ILLAR YA'DA JITA-JITA (Sheik Anas Assalafiy Fagge)
Imamu Muslim ya rawaito hadisi daga Abu Huraira Allah ya 'kara masa yarda yace manzon Allah alaihis-salatu was-salam yace :
" ya ishi mutum girman laifi ya ringa zantar da duk abinda yaji ".
Ya 'yan uwa Hakika kowace kalma da muke furtawa ko rubutawa a litattafai ko jaridu ko kafofin sadarwa na zamani ( social media) suna da matukar tasiri a cikin al'umma da hadarin gaske a rayuwar musulmi.
Da yawa mutane suna yin sakaci ( musamman a kafofin sadarwa na zamani) da zarar sun karanta wani labari basa tsayuwa su tabbatar da ingancinshi sai su shiga ya'dawa, ko kumama ya inganta amma ya'da irin wannan labarin yana iya haifar da 'barna mai girma cikin al'umma, ko kuma ya zama tozartawa ko shiga alfarmar wani musulmi, Wanda hakan kuskure ne babba duba da hadisin da muka ambata a sama.
Annabi alaihis-salam yana cewa :
" Hakika mutum yana zance da wata kalmar da be dauketa a bakin komai ba, amma tayi nesa dashi cikin wuta sama da nisan da ke tsakanin sama da 'kasa ".
Da yawan mutane suna yin hakane ba don mummunan nufi ba, se don kawai ace daga gurinsu aka fara samun labarin !!!
Ya 'yan uwa mu kiyaye duk abinda zamu ya'da kona ilimi ko na labarin yau da kullum mu fara tabbatar da ingancinsa, sannan mu duba maslahar da take cikinsa ko kuma wace irin kofa ya'da wannan abun ze bude, ta alheri ce kota sharri Kafin mu ya'da. Domin mu tuna cewa Allah ze mana hisabi akan duk ayyukanmu na zahiri dana ba'dini.
Allah ya bamu ikon gyarawa.
Anas Assalafy Fagge.
17/shawwal/1436 A.H
IDAN KANA BUKATAR A TALLATA MAKA HAJAR KA A WANNAN SHAFIN DA SAURAN SHAFUKAN MU KANA IYA TUNTUBAR MU TA WADANNAN HANYOYIN KAMAR HAKA:
Email: bjournalist55@hotmail.com
Phone No: 09035830253
Facebook: Basheer Journalist Sharfadi
Address: Ittihad Computer Centre, No 92 Daneji Kano
Jaxakallahu khairan