Lamborghini Huracán LP 610-4 t
Google69490f6862051cb8
google-site-verification: google69490f6862051cb8.htmlgoogle-site-verification: google69490f6862051cb8.htmlgoogle-site-verification: google69490f6862051cb8.htmlBasheer journalist sharfadi14

Basheer journalist sharfadi14.jpg6
Basheer journalist sharfadi 11 1
Maraba Da Zuwa Wannan
Shafi Mai Al-barka 1

☀ Zabi inda kake son shiga ☀
Menunks
→Home
→Akidojin Ahlussunnah
→Addinin musulunci (35)
→40 Hadith (50)
→Fadakarwa (120)
→Neman labarai (20)
→Shi'a Kafirci (50)
→Hadith (55)
→Khudubobi (24)
→Tarihin magabata (60)
→Raddi / Maida martani (99)
→Face book post (30)
→Monthly Archives (60)
→Tambaya da Amsa (20)
→Sahabban Annabi {s.aw} (50)
→Taskar maluman sunnah (25)
→Akidar Y'an Shi'a Dangane da Al'kur'ani
→Fassarar Usulussunnah (20)
→Sheik Ja'afar {Rahimahullah} (65)
→Sheik Abubakar Gumi {Rahimahullah} (30)
→Sheik Dr. Muhammad Sani R/Lemo
→Salafiyyah Network Nigeria (100)
→Adam Sani Abu-Umayrah (99)
→Salaf Ustaz (79)
→Malama Ummi Ahmad Katsina
→Malama Amina Saleh Mande
→Labarai (40)
→Nishadantarwa (10)
→Siyasar Nigeria (9)
→Vidio (33)
→Audio (66)
→Hotuna (120)
→Internet Cheat (90)
→Site Achieve
→Application (10)
→Games (8)
→About me (01)

Wannan shafin mallakarCoollogo com-1281358 3
Ne




SHAFI DON KARUWAR MUSULMI
HUDUBAR YAU JUMU'A 27/NOV/2015 DAGA MASALLACIN JUMU’A NA UTHMAN BN AFFAN DAKE GADON KAYA A KANO AUDIO MP3

Sheik Dr. Abdallah Usman G/Kaya.

•A Yau Jumu'a 15/02/1437 wanda tai dai-dai da 27/11/2015 Sheik Dr. Abdallah Usman G/Kaya ne Ya Jagoranci Huduba gami da Sallar Jumu'a a Masallacin Usman Bn Affan Dake G/kaya a Kano.

•Dr. Abdallah Ya gabatar da Huduba Mai Taken Koyi da Annabi (s.a.w) wadda a Iya cewa Bulaliya ga Ahlussunnah Kar dai ka sake a Baka Labari Danna Kasa Domin sauraro:

http://darulfikr.com/#!/shared/2686

•Ga masu matsalar downloading sai subi wannan link dake kasa:

http://darulfikr.com/mobile/#!/shared/2686

•Ayi sauraro lfy•

Ku cigaba da kasancewa damu a Darulfikr.com domin cigaba da samun karatukan maluman Sunnah.

Darulfikr.com Ta kuce Domin Yada Sunnah.

•Shiga wannan Rubutun na Kasa Kayi Like na wannan shafin Mai Al-barka:

•Like @[1696162707261773:0]

www.facebook.com/abbanhafsah

•Ka Danna Kasa Domin Gayyatar Abokanan
Ka:

https://m.facebook.com/1696162707261773/invite_friends/?cancel_uri=%2Fabbanhafsah&ref=entries

Basheer Journalist Sharfadi (Abu Hafsah).
15/02/1437 Ah. 27/11/2015Ac.
www.darulfikr.com
www.sahabbai.faa.im
www.basheerjournalistsharfadi.xtgem.com

DAGA MASALLACIN JUMA'A NA LAYIN FARUK U/UKU:(jibwis Social Media Kano)

Ayau juma'a na'ibin liman na wannan masallaci Dr Aminu isma'il shi ya jagoranci huduba da sallar juma'a a wannan masallaci inda hudubar malamin tayi magana akan :"TARA DUKIYA TA HANYAR HALAL"

- Bayan godiya ga Allah wanda ya umarci mu da muci da dadan abubuwa da salati ga annabin rahma da malam yayi. . . . .

- Jin tsoron Allah da dangane da cin da dadan abubuwa da neman halal. . . . . . . . .

- Musulunci ya kawo hanyoyi da yawa gurin neman mallakar dukiya. . . . . . . .

- Duk wata dukiya musulunci ya nuna hanyoyin da da za'a mallaketa ta hanyar da ya dace batare da barna ko kashe ta
tahanyar da bata dace ba. . . . . . .

- Musulunci ya kwadaitar da neman dukiya ko kadan ce amma bai yarda a nema ta hanyar da bata dace ba. . . . . .

- Mutum ya zama yana cin halak shi ne sababin amsar addu'a malam ya kawo misalai daga ciki hadda yanayi da muke ciki na rashin tsaro da talauci da firgici amma muna addu'a kamar ba'ayi meye dalili sai mun guji haram ya kawo hadisai. . . . .

- magabata suna kula da cin halak da gudun cin haram ya kawo misali da sayyadina Abubakar da wani ya kawo masa abinci yaci sai daga baya yake gaya masa hanyar daya samu kudin wannan abincin haramtacciya ce sayyadina Abubakar sai da ya fitar da duk abin da yaci ta hanyar amayar da shi. . . . . . .

- Dukiya ta halak ni'ima ce ta hanyar ta mutum zaiyi ibada misali zuwa hajji bada zakka dss. . . .

- Dukiya ta haram bala'I ce zata disashe maka zuciya ga musifar da zaka tarar agaban ubangiji. . . . . .

- Da yawa mutane basa kiyaye hanyar neman dukiyar su misali cin hanci cin riba kwace sata da biro fashi a kasuwanci kuma kamar cinikin kwaya wadda zata gusar da tunanin mutane dss. . . . . . . .

- Ta yaya muna wannan halin zamuyi addu'a kuma a amsa mana?ta yaya ba muji tausayi ba Allah ya ji tausayin mu?. . . . . .

A karshe shehin malamin ya rufe da addu'ar Allah yajikanmu ya tausaya mana yabamu ruwa mai amfani. . . . . . .

Allah ya karawa malam lfy

Abu-unaisa
Chairman Jibwis social
Media Tarauni kano.
31/7/2015.


