HUKUNCIN SALLAR NAFILA KAFIN SALLAR MAGRIBA.!!
Ma'abota ilimi sunyi sabani akan Shin ya hallata ayi Sallar Nafila kafin ayi Sallar Farilla ta Magriba ko bai hallata ba.
Kamar yadda wasu daga Malaman Fiqhu suka tafi akai shine babu wata Sallah ta Nafila da akeyi kafin Sallar Magriba dai sai a bayan ta.
To amman Manyan Malaman Hadithi sunyi sabani akan hakan, Domin an ruwaito Hadithi daga Anas bn Malik (R.A) yana cewa.
عن أنس قال: كنا نصلي على عهدالنبي ركعتين قبل صلاة المغرب فسُئِل: أكان الرسول يصليهما؟ فقال:يرانا نصليهما فلم يأمرنا ولم ينهنا � مسلم ٨٣٦
MA'ANA:
( An 'karbo Daga Anas "RA" yace. Mun kasance Muna yin Sallah raka'ah guda biyu a Zamanin Annabi s.a.w kafin Sallar Magriba, Sai aka tambayi Anas: Shin Manzon Allah s.a.w yakasance yana yi? Sai Anas yace: Yana ganin mu muna yin Sallah sai dai bai umarce mu ba kuma bai hana mu ba.) Muslim 836
Don Haka akan Wannan Hadithi ne Manyan Malaman Hadithi irin su Sheikh Albany suke ganim hallaccin yin Sallar Nafila kafin Sallar Magriba.
===> Saboda fadar Manzon Allah tsira da aminci Su tabbata agare shi yace.
قال ص :" ما من صلاة مفروضة إلا و بين يديها ركعتان “ . � الصحيحة 232
• قال الألباني:الحديث يدل على مشروعية الصلاة بين يدي كل صلاة مكتوبة
MA'ANA:
( Babu Wata Sallar Farilla face akawa Raka'ah guda biyu a tsakanin ta.) Sahih na Albany 232.
• Albany yace ( Hadithin yana yin nuni da Shari'ancin yin Sallar Nafila a tsakanin ko wace Sallar Farilla.)
Fatan Mu ALLAH ta'ala ya karbi ayyukan mu yasa mu cika da imani ya kuma bamu Aljannah firdausi. Ameen
Umar Rabiu Daura.
JIBWIS S MEDIA KADUNA
19 Shawwal 1436
04 August 2015.
IDAN KANA BUKATAR A TALLATA MAKA HAJAR KA A WANNAN SHAFIN DA SAURAN SHAFUKAN MU KANA IYA TUNTUBAR MU TA WADANNAN HANYOYIN KAMAR HAKA:
Email: bjournalist55@hotmail.com
Phone No: 09035830253
Facebook: Basheer Journalist Sharfadi
Address: Ittihad Computer Centre, No 92 Daneji Kano