KUNGIYAR IZALA TA KANO TAKAIWA SHUGABAN DARIKAR KADIRIYYA NA YAMMACIN AFRIKA ZIYARA
A yammacin jiya lahadi ne 13/11/1435=7/9/2014 kungiyar Izala reshen jihar kano karkashin jagorancin Sheikh Dr. Abdullahi Sale Pakistan da gangamin 'yan majalisar zartarwarsa da Shugabannin kungiyar na kananan hukumomi 44 suka kaiwa gidan Kadiriyya ziyarar girmamawa.
Tawagar wacce ta samu tarbar Shugaban Darikar Kadiriyya na Afrika ta Yamma, "Sheikh Karibullah Dr. Nasiru Kabara" tare da manyan hadimansa.
A lokacin da yake gabatar da jawabinsa, Shugaban Izala na jihar kano, ya bayyana wannan ziyara a matsayin makamanciyar wacce magabatan mu suka yiwa Juna a shekaru sama da ashirin da suka gabata, inda Marigayi Sheikh Dr. Nasiru Kabara yayi tattaki har garin Kaduna ya ziyarci Sheikh Abubakar Mahmud Gumi, daga baya shima yayi ramakonta.
Ya bayyana makasudin wannan ziyara don sabunta 'yan uwantakar dake tsakanin mu ce, da kuma kara samun fahimta da sassauta harshe ga juna, da samun cikekken hadin kai akan koyarwar alkur'ani da Hadisan Manzon SAW bisa fahimtar magabata Sahabbansa da wadanda suka biyo bayan su.
Ya bayyana rashin hadin kan musulmi da irin kalubalen da muke fuskanta a zamantakewar mu na wannan lokaci, zubar da jini da koma bayan kasuwanci da sauran al'amura.
Da yake maida jawabinsa, Shugaban Darikar Kadiriyya Khalifa Sheikh Karibullah, ya bayyana farin cikin sa da wannan kasaitacciyar ziyara. Ya yiwa Allah godiya da ya nuna masa wannan rana data tunatar dashi makamanciyar ta data faru ga magabatansa.
Ya yaba matuka da irin wannan yunkuri da Dr. Abdullahi Saleh Pakistan yake yi na sassauto da damuwa da kuma hadin kan musulmi, yace musulmi ba za suyi kima da kwarjini ba har sai sun dunkule wuri guda.
Sheikh Karibullah ya gabatar da kyautar litattafai ga Jagoran na Izala a matsayin tukwicin yaba wannan ziyara.
Daga cikin wadanda suka rufawa Shugaban na Izala baya har da Shugaban kwamitin Yada labarai na kasa na Kungiyar, kuma kakakin ta a jihar Malam Ali Dan Abba da kuma Shugaban majalisar Dattijan kungiyar Sheikh Abdulwahhab Abdullah.
Allah ya sanya albarka da alkhairi a cikin wannan ziyara mai cike da darussa.
Created at 2014-09-08 09:53:02
Back to posts
UNDER MAINTENANCE
Allah ya hada mana kan malumanmu Allah ya taimaki musulunci
To Allah ya kara hadin kan a kauda kalmar kafurci,
Allah yakawo mana hadinkai mai dawwama har abada domin shine kashin gadon bayanmu mu matasa daliban Ilmi.