HUDUBAR JUMU'A DAGA MASALLACIN JUMU'A NA TUDUN MURTALA DAKE KANO AUDIO MP3

(Sheik Barr. Ishaq Adam R/Zaki),
(Huduba ta 2 akan batun DR Ahmad BUK),

*Sources:- Jibwis Social Media Kano

-A yau Jumu'a 25/08/1436 wanda yayi Dai-Dai da 12/06/2015, Sheik Barrister Ishaq Adam Rijiyar Zaki Shine Ya Jagoranci Huduba da Sallar Jumu'a, a Masallacin Jumu'a na Tunawa da Sheik Ja'far Mahmud Adam, Kuma Head Quater Kungiyar #Izala ta Jihar Kano,

-Shehin Malamin Yayi Huduba akan Sunnar Annabi (s.a.w), Bayan da yayi Godiya da Kirari ga Allah Da Kuma Sallati ga Annabin mu (s.a.w), Sannan Yayi cikakken bayani akan Sunnar Annabin Sannan ya Kutsa kai Tsaye Kan Takaddamar dake Tsakanin Mu da Jami'an Tsaron Kano akan DR. Ahmad BUK,

*Waka dai a Bakin mai Ita Tafi dadi Domin Sauraron wannan Huduba Shiga wannan rubutun na Kasa:-

*http://kiwi6.com/file/9jxv1fvy4j

*Ayi Sauraro Lafiya*

Jibwis Social Media Kano,
25/08/1436, 12/06/2015,


HUDUBAR JUMU'A DAGA MASALLACIN JUMU'A NA UTHMAN BIN AFFAN DAKE GADON KAYA KANO AUDIO MP3

-A yau Jumu'a 12/06/2015, Sheik Ali Yunus Shine Ya jagorancin Huduba da Sallar Jumu'a a Masallacin,

-Bayan Godiya ga Allah da Sallati ga Manzon Tsira (s.a.w) Shehin Malamin Yayi Bayani Dan Gane da Falalar Watan Ramdhana wanda yake Gabato mu Da Irin Garabasar dake cikin sa da kuma Darajar da wata yake da shi,,

-Daga nan Ya tabo Magana akan Abinda ya faru a wanna sati na cin Mutuncin Da Jami'an Tsaron Jihar Kano Suka yi ga Sheik DR. Ahmda Bam-Ba wai don yayi Raddi ga Yan Tijjaniyyan da suka zagi Annabin mu,

-Hausawa na cewa WAKA A BAKIN ME ita Tafi Dadi domin Sauraron Cikakkiyar Hudubar a Bakin Shehin Malamin Shiga wannan rubutun na Kasa:-

http://kiwi6.com/file/a12o4rvfu1

*Fatan Za'ayi Sauraro Lafiya*

Jibwis Social Media Kano,
10/06/2015,


HUDUBAR JUMU'A

Daga Masallacin Tudun Murtala head quater IZALA ta Jihar Kano.

Wadda babban limamin masallacin kuma shugaban Izalar Jihar Kano Sheikh Dr. Abdullahi Saleh Pakistan ya gabatar.

A takaice hudubar Malam tayi magana akan abubuwa kamar haka:

Tun farko bayan godiya ga Allah madaukakin sarki da salati ga fiyayyen halitta Annabi Muhammad (SAW), Mallam yaja hankalin mutane da cewa kamar yadda muka dade muna rokon Allah da Ya kawo mana canji kuma Allah Ya karbi rokon mu ya kawo mana canjin to ya zama wajibi mu gode maSa ta hanyar bin umurnin Sa da gujewa abunda Ya hane mu.

Mallam Ya cigaba da cewa addu'ar da muka yi a baya ta zamto kamar damba ne muka daura yanzu ne lokacin da ya dace mu dage da addu'ar wadannan sabbin shugabannin namu da muke yiwa kyakkyawan zaton mutanen kirki Allah Ya arzuta su da mataimaka da mashawarta na kwarai.

Sannan Mallam ya koma a bangaren wadancan zindikan, kafiran wadanda su kayi batanci da cin mutunci ga fiyayyen halitta (SAW) Inda malam yayi kaca-kaca dasu da miyagun akindun su na kafirci.

Daganan Mallam ya jawo hankali gwamnati cewa ya zama wajibi a gaggauta yanke ma wadancan zindikan hukuncin kisa saboda ba iya addinin musulunci bane ya yanke masa wannan hukuncin shima constitution din da suke takama dashi wannan hukuncin ya yanke masa.

Daga karshe Mallam yayi addu'ar wadannan sabbin shugabbanin da aka rantsar a yau Allah Yayi riko da hannun su Ya arzuta su da mashawarta da mataimaka na kwarai, su kuma wadancan masu takalo fushin Allah to Allah Yayi mana maganin su Ya tsare mu da sharrin su.

Jibwis Social Media Kano
29/05/2015.


HUDUBAR JUMU'A DAGA MASALLACIN JUMU'A NA IHYA'US SUNNAH DAKE KOFAR NASARAWA KANO MUNICIPAL

A yau Jumu'a 04/08/1436, wanda yayi dai-dai da 22/05/2015, Babban Limamin Masallacin Sheik DR. Muhammad Sani Ashir Kano shine ya jagoranci Huduba da Sallar Jumu'a a Masallacin,

Bayan yabo da Kirara ga Ubangijin Halittu sannan yayi Salati ga Annabi Muhammad (s.a.w) Shehin malamin yace:-

''Yan uwa Musulmai wajibine akan mu mu tabbata mun Kudurce Hakika Annabi Muhammad (s.a.w) Manzon Allah ne, Kuma Muyi Furuci da shi a Harasunan mu sannan agan shi a aikace,

-Allah ne ya aiko shi Izuwa ga Mutane da Kuma Al'janu gaba daya Kuma Idan mutum ko Al'jan ya mutum beyi Imani da Manzoncin sa ba, To ya Hakika ya mutu a cikin Halaka,

-Abinda ke nuna mana shine:-

-Yi masa biyayya cikin abinda yayi umarni dashi, Ma'ana duk abinda Annabi (s.a.w) yayi umarni muyi kokari da gaske wajen aikatawa,
Kin Aikatawa ko sakaci game da Umarnin sa yana nuna Raunin Imani ne,

-Sanann Abu na Biyu Shine: Gasgata shi cikin Dukkan Abinda ya baada Labari dashi,

-Annabi (s.a.w) ya bada labarin Abinda ya faru a can da kafin mu sannan ya bada Labarin Abinda yake Faruwa yanzu da kuma wanda zai faru a nan gaba,

-Majibi ne mu gasgata dukkan Labarin da yazo mana dashi kada mu zama cikin masu shakku, Indai magana ta tabbata daga Annabi (s.a.w),

-Abu na uku 3: Kauracewa duk wani Abu dayayi hani, Kubar Abu kaza kada kuyi Kaza, Duk Abinda Annabi (s.a.w) ya hana muga mun kaurace masa mun tsorace shi mun nisan ce masa,

-Abu na Hudu4: Kada mu bautawa Allah se da Abinda ya sha'ar an ta (Abinda yace ayi) Saboda Shari'arsa Itace Gamsash-shiya ta Adalci Tsan-tsa,

-Babu Abinda ya rage wanda mutum ze yi ya shiga Aljannah se da Ya Annabi yayiwa Duniya bayani,

-Sannan Babuwani Abu da ya rage wanda ze nisanta mutum da shiga wuta, Sai da Annabi (s.a.w) yayiwa duniya bayanin ta nisance shi,

-Kuma ya tara mutane a Hajjin Bankwana yace:-

''Shin na Isar da Sakon Allah??
Sukace : EH, yace:
''Ya Allah ka Shaida,
''Ya Allah ka Shaida,

Daga nan malam ya dora da kwararo Bayanai da dama Akai, Ya Allah ka yi salati ga Annabin mu Muhammad (s.a.w) ka tarwatsa dukkan makiyan sa,

Basheer Journalist Sharfadi (Abu Hafsah)
04/08/1436, 22/05/2015,


*HUDUBAR JUMU'A DAGA MASALLACIN JUMU'A NA IHYA'US SUNNAH DAKE KOFAR NASARAWA*

A Yau Jumu'a 7/5/2015, Sheik Anas Abbas R/Lemo shine ya jagoranci Huduba da kuma Sallar Jumu'a a masallacin,

Tun da farko Bayan mal. Yayi godiya da yabo ga Allah {s.w.t} sannan yayi salati ga Annabi { saw} kuma yayi mana wasiyya da muji tsoron, Sannan yayi Nasiha ga Shuwagabanni.

