Hudubar masallacin jumu'a na uthman bin Affan dake gadon kaya kano ta ranar jumu'a 29/8/2014
A Yau Limamin masallacin ne Sheik Ali Yunus ne Ya gabatar da huduba inda ya fara da godiya, yabo, kirari, da jinjina ga Allah Madaukakin Sarki, ya kuma yi salati ga fiyayyeh halitta da sauran sahabbai.
Daga nan Yayi bayani da tsokaci kan abubuwan da suka shafi cututtuka da yaduwarsu a cikin al'umma inda ya kawo misali da cuta ta kusa kusannan (Ebola) ya kuma kawo ayoyi da hadisai na fiyayyen halitta (S.A.W).
Daga nan yayi bayanin cewa Addinin Musulunci addinine da wayewa wanda yake da rigakafi tun jimawa tun kafin a haifi kakannin wanda suke ikiran kariya da riga kafi ya kawo misalai da dama daga ciki akwai.
1. Hani da Manzon Allah (S.A.W) Yayi dangane da yin bawali ko bahaya a inuwa, hanyar da jama'a ke wucewa da kuma ruwa mara tafiya.
2. Umarni da Manzon Allah (S.A.W) yayi akan kare fuska yayin da mutum zai yi atishawa.
3. Cire abin sha da yin numfashi a wajensa da sauransu.
Wadannan kadanne daga cikin hanyoyin kariya daga yaduwar cuta.
Daga Karshe Yayi Addu'ar Allah ya tsare mu daga wannan cuta, ya kuma yayewa wadanda ta shafa ya amintar da mu a duk inda muke.......
Created at 2014-08-29 16:43:53
Back to posts
UNDER MAINTENANCE
Allah yasaka da alkhairi
Allah yabada lada
Ameeeeeen ya Allah
KHAIRAN
Allah ya saka da Alkhayri