KYAUTATAWA MARAYA !!! (Anas Assalafiy Fagge)
Allah yana cewa: "....kuma suna tambayarka danganeda marayu, kace dasu kyautata musu alkhairi ne..." ( suratu-bakara. 220) .
Allah yana cewa : " lallai wadannan da suke cin dukiyoyin marayu da zalunci, ka'dai wuta suke ci a cikkunansu " ( suratul-Nisa'i. 10)
Manzon Allah S.A.W yace : " dani dame daukar nauyin marayansa kona wani a aljannah zamu zama kamar haka, se yai nuni zuwa ga yatsunsa manuniya dana tsakiya " ( sahihul-Bukhari, 5304) ( Sahih Muslim, 7660) (Al-Muwadda' 1700) ( Almusnad 8868)
Manzon Allah S.A.W. Yace : " ku nesanci abubuwa bakwai masu halakarwa, sai sahabbai sukace menene ( wadannan abubuwa guda bakwai) ? Sai Annabi alaihis-salam yace :
1- tarayya da Allah ( shirka) .
2- da Sihiri ( Asiri) .
3- kashe rai wanda Allah ya haramta ba tare da gaskiya ba.
4- da cin Ribaa.
5- da cin dukiyar maraya.
6- da juya baya ( guduwa) ranar ya'ki.
7- da yiwa mata kamammu muminai 'kage ( sharri) .
( sahihul-Bukhari 6857) ( sahihu Muslim 272) ( Sunan Abiy Dawud 2876)
Manzon Allah S.A.W yace : "......Hakika wannan dukiyar kayan morewace da da'di, madalla da aboki musulmi, Wanda ya sameta ( dukiya) da hakkinta, ya bawa maraya da mikini da 'dan tafarki ( matafiyi) , Amma wanda ya sameta bada hakkinta ba, kamar wanda yake ci ne amma baya koshi, kuma zata zama sheda akansa ranar kiyama " ( sahih ibn Hibban, 3227) ( sunan Al-nasa'iy, 3581) .
Annabi S.A.W. Yace : " mafi alkhairin gida a cikin musulmai, shine gidanda akwai maraya kuma ana kyautata masa, mafi sharrin gida a cikin musulmai shine gidanda akwai maraya kuma ana munana masa " ( Sunan ibn Maajah, 3679) .
Anas Assalafy Fagge.
8/9/1436 A.H
25/6/2015.
IDAN KANA BUKATAR A TALLATA MAKA HAJAR KA A WANNAN SHAFIN DA SAURAN SHAFUKAN MU KANA IYA TUNTUBAR MU TA WADANNAN HANYOYIN KAMAR HAKA:
Email: bjournalist55@hotmail.com
Phone No: 09035830253
Facebook: Basheer Journalist Sharfadi
Address: Ittihad Computer Centre, No 92 Daneji Kano