Shehin Malamin ya gabatar da Huduba mai taken: [ RAYA MASALLATAN ALLAH ]. Inda Mal. Ya kawo ayoyi daga cikin suratu nur Inda Allah {s.w.a} yake cewa:-

''A cikin wadansu gidaje wadanda Allah yayi umarnin a daukaka, kuma a ambaci sunayensa a cikinsu, sunayin tasbihi a gare shi a cikin safiya da maraice. wadansu maza wadanda wani fatauci baya shagaltar dasu, kuma shayarwa bata shagaltar dasu daga ambatan Allah, suna tsai da salla suna bada zakka, kuma suna tsoron wani yini wanda zukata suna firgita a cikinsa da gannai''

Gina masallaci iri biyu ne. Akwai gina masallaci ta fuskar gini kuma akwai gina masallaci ta fuskar raya shi da karatu.

Manzon Allah {s.a.w} yace:-

'Akwai mutane 7 bakwai ubangiji zai sasu a inuwar sa ranar da babu wata inuwa sai inuwar sa, To daya daga ciki akwai mai raya masallaci''

Manzon Allah {s.a.w} yace:

''Babu wani masallaci wanda ake Kulla kaya ayi tafiya dan bautar ubangiji sai dai masallatai uku :-

1, Masallaci mai alfarma na makka, 2, Masallacin manzon Allah,
3, Masallacin qudus. ''

Inji Shehin Malamin,

A karshe malamin ya Rufe khudubarsa da bayani akan bambamcin lada tsakanin masallatan.

Kamilm Umar Kofar Nasarawa,
07//05/2015,



**HUDUBAR JUMU'A DAGA MASALLACIN JUMU'A NA IHYA'US SUNNAH DAKE KOFAR NASARAWA KANO**

A yau Jumu'a 21/06/1436, Wanda yayi dai-dai da 10/04/2015, Babban Limamin Masallacin Sheik D.R Muhammad Sani Ashir Kano ne ya jagoranci Sallar Jumu'a A masallacin Inda ya gabatar da Huduba akan Ambaton Allah,

Bayan Godiya Ga Allah da Salati ga Manzon Allah (s.a.w) Shehin Malamin Yace:-

'Yana cikin Abinda mutane da dama suka gafala suka barshi, Wasu kuma suka wuce gona da'iri a cikin sa, Shine zikirin Allah (s.w.a).

Zikiri yana daga cikin mafifitan Ayyuka yana daga cikin mafificin Abinda ake yiwa Allah godiya da shi,
Maluma sun ambata cewa shine Abinda Idan mutum yana cikin Kunci Allah yake yaye Kunci Dashi. Yana daga cikin Abinda Idan Mutum yana cikin Talauci Allah yake yaye Talauci dashi, In mutum yana cikin Bacin Rai Ko da muwa Mutum yake Kawar masa, Idan wani Abu ya gagareshi Allah (s.w.a) Ya Isar masa,

Saboda Falalar da wannan Ibada take dashi Ayoyi Da dama Da Kuma Hadisai Ingantattu Da dama sun zo A kan Falalar Ambaton Allah,

Yana daga cikin Ayoyin da. Suka zo akan Falalar Zikirin Allah, Allah (s.w.a) yake cewa:-

'Ya ku Wadanda Ku kayi Imani Ku Ambaci Allah Zikiri Mai yawa. Kuma ku ringa Tashbihi ga Allah safiya da maraicen ku'

Allah ya qara cewa:

'Ku Ambaceni Nima zan Ambace Ku, Ku Godemin Kada Ku Kafirce min'

Shi yasa ka ma da Ibnul Qayyum Ya tashi yin Ta'arifi Na Zikiri sai Yace:-

'Ai abinda ake cewa zikiri ya zama baka gafala ba, baka cikin mutane da suka manta ga Allah,

Ma'ana ko yaushe kana tuna Allah wannan ze zam Allah yana tunawa da kai,
Ko yaushe kana Ambaton sa wannan ze, Allah ya dinga Ambatonka,
Duk Lokacin da kake Razanuwa da Allah bayan ka tuna shi! Lokacin Ubangiji yake matsar da kai ya nisantar da kai ya Tunkude ka daga Kusanci da wutar Jahannama.
Inji Shehin Malamin,

Sannan ya cigaba da Kwararo A yoyi da Tarin Hadisai Da suke magana akan Ambaton Allah Inada yace: 'Idan Allah ya kaimu sati mai zuwa Hudubar sa zata dora ne akan Fa'ida da ake samu da Ambaton Allah,

A karshe Yayi Kira ga Al'umma da su fito Gobe domin Kada Kuri'un su Sannan su Barwa Allah zabi,

Basheer Journalist Sharfadi (Abu Hafsah),
21/06/1436, 10/04/2015,



HUDUBA DAGA MASALLACIN TAHEER HUNGU GYADI-GYADI :
A yau limamin masallacin mal,lawan musa shi ya jagoranci huduba da sallar juma'a

Malamin yayi huduba akan hakuri bisa kaddarar ubangiji.

Malam ya ce wannan rayuwar jarrabawa ce daga allah dan haka allah zai jarrabeka akowanne irin hali.

Ya ce yana daga cikin imani yin hakuri idan allah ya jarrabeka da mutuwa ko asarar dukiya to yin hakuri a wannan lokaci yana daga cikin imani.

Sannan malam ya yi shimfida akan abu huraira darajar sa matsayinsa da falalarsa daga bisa ni malam ya dora akan bayanin da yake yi yakawo ayoyi da hadisai da akan hakuri

Malam yace soyayya ce a gurin allah ya jarrabeka da kowacce musiba.

Daga karshe malam yayi addu'a allah yabamu ikon cin jarrabawar da allah yake yi mana.

DAGA ABU UNAISA.
27/2/2015.



HUDUBA DAGA MASALLACIN SAHABA KUNDILA ZARIA ROAD

Mal. Muhammad bn Usman Ya gabatar.

Yayi Hubane akan: Wani Hadisi na Abdullahi bn Mas'ud, Manzon Allah (SAW) yace ''Ranar Al-kiyama kowane mutum bazaibar filin Al-kiyamaba sai ammasa tambayoyi hudu (4):

1- me kayi a rayuwar ka?
2- wane irin aiki kayi da jikin ka har ka tsufa?
3- ya kayi da ilimin ka?
4- ta wace hanya ka samu kudin ka ta wace hanya ka kashe?.
Wasu suna karawa da, za a tambaye ka dangane da Ahlilbaiti, wannan bai ingantaba a cikin Hadisin.

