Sheik Aminu daurawa ya ziyarci sakatariyar qungiyar izala
A safiyar Laraba 19 Ramadan Shahararren Malamin Sunnah kuma masanin tarihin Musulunci Sheikh Muhammad Aminu Ibrahim Daurawa ya kai ziyara Sakatariyar kungiyar Izala na jihar Gombe dan kara dankon zumunci tsakanin juna.
Shugaban Majalisar Malamai na jihar Gombe Sheikh Abubakar Abdullahi Lamido, ya yabawa Sheikh Daurawa a bisa irin kokarin da yake na karantarwa, sada zumunci da kuma mutunta Malamai da yake na kungiyar Izala tun fara gabatar da Tafsirinsa a garin Gombe sama da shekaru goma sha bakwai.
"Malam a baya in yazo gabatar da Tafsiri garin Gombe, sai ya bimu gida gida yana gaishemu a garin Gombe tare da bamu shawarwari kan ayyuka na addini da muke gabatarwa, babu abin da zamu ce masa sai addu'an fatan alheri" Inji Sheikh Lamido"
A nasa bayanan Sheikh Daurawa yayi dogon bayani akan muhimmancin hadin kan musulmi bisa lemar Fadin Allah da Manzonsa, ya kuma yabawa kungiyar Izala kan kokari da take wurin karantar da mutane data shafe sama da shekaru talatin tanayi akan sanin hakikanin addini kamar yadda aka saukar,
"Tun muna yara Muke ganin Malaman Izala suke karantar da Sunnah, gashi har mun taso mun tarar dasu a wannan aiki duk da gemunsu yayi fari tas a halin yanzu" Inji Sheikh Daurawa"
Cikin tawagar da suka tarbi Shehin Malamin akwai Mataimakin Shugaban Kungiya na jihar Gombe Alhaji Sambo Billiri, Sheikh Abubakar Abdullahi Lamido (Shugaban Majalisar Malamai na jiha), Alhaji Maigari Usman Malala (Shugaban Agaji na Jiha), Alhaji Adamu D.O. Hinna (Sakataren Kungiya na Jiha), Alhaji Ibrahim Aliyu Maizare (Uban Kungiya na jiha), Alhaji Ibrahim Baba Suleiman (Shugaban Social Media na kasa), Tare da Sauran Shugabanni/Malamai/Yan Agaji da sauran wakilai a fadin jihar.
Muna addu'an Allah ya bada ladan ziyara, ya kuma hada kan musulmi akan tafarkin fadin Allah da Manzonsa. Amin.
Created at 2014-07-16 13:10:56
Back to posts
UNDER MAINTENANCE
allah yasaka da alheri
alarakataki gona
Allah Yakaremana Malaman Sunnah Aduk Inda Suke Amen