*** LAFAZIN SHEIK JA'AFAR {Rahimahullah} ***
IDAN BAKA SHIRYA KA MUTU BA...
.
.
Marigayi Malam Ja'afar a wata Lakcar sa ya na cewa:O
,
"Idan kai kana ganin cewa ba ka shirya ka MUTU ba, kana da inda zakai don kar ka mutu, to don Allah idan ina karatu ko ina huduba kadaina zuwa sahun gaba, don idan an harbeni kar jini ya vata ma shaddarka da kake ado da ita.
Don Allah idan ina karatu kadaina zuwa sahun gaba, idan ina huduba kadaina zuwa sahun gaba, dan idan an harbeni kar jini ya fallatsarmaka ya vata ma shaddarka da kake ado da ita"
.
.
.
Allahu akbar! Haka kuwan akai, cikin ikon Allah asubahin wata juma'a a masallacin sa dake dorayi, wasu Y'an ta'adda la'anannu y'an jahannama suka harbe Malam har lahira. Inda muryarsa ta dinga daukaka tana cewa
.
.
"INNA LILLAHI WA INNA ILAIHIR RAJI'UN LA ILA HA ILLALLAH MUHAMMADUR RASULULLAH"
.
.
Duk jama'a Makota masallaci da wadanda suke nesa da Masallaci suna jinta cikin amsa kuwar Masallacin.
.
.
Allah sarki Malam Katafi amma har a yanzu kana raye,
.
.
Allah ya jikan Malam ya gafarta Musu shi da dan uwansa Malam Albani Zariya.
Da ma sauran Al'ummar Musulmi baki daya
Created at 2014-09-04 12:39:01
Back to posts
UNDER MAINTENANCE
Allah yajikan malam
Allah ya saka da alkairi
Allah yajikansu da rahama yasa aljannace makomarsu, ameen.