Sannan yayi tsokaci dangane da wadan su Karin maganan Hausa da ake yi:
1- Allah ya kawomu shekara ta kawomu.
yace ''kace Allah ya kawomu mana kawai, ba sai kace shekara ta kawomuba, wannan ba daidai bane.
2- Taya Allah kiwo yafi Allah nanan. da sauransu



KHUDUBAR JUMA'A DAGA MASALLACIN SA'AD BIN MU'AZ DAKE CIKIN GARIN BEBEJI.

Yau juma'a 8/5/1436=27.2.2015

Khudar ta yau mafi yawancinta ta karkata-ne akan hadisinnan dake magana akan abubuwa guda hudu, wanda Manzon Allah S.A.W. yace duk wanda yake dasu to akwai alamun munafinci tattare dashi, wato:

1.Karya.
2.Saba alkawari.
3.Ha'inci, da kuma
4.Fajirci.

Daga ciki khudubar tasa har ila-yau, Limamin ya bayyana ma'anar munafinci inda yace shi munafinci ya rabu gida biyu, akwai babba, akwai karami kamar yadda ya tabbata a sunnah.

Inda yayi bayaninsu daya bayan daya inada yaja hankali sosai akan babban munafinci wanda shine ke sabbaba kai mutum zuwaga kafirci, sannan kuma yayi bayani akan kjaramin munafinci kuma yaja hankali akansa, domin shima da sannu yana iya kai mutum izuwa babban munafincin.

Allah ya shiryemu ya kara karemu kuma ya tabbatar damu akan tafarkin sunnar Annabi S.A.W.



HUDUBAR JUMU'A DAGA MASALLACIN JUMU'A NA IHYA'US SUNNAH DAKE KOFAR NASSARAWA (Rubutu & Audio MP3)

Yau Jumu'a 07/05/1436 = 27/02/2015 Sheik Anas Abbas Rijiyar Lemo shine ya Jagoranci Sallar Jumu'a a Masallacin.

Shehin Malamin yayi Huduba akan SADA ZUMUNTA Tun da farko Limamin yayiwa Al'umma Nasiha da Muji Tsoron Allah Sannan muyi biyya ga Shuwagabanni Sannan ya cigaba da bayani Inda yayi bayanai masu Fa'ida Baya da kawo Ayoyi Da Hadisai.

'Annabi (s.a.w) yace 'Ba ze shiga Al'jannah ba me yanke zumunci'

'Hakika ma'abota Hankula sune suke Hankalta (su suke tunanin da ze an fane su) wadan da suke cika Al'kawarin Allah ba sa warware shi. wanda kuma suke sadar da Abinda Allah ya yi Umarnin a sadar da shi na zumun ci. Kuma suke tsoron Uban gijin su. Kuma suke tsoron su samu mummunan sakamako ranar Al'kiyama.
Wadannan sune wadanda Allah zai gadar musu Al'jannah da wadanda sukayi kyakykyawan Aiki daga zuri'ar su daga Yayan su da Iyayen su. Mala iku suna shiga ta kowace kofa a garesu suna cewa Aminci agare ku sbd abinda kukayi hakuri akan sa anan duniya.'

A Kwai Hadisi wanda Abu Ayubal Ansari ya rawaito cewa:
'Wani Mutum yazo wajen Manzon Allah (S.a.w) yace: Ka gayamin wani aiki da zan yi In shiga Al'jannah. Da Aikin da zai nesantani Da Shiga Wuta.
Sai Annabi (s.a.w) yace: Hakika An datar da wannan mutumin ya tambayi Abinda yake na Al'khairi.
Sai Annabi (s.a.w) yace dashi:

1.Ka bautawa Allah kada yi Shirka da shi.
2.Ka Tsaida Sallah.
3.Ka bada Zakka.
4.Ka Sada Zumunci.

Da ganan Limamin ya cigaba da kwararo bayanai Sosai Inda a karshe ya ja Hankalin mu kan Biyayya ga Iyaye da Kuma yiwa Kasarmu Addu'a akan Allah ya bamu zaman lafiya.

Hausawa Suka ce Waka a Bakin Me Ita Tafi Dadi Domin Sauraro Ko DownLoading na Hudubar Daga Bakin Shehin malamin Shiga wannan Rubutun Na Kasa.

http://kiwi6.com/file/n2ddx6bvm3

Basheer Journalist Sharfadi
07/05/1436. = 27/02/2015



•••HUDUBAR JUMU'A DAGA MASALLACIN JUMU'A NA IH'YA'US SUNNAH DAKE KOFAR NASSARAWA KANO MUNICIPAL•••

A Yau Jumu'a 23-04-1436 Wanda yayi dai-dai da 13-Feb-2015. Babban Limamin Masallacin Jumu'a na Ihya'ussunnah dake Kofar Nasarawa Sheik D.R Muhammad Sani Asir Kano Shine ya jagoranci Sallar Jumu'a a A Masallacin.

Shehin Malamin yayi Huduba akan:

'MASU IZGILANCI DA ADAWA DA ADDINIn MUSULUNCi'

D.R yayi bayanai sosai game da haka da kuma irin yadda Allah yake murqushe duk wani mai Adawa da Addinin sa.
'INN KAFAINA KAL MUSTAHZI'EEN'
Ma'ana: 'Mun Isar maka daga Masu Izgilanci'

Saboda Haka babu wanda ya isa yayi Nasara Akan Addinin Musulunci domin Allah ze kare Addinin sa Ko da son me so ko da qin me qi dole se gaskiya ta bayyana Kuma Duk wuya duk rintsi duk Adawar wani ko mai Ikon sa matuqar yayi jayayya da Addinin Allah Ba zai kai ga ci ba.
A ta bakin Shehin Malamin.

Sannan ya kawo qissar Irin nasarorin da Allah ya bawa musulunci a yaqin Badr Inda aka kashe Fir'aunan wannan zamani wato Abu Jahl sannan ya kawo qissa ta kisan Ubayyu Bin Kalab Duka dai daga Tafsirin ayar 'Inna Kafainakal Mus'tahzi'een'

Kar shen rahoton kenan se a mako na gaba.

Basheeer Journalist Sharfadi
23/04/1436 - 13/02/2015



HUDUBAR JUMU'A DAGA MASALLACIN JUMU'A NA IHYA'US SUNNAH Kofar Nassarawa kano.

A yau Jumu'a 10/4/1436. Wadda tayi dai-dai da 30/01/2015. Babban Limamin Masallacin Jumu'a na 'IHYA'US SUNNAH' Dake Kofar Nassarawa A Kano. Sheik D.R Muhammad Sani Ashir Kano Shine ya jagoran ci Sallar Jumu'a A Masallacin.

Babban Limamin yayi Huduba akan yadda mutane ke neman Duniya ba tare da tuna lahira ba. Malamin Yayi Bayanai sosai sannan ya ja Hankali Al'umma da su dinga tuna lahira a cikin Ayyukan su domin dai duniya ba matabbaciya bace.

Shehin Malamin Ya kawo ayoyi da dama akan batun Sannan yayi Kira ga Al'umma da muji Tsoron Allah.

