HADARIN ZAMA DA MACE DAYA!!! (Anas Assalafiy Fagge)
Na san mata da kuma ragwayen maza za su yi min ca akan wannan gaskiyar da zan bayyana, amma dai ko ba komai na fadi hakika, na fadi gaskiya, na amayar da abinda wasu suka kasa. Zama da mace daya yana kawo illoli da dama ga magidanci da su mata kansu da kuma alumma.

GA MAGIDANCI :-

Yana rage masa nishadin aure.

Yana kawo tsufa da wuri.

Yana saka maigida cikin damuwa musamman a kwanakin aladar matarsa ko lokacin rashin lafiyarta, ko idan ta yi tafiya.
Yana saka wa mace ta rika daga masa kai, tayi masa yadda taso saboda ta san ba shi da yadda zai yi.
Yana rage masa samun soyaiya da tarairaya da kulawa da ya cancanta a matsayinsa na maigida.
Yakan hana shi tantance son na gaskiya daga bangaren matarsa ko wanin haka.
GA SU MATA :-
Yana hana wadansu samun mazajen aure.
Yana dora wa matargida aiyukan da suka shige misali kamar, kulawa da maigida, yarangida da ita ma kanta.
Yakan hana mace samun isasshen hutu da kuma lokacin kulawa da kanta.
Yana rage wa mace kuzarin nuna soyaiya ga maigidanta.
Yana saka matargida cikin tsoro da fargaba marasa yankewa.
Yana haifar da rashin amincewarta ga maigidanta da dauwamar da tuhuma ta har abada.
Yana saka mace cikin shirin yaki da dawainiyar dakon makamai marasa ranar yankewa.
Yana saka mata yawan zargi ga dukkan matan da suke da alaka da maigidanta ko ma wace iri ce.
Yana kara mata zafin kishi da rashin nutsuwa marasa ranar yankewa.
GA AL`UMMA
IDAN KANA BUKATAR A TALLATA MAKA HAJAR KA A WANNAN SHAFIN DA SAURAN SHAFUKAN MU KANA IYA TUNTUBAR MU TA WADANNAN HANYOYIN KAMAR HAKA:
Email: bjournalist55@hotmail.com
Phone No: 09035830253
Facebook: Basheer Journalist Sharfadi
Address: Ittihad Computer Centre, No 92 Daneji Kano