RAHA ( BARKWANCI) A MUSLUNCI. (Anas Assalafiy Fagge)
Hakika Raha ( Barkwanci) 'dabi'a ce me kyau a musulunci, idan ta ku'buta daga cutarwa,izgili, wuce gona da iri da shagaltuwa ga barin ibada.
Imamul-Bukhary ya fitar da ruwaya daga Bakar ibn Abdillah yana cewa : " Sahabban manzon Allah alaihis-salatu was-salam sun kasance jefefeniya da kankana, amma idan aka dawo kan ha'ki'kar yanayi sune mazajen ( gaske) .
( Al-adabul-mufrad, 266) ( As-sahihah, 435) .
Imamu Ahmad, Abu Dawud da ibn Maajah sun fitar da ruwaya daga Nana Aisha Allah ya 'kara mata yarda tace : " ta kasance tareda manzon Allah alaihis-salatu was-salam a halin tafiya, se mukai tseren gudu ni da shi, sena wuce shi, lokacinda nayi 'kiba se mukai tsere se ya wuceni, se yace : anyi 'daya da 'daya ". ( Al-musnad 6/264) ( sunan Abiy Dawud, 2578 )( sunan ibn Maajah, 1979 ).
Imamul-Bukhary da Muslim sun fitar da ruwaya daga Anas dan Malik Allah ya 'kara masa yarda yana cewa : " inada dan-uwa ( Yaro) yanada wani tsuntsu da yake wasa dashi me kama da kanari, se tsuntsun ya mutu, annabi alaihis-salatu was-salam ya shigo gidammu se yaganshi ( yaron) cikin damuwa, se annabi ya tambayi dalili se aka gaya masa tsuntsunsa ne ( nugair) ya mutu se Annabi yace dashi : Yaa Aba Umair meya samu Nugair? Tun daga lokaci idan zeyi masa Raha se yace dashi : Yaa Aba Umair meya samu Nugair " ( Al-adabul-mufrad, ) ( sahih Muslim, 2150 ).
Imamu Al-'dabarany da ibn Hibban sun fitar da ruwaya. Daga Anas dan Malik yace : " wani mutumin 'kauye yana zuwa ya kawowa Annabi kyauta, wata rana Annabi Alaihis-salam ya shigo kasuwa se yaga wannan ba'kauyen, se ya biyo ta bayansa ( ba'kauyen) se ya rufe masa ido, shi kuma yanata 'ko'karin se yaga waye, yana ganin Annabi alaihis-salam ne, se ya manne bayansa da 'kirjin annabi alaihis-salatu was-salam, se Annabi yace waye ze sai bawa? ( yana masa Raha) , sai yace ya manzon Allah ai bawni tsada zanyi ba, se Annabi alaihis-salam yace aiko a gurin Allah Kai me tsada ne " ( mu'jamul-kabeer, 5310) ( sahihu ibn Hibban, 5307 ).
Zamu cigaba da yardar Allah.
Anas Assalafy Fagge.
13/9/1436 A.H.
IDAN KANA BUKATAR A TALLATA MAKA HAJAR KA A WANNAN SHAFIN DA SAURAN SHAFUKAN MU KANA IYA TUNTUBAR MU TA WADANNAN HANYOYIN KAMAR HAKA:
Email: bjournalist55@hotmail.com
Phone No: 09035830253
Facebook: Basheer Journalist Sharfadi
Address: Ittihad Computer Centre, No 92 Daneji Kano
Allah yasaka da alkhairi mal ANAS Assalafiy