Allah ya bami Ikon Amfana da Dabbaqa dukkan Abinda mukaji.

Basheer Journalist Sharfadi
10/4/1436 = 30/1/015.

www.basheerjournalistsharfadi.xtgem.com



HUDUBAR JUMU'A DAGA MASALLACIN AHLUSSUNNAH NA RANO

A Hudubarsa ta YAU jumu'a 25/3/1436 wadda tayi dai-dai da 16/1/2015 Limamin masallacin Ahlussunah na garin Rano wato Sheik Mal. Bukhari Yusif yayi Huduba ne akan yin hakuri wajen bin Allah da manzon sa,

Shehin Malamin yayi Huduba mai faida inda yayi takawo misalai sannan yayi bayanai akan cewa ldan Allah ya kafa dokokinsa to dole ayi hakuri kuma abi dokokin nasa domin wasu abubuwan suna samun mu saboda rashin hakurin mu: daga karshe malam yayi Addu'oin neman zaman lafiya a kasarmu da sauran duniya baki daya

Allah Ya taima kemu,



HUDUBA DAGA MASALLACHIN JIBWIS UNGUWAR GARA BATAIYA ALBASU LG KANO,

A yau 25/3/1436Hjr=16/01/2015 Limamin masallacin Ahlussunnah na Al'basu Malam Musa Muhd Bello shine ya gabatar da hudubar A yau,

Inda malamin yayi mana Huduba akan 'Ya‪da jita-jita ‬da I‪llar da take haifarwa ga Al'umma‬,

Malamin yayi dogon jawabi tare da kawo ayoyi da hadisai, daga cikin ayoyin daya kawo akwai aya ta 83 a cikin suratul nisa'i da suratul fujrat aya ta 6 da sauran ayoyi da hadisai,

Daga karshe yayi addu'a ga Al'ummar musulmi da kasa baki daya,

ALLAH yasa kawa malam da A'lkhairinsa, Ameeeeeen



HUDUBAR JUMU'A DAGA MASALLACHIN MARKAZ IMAMUL BUKHARI DAKE R/ZAKI,

Babban Limamin masallacin wato Dr Muhammad Rabi'u Rijiyar Lemo a yau shine wanda yagabatar da limancin Sallar a Yau,

Malamin yayi Huduba mai matukar ma'ana kuma mai amfani ga Al'ummar musulmi kai har ma wadanda ba musulmaiba in sunji zasu amfana,

Malamin yayi magana ne akan abin da yafaru a yan kwanakin nan dangane da wasu makiya Allah makiya manzon Allah (SAW) kuma makiya Addinin Allah da sukayi kokarin taba mutuncin manzon Allah(SAW) wanda kuma yafi karfinsu,

Malamin yayi magana kan cewa yakamata musani taba manzon Allah(SAW) taba Allah ne,

Allah yace yin gaba da masoyinsa shirin yin yaki dashine to ina ga taba Annabi cikin Annabawa kuma wanda cikin Annabawan duka yafisu.

Wannan ke nuna mana tsananin soyayyar Ahlussunnah ga manzon Allah (SAW).

Allah ka karawa Annabi wasila da fadhila, Allah kai mana maganin makiya Addinin nan naka.



☆★☆ HUDUBA DAGA MASALLACIN JUMA'AH NA GARIN KWANKWASO MADOBI LOCAL GOVERNMENT ☆★☆.

Bayan Malam yayi Sallama irinta Addinin musulunci...

Sannan ya Tsoratar da mu Akan Muji Tsoron Allah Matuqa.

Malam yayi mana magana akan harshe da ni'imarsa ga dan Adam Musulmi ,

Inda malam yace:-

'Da harshe ne kafiri ya ke shiga musulunci sannan dashi ne ake ambaton Allah kuma babu kalmar da mutum zai furta face akwai mala'iku biyu a tare dashi imma ya fadi Alkhairi immah fadi sharri.

Sannan yace muyiwa harsunanmu linzami da furta ayyukan Alfasha kuma musabawa harsunanmu da kyawawan kalamai.



HUDUBAR JUMU'A DAGA MASALLACIN JUMU'A NA IHYA'US SUNNAH DAKE KOFAR NASARAWA KANO
.
A yau Jumu'a 5 gawatan Rabi'ul Auwal shekara ta 1436, wadda tai dai-dai da 26/Dec/2014, Sheik Anas Kofar nasarawa ne ya jagoranci Sallar Jumu'a a masallacin Jumu'a na Ihay'ussunnah dake Unguwar kofar nassarawa a kano,
.
Shehin malamin yayi huduba kan dogaro ga Allah Da mika wuya izuwa gareshi. Tun da farko bayan gabatarwa da yabo da kirari ga Allah s.a.w sai malamin yayi kira ga Al-umma da muji tsoron Allah kana muyi biyayya ga shugabannin mu.
.
'' ‪#Allah‬ya umarce mu da muyi biyayya ga shuwagabannin mu #Allah s.w.a yana cewa : 'Yaku wadanda kukayi Imani Kuyi biyayya ga Allah da manxonsa da ma'abota Al-amari daga cikinku'
.
Sannan mutane mu dinga karanta Al-kur'ani muna halarto da ma'anonisa domin shine muke da tabbacin dacewa da biyayyarsa", Inji Shehin malamin,
.
''Kuma muna masu godiya ga Allah da dogaro Izuwa gareshi kuma muna komawa a gareshi Idan musifa ta samemu se muce
.
'INNA LIL LAHI WA'INNA ILAIHI RAJI'UN' kuma Allah shin maji6incin Al-amuranmu bamu da wani maji6inci Al-amari wanda bayansa, ''Inji Shehin malamin
.
Inda bayan kammala Hudubar malamin ya jagoranci Sallar Jumu'a a masallacin.
.
Allah ya kaimu sati mai zuwa da rai da lafiya.

