KUSAKUREN MASU AZUMI (Anas Assalafiy Fagge)
Na daga cikin abubuwanda mutane suke kauda kansu daga garesu a wannan wata na Ramadan shine :
1- yadda wasu suke shagaltuwa da siyan kayan abincin gwangwajewa ba don taimakon mabukata ba, se dan tara kala-kalar abinci a gaba yayi shan ruwa, Wanda kuma sun san ba zasu iya cinyewaba don alfahari kawai. Ga kuma mabukata ba aje an basu ba. Hakika yin hakan ya sabawa shari'a ta hanyoyi da yawa. Daga ciki akwai **kasancewar hakan almubazzaranci, Allah ta'ala yana cewa : " kuci kusha, kar kuyi almubazzaranci, domin Allah baya son masu almubazzaranci " ( al-a'araf 31) .
Haka nan manzon Allah alaihis-salatu was-salam yace : " kuci kusha kuyi tufafi kuyi sadaka ba tare da almubazzaranci ko rowa ba " ( sahih sunan al-nasa'iy 2559) . ***** sannan tara abinci kala-kala aci Wancen aci wannan har ciki yayi fam ya sabawa fadin manzon Allah alaihis-salatu was-salam cewa : " dan Adam be taba cika wata jaka mafi sharrin cikinsa ba" ( sahih al-jami' 5674). Wannan haifar da mutum ya kasa tashi yayi ibada. Allah ya kiyashemu.
Anas Assalafy Fagge.
5/9/1436 A.H
IDAN KANA BUKATAR A TALLATA MAKA HAJAR KA A WANNAN SHAFIN DA SAURAN SHAFUKAN MU KANA IYA TUNTUBAR MU TA WADANNAN HANYOYIN KAMAR HAKA:
Email: bjournalist55@hotmail.com
Phone No: 09035830253
Facebook: Basheer Journalist Sharfadi
Address: Ittihad Computer Centre, No 92 Daneji Kano