddata 70 ne sukai shahada!
.
Zamuga cewar Annabi s.a.w yasha tura sahabbansa garuruwa koyarda Al-qur'ani da Addini, kamar Mus'ab bn Umair, wanda ya aikashi Madina, da Abdullahi bn Ummi Makhtum, wanda shi Makaho ne ma, amma dake abin a Qirji ne, da Mu'azh bn Jabal Zuwa Makkah bayan Hijrah don karantar da Qur'ani da Addini! Kuma muga yanda a lokacin sahabbai ke rige-rigen Haddace Al-Qur'ani, da sanya Yayansu zaurukan Haddace Qur'ani, wanda a Qarshe dayawansu sun haddace Qur'ani da Qira'o'I daban daban! In muka dubi Qaramin Misali, lokacin da Sahabbai sukai Hijrah zuwa Habasha, ai Ba Qur'ani suka bude suka karantawa Najjashi ba, a'a Hadda ce!
.
Don Haka in Allah bai sanyaka cikin Jakadun Al-Qur'ani ba masu bashi kariya, to kada ka soki Mahaddatan ko haddar, koda yake masu hikima na cewa: AL-INSAANU ADUWUL-LIMA JAHILA.
.
Zamu hadu a kashi na 2!

→Labarai

FASSARAN USULUSSUNNAH NA IMAM AHMAD DAN HANBALI Kashi na (3) Daga Abu Jareer Ameer bn Hamza

FASSARAN USULUSSUNNAH NA IMAM AHMAD DAN HANBALI
.
Darasi na uku
.
11-Mallam yace: yana daga cikin Sunnoni wajibai wadanda duk wanda yabar wani abu daga ciki(bai yarda dashiba), kuma baiyi imani dashiba, to wannan ba Ahlussunnah bane(sune tindaga gaba na 12 harzuwa na 50):
.
12-Imani da kaddara na alhairi kona sharri, da gasgata Hadisanda suke bayani gameda Kaddaran, da sallama mata/yarda da ita, kuma kada kace: don me?(misali donme Allah ya halicci kaza da kaza?), kuma kada kace: ya akayi? abinda ake bukata kawai gasgatawa dakuma imani da ita(Kaddaran). Duk wanda baisan fassaran Hadisiba amma malamai sukamasa bayani ta littafan fiqhu to wannan ya isheshi kuma za'amar hukunci da abinda ya karanta, dolene yayi Imani da Hadisin dakuma duk abinda ya kunsa kuma ya Sallamawa bayanin magabata akai, misali: Hadisin(Ibn Mas'ud radiyallahu anhu, da Annabi s.a.w yakecewa: lallai dayanku ana tattara halittansa cikin cikin mahaifiyarsa kwana arba'in yana maniyi, harzuwa karken hadisin duba Buhari(3208) da Muslim(2643) da dai sauran Hadisanda suke magana akan kaddara da Hadisanda suke magana gameda ganin Allah dukkansu dana Sunayen Allah dolene ayi Imani dasu kuma kada ayi musun koda harafi daya rak acikin duk Hadisin dayazo gameda hakan ta hanyar Amintattu.
.
kuma kada kayi jayayya da kowa cikin lamarin kaddara hakama kada kayi gogaiyya da kowa, kuma kada ka koyi musu domin musu gameda Kaddara da Kur'ani da makamantansu suna daga ababen ki wadanda aka hana, duk mai aikata haka baya dacewa da Sunnah idan kuma ya dace da Sunnah to dole saiyabar musu da jayayya ya sallama kuma ya yarda da duk ababenda suka inganta.
.
zamu kwana anan, sai in ALLAH yabamu aron rai zuwa darasi na gaba,
.
ya ALLAH ka kara Tsira Aminci Ni'ima ga shugabanmu Annabi Muhammad s.a.w
.
Via:- Haqqin ALLAH AKAN Bayinsa https://­m.facebook.com/­HaqqinAllahAkanBayins­a

Back to posts
This post has no comments - be the first one!

UNDER MAINTENANCE


Kaima shiga a tattauna da kai
* No boards.

Online: Guests: 3


→Ra'ayin jama'a game damu

 IDAN KANA BUKATAR A TALLATA MAKA HAJAR KA A WANNAN SHAFIN DA SAURAN SHAFUKAN MU KANA IYA TUNTUBAR MU TA WADANNAN HANYOYIN KAMAR HAKA:


Email: bjournalist55@hotmail.com

Phone No: 09035830253

Facebook: Basheer Journalist Sharfadi

Address: Ittihad Computer Centre,  No 92 Daneji Kano


MAI TALLA SHI KE DA RIBA


*Bayanan ka*
Browser din da ka hawo Mozilla

Kasar da kake United States

Adadin Maziyarta 214883

Adadin Wadanda Sukayi Comment 65691

A Wadanda Suka Shiga Tattaunawar Mu 54



→Yi Adding Dina Ta Facebook
→Yi Like Na Dakarun Sunnah Page
→Yi Like Dina Ta Facebook

*Shafuka Masu Alaka Da Mu*

→Basheer Sharfadi wordpress
Basheer Sharfadi Blog Spot
UP

Basheer Journalist Sharfadi (Abu Hafsah)
ISLAMIC DATE
  • phpimg2.php?it&ic=yellow



  • Click to Sms
    Click to Call


    Basheer journalist sharfadi3
    Coollogo com-1281358