10891966 1570065556561535 1069268175580535784 n


HUDUBAR JUM'AH DAGA MASALLACIN ABU HURAIRA (RA) A SOKOTO:
.
A yau jum'ah 4 ga R. Awwal Sheikh Ali Yunus daga Kano shine ya jagoranci sallar jum'ah a
wannan masallaci bayan ya yi huduba a kan Muhimmancin rokon Allah samun lafiya.
.
A cikin hudubarsa, limamin ya yawaita yabo da fadanci ga Allah madaukakin Sarki da salati da
gaisuwa ga manzon Allah da iyalansa da almajiransa.
.
Malamin ya yi kira gare mu da mu ji tsoron Allah mu lizimci bin dokarsa mu sani duniya ba
wurin zama ba ce; mutuwa ko yaushe tana iya riskar mu. Sannan ya shiga sharhi a kan hadisin
Ibn Umar (R) wanda ya hikaito wata muhimmiyar addu'a wadda ya ce manzon Allah (S) bai barin ta safe da yamma a kowace rana.
.
Wannan addu'ar ita ce:
.
ALLAHUMMA INNI AS'ALUKAL AFIYATA FID DUNYA WAL AKHIRA. ALLAHUMMA INNI AS'ALUKAL AFWA WAL AFIYATA FI DINI WA DUNYAYA WA AHLI WA MALI.
.
ALLAUMMAS TUR AURATI.. WA AAMIN RAU'AATI..
.
ALLAHUMMAHFAZNI MIN BAINI YADAYYA WAMIN KHALFI.. WA AN YAMINI WA AN SHIMALI WA MIN FAUQI.. WA AUZU BI AZAMITIKA AN UGTALA MIN TAHTI.
.
Malam ya kawo ruwayar da ta nuna Abbas sau tari yana zuwa neman shawarar manzon Allah
(S) akan adduar da ya kamata ya rinka yi sai manzon Allah ya ce masa:
.
"Ka roki Allah samun lafiya"
.
Duniya da lahira ba su yin dadi sai da samun lafiya.
.
Neman lafiya da zaman lafiya na daga cikin adduoin Annabi (S) safe da marece kuma yana yin wannan addua a cikin sujada.
.
Haka kuma Annabi (S) ya karantar da ita ga Sayyidi Alhasan.
.
Abubakar Siddiq (R) ya hau mimbari watarana sai ya fashe da kuka sannan ya ce:
.
'Annabi (S) ya hau wannan mimbari sannan ya fashe da
kuka sannan kuma sai ya ce,
.
"Ku roki Allah ya ba ku lafiya domin babu wata ni'ima da ake bai wa bawa bayan cikakken imani wadda ta kai a ba shi lafiya"
.
Kuma Annabi (S) ya ce :
.
"Babu wata adduar da ta fi mutum ya roki Allah samun lafiya"
.
Neman lafiya a cikin addini shine Allah ya hana ka cin karo da miyagun curutoci na zukata da
na gangar jiki da bin sha'awa da son zuciya da aikin shaidan. Lafiyayyen mutum a cikin addini
shine wanda bai bi shedan ba ya fada a cikin kowane irin bata.
.
Samun lafiya a lahira shine tun daga zuwan mala'ikun mutuwa mutum ya samu ikon furta kalmar shahada. A cikin kabari,
.
samun lafiya shine ka ba da amsar tambayoyin da mala'iku
zasu yi maka. Idan an tashi daga cikin kabari
.
samun lafiya shine ka samu saukin tsayin alkiyama da saukin tsallaka siradi da samun shiga aljanna.
.
A nan duniya samun lafiya shine rashin gamuwa da kowane irin bala'i ko cuta a cikin rayuwarka..
.
cikin dukiyarka.. cikin iyalanka da
yan uwanka.
.
A cikin hadisi, Annabi (S) ya ce:
.
"Duk wanda ya ga wani mutum a cikin wata jarrabawa sai ya ce:
.
"Na gode ma Allah da ya ba ni lafiya bai jarabce ni da irin jarabawar da ya yi ma wannan bawan nasa ba kuma ya fifita ni akan da yawan wadanda aka halitta fifitawa"
. To, Allah ba zai jarabce shi da wannan cutar ba".
.
Tirmidhi ya ruwaito shi ya kyautata shi.
.
Daga karshe limamin ya yi mana addua ga kanmu da kasarmu da sauran al'ummar musulmi.
.
Allah ya karba



KHUDUBA DAGA MASALLACIN JUMA'A NA TRIUMPH DAKE KARAMAR HUKUMAR FAGGE
.
Malaminda ya jagoranci sallar juma'ar a yau shine SHEIKH KHAMIS NASIDI.
.
Khudubar tasa ta maida hankali ne akan wani babban al'amari a addinin musulunci wato TAQAWA.
.
Yajawo ayoyi dayawa acikin littafi mai tsarki wadanda suke bayanin taqawa sannan yayi bayani filla-filla. Haka kuma yajawo hadisai da sukazo akan abinda ya shafi taqawa.
.
Malamin ya bayyana cewa duk abubuwanda suke samun al'umar musulmi a halin yanzi suna faruwa ne saboda karancin taqawa a zuciyoyinsu
.
Malamin ya kara da cewa "babu wani d'a da mace mai daura zani a hannun hagu ta haifa wanda ya isa yabaka tsoro matukar karike taqawa hannu biyu-biyu"
.
Ita dai taqawa itace ake fassarawa a hausa da tsoron Allah madaukaki.
.
A karshe malamin yayi dogayen addu'o'I jama'a suna cewa ameen.
.
Muna rokon Allah madaukaki ya amsa mana ibadarmu da addu'o'inmu. Amen summa amen.



KHUDUBAR JUMA'A DAGA MASALLACIN USMAN BIN AFFAN DAKE KOFAR G/KAYA
.
Sheik Dr. Abdallah Umar Usman G/kaya shine yagabatar da khudubar, wadda yayita akan falalar Annabi SAW, kasancewarsa mai gaskiya, mai hakuri, mai kyauta, mai yadda da duk halinda ya tsinci kansa aciki.
.
Shehin malamin ya fadada bayani akan wadannan abubuwan da aka lissafa abaya.
.
Malamin yace "Annabi SAW ya kasance zababbe acikin zababbu, ya kasance mai gaskiya a lokacin dadi da lokacin wuya, ya kasance mai hakuri yayin fushi da rashinsa".
.
Ya bayyana cewa annabi SAW yana hakuri akan duk yadda yasamu kansa aciki, har yakawo misali da tsawon lokacinda ake dauka ba'a dora tukunya a gidansa ba. Amma duk da haka yake hakura.
.
"Manzon Allah SAW yafi kowa yin kyauta, kyautar ma irin ta wanda baya tsoron talauci, sannan mutum ne mai rikon amana, hatta dukiyoyin kafirai yana tsare musu batare da ko allura tabata ba,
.
hakan yasa har kafirai suke kiransa da AMINU" inji malamin.
Ana fada mana wadannan halaye ne ba don kawai muji suwuce ba bayan kunne ba, saide ana fada ne don muyi koyi da halayen nasa.
.
Allah yabamu ikon koyi da masoyinmu, Annabin Rahama SAW.



