TSAYAR DA GEMU !!!(Sheik Basheer Hassan Kurawa)
HUKUNCIN TSAYAR DA GEMU
Tsayar da gemu waji bini ga maza banda mata saboda dalilai kamar haka:
1- fadin MANZAN ALLAH (SAW):kusa bawa mushrikai, ku tsaida gemu, ku datse gashin baki.
2-aske gemu kwaikwayan yahudawa ne da majusawa kamar yadda yazo a hadisai.
3-aske gemu canza halittar Allah ne kamar yadda Allah yake cewa afadin shaidan:(lallai saina umarcesu dasu canza halittar Allah.).
4-aske gemu kamance ceniyace da mata:(Allah ya tsinewa mai kamance ceniya da mata).
YAHALARTA A RAGE GEMUN DAYA WUCE KAMU DAYA ?
Wasu malamai sun tafi akan halaccin aske gemun daya wuce kamu daya saboda hadisin ibn umar :(daya aske sama da kamu daya na gemunsa a hajji.)
Wasu malamai sun tafi akan bai halattaba ko kadan saboda
-=Ibn umar ahajji ya aske sukuma koyaushe suke askewa.
=Allah cewa yayi a aske kai ba gemu ba.
=idan sahabi ya aikata aikinda ya sabawa nassi to baa binsa.
MAGANA MAFI INGANCI
Wajibine barin gemu kuma haramunne askewa saboda hadisai masu yawa dasuka tabbatar da hakan samada hadisai biyar.
Wallahu a alam.
Dan uwanku Bashir Hassan Bashir
Tambaya ko karin bayani +249992933374
IDAN KANA BUKATAR A TALLATA MAKA HAJAR KA A WANNAN SHAFIN DA SAURAN SHAFUKAN MU KANA IYA TUNTUBAR MU TA WADANNAN HANYOYIN KAMAR HAKA:
Email: bjournalist55@hotmail.com
Phone No: 09035830253
Facebook: Basheer Journalist Sharfadi
Address: Ittihad Computer Centre, No 92 Daneji Kano