*** KHUDUBAR YAU JUMU'A 9/ZUL-HIJJ/ 1435 : 3/10/2014 DAGA @[441850945825133:0] ***
.
Source :- www.basheerjournalistsharfadi.xtgem.com/khudubobi
.
A yau limamon masallaci Ash-sheik D.R Abdallah Usman gadon kaya ne ya jagoranci huduba da kuma sallar jumu'a a massalacin
.
Shehin malamin ya fara da godiya ga Allah da salati ga Annabi (s.a.w)
,
Bayan haka yayi kira ga yan uwa musulmi da cewa:-
.
''wannan rana itace ranar arfa wadda aka sunnar ta mana mu Axumceta
.
Ya kara dacewa wannan rana duk wanda ya A xumceta xa a kankare masa zunubansa na shekara biyu .
.
sannan yace: ' muna yin jaje ga duk wanda ya tashi yau baya axumi. suna nan su abinda suka sani kawai shine gobe sallah
.
Haka kuma yayi kira da muyi gaggawa wajen aikin alkairi
.
Inda yace:o
.
''Bamu jima da gama ramadana ba gashi munxo kwanaki 10 wadanda aiki a cikin alkhairi yafi jihadin dau kaka kalmar Allah a filin daga haka Annabi yace
,
Bayan wannan akwai layya na yanka dabba Allh ya shAr'antamana yanka dabba wanna dabba dai xa'a iya yanka rago bijimin sa duk ya halatta
.
Sannan kuma Shehin malamin ya kara da cewa :
.
''jinin dabbar da aka yanka bashi ke xuwa gun Allah ba Inda yace ''Lan yanalallahu luhumuha wala dima uha walakin yanaluhttakwa minkum''
.
Ya cigaba da cewa Akwai mutanenn dake yaudarar kansa sunada kudi amman ya siyo wani rago ya yanke akwar gida wanda ko kaji ka ajiyewa xasu cinye
.
Eh yaya Annab (s.a.w) xe yanka rakuma 100 amman kai Allah ya yassaremak kana rowa makotan kama basusan me kake ba se matarka kawai!
.
.
Ya cgb da cewa:o
.
' kuma Annabi ya umracemu da yin kabbarori
,
kuma akwai aikin hajji babban aiki kenan wanda yau dinna shine ake babban aiki suna can sun daga hannunsu suna rokon Allah
.
Ya tabbata a hadisi yau dinna Allah yana alfahari da ita kuma Addu'a ance ayita a ranar arfa ba awajen arfa ba kunga kenan har da mu wadanda bamujeba se muyita addu'aa muyi amfani da wannan rana yau ce kawai gobe wallahi ba tamu bace
.
mu duba al farmar da Allah yayi mana ga jumu'a ga arfa kuma acikinta akwai wani lokaci da ake amsa Addu'a kuma itacea xa'a tashi Al-lkiyama
.
Ya kamata mu dage mu amfani da wannan rana mai daraja Al-hazai suna can suna ta addu'a
.
sannan yayi jan hankali ga mutane game da rowar nama
.
A karshe kuma ya yi bayani mai gamsarwa dangane da ranar idi kana daga bisani ya jagoranci sallar jumu'a inda ya karanta farkon suratul fajr a raka'ar farko sannan ya karashe surar a raka'a ta biyu.
.
.
Ya Allah ka bamu ikon Amfana da Abinda muka ji

Sheik Abdallah
DSC 0000009
Uthman bin affan


Koma saman shafi

→Labarai

HASSADA MUGUN CIWO, ANIYARKA TABI KA ABDULJABBAR KA SANI HALIFA QARIBULLAH YAFI KARFINKA,(Imam Aliyu Indabawa)

HASSADA MUGUN CIWO, ANIYARKA TABI KA ABDULJABBAR KA SANI HALIFA QARIBULLAH YAFI KARFINKA,(Imam Aliyu Indabawa)
.
Wannan da kuke gani shine Dr kalifa qaribullah nasiru kabara, wanda ya kasance shine halifan dariqar qadiriyya, kuma muna girmama shi saboda halayensa na kawaici da sanin ya kamata, sai Allah ya jarrabe shi da wani taqadarin kani wanda ya addabe shi da hassada kullum cikin zaginsa yakeyi yana kushe shi yana aibata shi,
.
Asali abinda yasa yake masa wannan hassadar shine saboda halifa qaribullahi Allah yayi masa ni'imomi da baiwarwaki wanda shi kanin nasa bashi dasu, yafi shi duk wani abu da ake so, ta bangaren daukaka, da Ilmi da 'yaya da kudi da magoya baya da manyan mutane Sarakuna, uwa uba kuma yana da hankali wanda shi kanin nasa yayi rashinsa,
.
Sannan ga mukamin Halifa da yake rike dashi wanda shine yafi komai kona masa zuciya da motsa masa hassada, saboda shi a tunaninsa ai shine yafi cancanta daya gaji mahaifinsa ya zama halifan qadiriya saboda tunaninsa wai yafi Qaribu Ilmi shine yasa ya dade yana zagin Halifa karibu yana cutar da shi ta ko'ina yana nuna hassadarsa gare shi, dayake dama hassada ga mai rabo taki ce, shi kuma halifa Qaribu kullum sai kara gaba yakeyi har wasu kashashen ma suna bashi lambar yabo ta girmamawa amman duk da haka har yanzu Abdun jabberun yaki ya gane,
.
Ku duba Ko A haife qaribu ya haifi Audujanbiri amman saboda tantiranci da rashin tarbiya babu irin zagin da bayayi masa akwai Lokacin Audu janbiri yace,"qaribu wai babarsa da cikinsa ta shigo gidan malam wai qaribu ba dan malam bane wai shege ne kuma a duba dashi qaribun dashi Audu janbirin waye yake kama da malam kabara, kuma wai a cikin taron daruruwan mutane yayi wannan maganar, ba wannan kadai ba da dai sauran maganganu masu muni wanda shi kuma qaribun dayake yasan kanin nasa yana da ragaggen hankali baya biye ta tashi kullum hakuri yake dashi, lokacin da magoya bayan qaribu suka ga abin nasa fa ya wuce tunani ya koma tsantsar iskanci da rashin mutunci sai sukace suma dai dai suke da dan iska, inda duk lokacin da yazo wani taro ko maukibi sai suki su barshi ya shiga idan ma ya shigo sai su jefe shaidani, haka suka dinga yiwa dan banza daga karshe dayaga uwar bari da kansa yaje ya bawa halifa Qaribu hakuri akayi salhu tun daga lokacin abu ya danyi shiru,
.
Sai yanzu ya tsiro da wani iskancin, yana zagin Halifa qaribullah, dama tun asali kasancewarsa mutum mai neman Suna kota halin qaqa, amman hakan yaki samuwa yasa yake cin zarafi da cin mutuncin mutane sai kaji shi yana zagin babban malami wanda ya haife ya haife shi,
.
haka ya koma ta6o 'yan siyasa wanda duk gomnatin da take kai to sai yayi ta zaginta kenan har sai an bashi wani abun, misali lokacin mulkin kwankwaso na farko haka ya dinga bi yana zagin kwankwaso har sai da kwankwaso ya bashi fili a gwale filin mushe, wanda yanzu haka a cikin filin yayi gidansa yayi masallacin juma'a filin ma hakkin mutane, lokacin da kwankwaso ya tafi shekarau yazo sai ya koma 6angaren shekarau yana masa jagaliya da yaga shekarau baya bukatar tafiya da 'yan jagaliya irinsu sai ya dinga zagin shekarau har yake cewa idan yabi shekarau to shi dan zina ne, ana nan sai malam shekarau yayi masa wani babban Alkhairi wanda ya fito yace duk duniya ibrahim masu girma guda uku ne, da Annabi ibrahim da ibrahim inyass da ibrahim shekarau, lokacin da kwankwaso ya dawo be tafi dashi ba sai ya koma zagin kwankwaso ko lokacin da kwankwaso ya ta6a Annabi S.A.W sai ya dinga zagin kwankwaso har yace dashi ya zama kafiri, haka ya tara mutanensa har ya dauki sulke da kwalkwali ya saka a jikinsa , ya umarci 'yan jagaliyar yaransa suka rike makamai suka fito gari suna zanga zanga, amman yadda zakasan munafiki ne sai gashi lokacin da yake wa 'yan tijjaniya raddi yana siffanta Muhammadu Rabi'u kwankwaso da mai kishin musulunci,
.
Ba 'yan siyasa kadai ba, tuntuni shine yau ya ta6o 'yan izala gobe kaji ya ta6o 'yan tijjaniyya jibi ya ta6o 'yan qadiriya ko wani malami wanda bashi da dariqa, tun mutane suna biye masa har suka gane manufarsa suka gane cewa yana fama da ta6in hankali ta yaya zasu tsaya suna rigima da mahaukaci sai duk suka kyale karen yaje yayi ta haushinsa shi kadai, daya ga haka sai ya canza dabara akan ya samu masoya wanda zai dinga damfararsu 'yan kudaden su, haka yayi ya dinga tara karatu da sunan kishin Annabi da soyayyarsa nan ko babu abinda yake koyawa sai jahilci da dure duren ashariya, Kunji AMIRUL FASIKINA HUJJATUL JAHILINA kenan,
.
Koda matasan suka fuskanci babu wata tsiya na karatu da ake karuwa da Abdun jabberun sai duk suka dinga watsewa suna karewa kamar hatsin guziri, daya fuskanci neman Sunan dayake har yanzu a kano ba'asan da wani Abdun jabberun ba, wanda ko a gwale filin mushe babu wanda yasan dashi, kuma gashi na cefane yana gagararsa sai ya tsiro da wani iskanci da zindikanci na zagin sahabban Annabi inda yaje ya kar6o kwangilar kudi wajen Iro jakin zariya L.A don ya samu magoya baya, lokacin daya fara zagin sahabbai irinsu sayyadi Mu'awiya A,S yana kawo hadisai ta karfin tuwo yana juya musu ma'ana malaman Sunnah sun zabura suna mayar masa da raddi wanda shi dama abinda yake so kenan ayi ta zancensa yayi suna a san dashi, bayan lokacin da malam Alqasim yayi buji buji dashi akan littafinsa muqaddimatul Khaziba, haka aka dinga fama dashi akan yazo a zauna ayi muqabala akan wannan mas'alar ta fi'atul bagiya, amman hakan yaki yuyuwa kullum ya zauna sai dai dure duren ashariya da tsine tsine da karya da cika baki da alfhari da ihu da kowayee, a haka yanzu zindiqancin nasa da iskancin nasa har yazo ya fara zaginsu sayyadi Abubakar yana karyatashi akan hadisin gadon Annabi, yana zagin sayyadi usman akan wai azzalumi ne a lokacin mulkinsa, yanzu da malaman Sunna suka gane cewar bamagujen dan shi'ar yanada ta6in hankali sai duk suka kyale shi, don idan banda me ta6in hankali babu wanda zai dinga zagin sahabbai yana tuhumarsu,
.
To sai rannan mai tatsinen a wani shirmen sa dayake yi wai da sunan karatu yana karanto wani soki burutsun littafinsa mai suna MUQADDIMATUL KHAZIBAH babi mai taken LA TASABBU AS'HABI sai yazo maganar akan wani Hadisi da Halifa Qaribullah ya rawaito akan Sayyadi Ali inda ya dinga ciwa halifa Qaribullah mutunci yana fada masa maganganu na 6atanci yana cewa zasu 6ata dashi akan imami, ba don komai yake haka ba wai don kawai halifa shi yana girmama sahabban Annabi baya zaginsu sannan yana fadar gaskiya a duk inda ta dace, ko a wani haukan karatun Amirul jahilina na baya naji wai har yana cewa wai qaribu yayi maja da 'yan izala yana kiransa da nasibi,
.
To janbiri idan ma izalar qaribu ya koma ai ya gano itace gaskiya ne, tunda gaskiya yake bi, kuma kowa yayi shaidar cewa qaribu malami ne me koyar da karatu wanda yakanyi tafsiri a gidan sarki, sannan a ranaku yakan karanta sahih muslim da Algunya da ishreniyya, ba kamar ka ba wanda babu abinda ka iya sai dai ka tara mutane kayi ta dura ashariya kana tsine tsine kana sheka karya kana hauka suna ihu kana koya musu ta'addanci kana cewa su dauki makamai suje masallacin da akai rikici a baya su kashe 'yan izala, kai saboda ci da qarfi irin na mai mai tatsine sai kaje ka rubuto hadisai da ayoyi kazo kayi ta karantasu da kyar kana kuskure a cikin ayoyin, mutumin da ko haddar simini daya bashi da ita a Qur'ani, kai ko Ayar Muhammadur rasulillah ma daya karanto akwai kusa kurai a cikinta, kai Abduljbbar wallahi jahili ne na karshe, na tabbata ko fatiha ma idan zai karanta sai an ci gyaransa, ayar suratul ma'ida IN TU AZZIBHUM FA INNAHUM IBADUK WA IN TAGFIR LAHUM FA INNAKA ANTAL AZIZUL HAKIM duk da rubuto ayar yayi amman shi jahilin sai cewa yayi FA INNAKA ANTAL GAFURUR RAHIM haka farkon raddinsa ga 'yan tijjaniya yace" ALLAZINA HUM IZA ASABATHUM sai ya sake cewa" ALLAZINA IZA ASABSATUM.. Kunji chakwakiya fa, haka a wani karatunsa yana karanta tarihin matan Annabi S.A.W wai ayar da take suratul Ahzab tana gargadi ga Matan Annabi itace" INKUNTUNNA TURIDNAL HAYATUD DUNYA WAZINATAHA FATA A LAINA UMATTI U KUNNA WA USARRIH KUNNA amman jahilin wai sai yace." FATA A LAINI UDALLIQUKUNNA WA USARRIH KUNNA, kuji jahili wanda beyi karatun Qur'ani ba, sannan ayar ta suratu Ahbaz yazo kan kissar Zainab da zaid ayar itace WAMA KANA LI MU'UMINUN WALA MU'UMINATUN IZA QADALLAHU WARA SULUHU AMRAN AY YAKUNA LAHUMUL KIYARATU MIN AM RIHIM WAYAY YA'ASILLAH WARA SULAHU FAQAD DALLA DALALAN MUBINA amman kasgin jahilin sai yace" FAQAD DALLA DALALAN BA'IDA kunji jahili wanda beyi karatun qur'ani ba. Idan nace zan dinga kawo kuskuren wannan hanfefen sai na kawo sunfi hamsin, don ko aya daya bazai iya ba ammn ya dinga wa Qur'ani Hawan qawara.
.
To wai wannan kuhungun jahilin kasgi, wai a fadar wasu wawayen shine malami kuma wai hanferen shine jagoransu, kai godiya ta tabbata ga Allah daya saka mabiya wannan zindiqin suka kasance wawaye mahaukata, tabbas kamar yadda suke fada na yarda Amirul jahilina shine mujaddadin wawaye na wannan zamani.
.
Abdun jabbarun sai dai kayi hakuri, na gaba yayi gaba na baya sai labari, halifa qaribullah yayi maka nisan da har abada bazaka ta6a kamo koda farcensa saba, sai dai ka cigaba da haukanka da zagin nasa idan bakayi wasa ba hassada itace zata sheke ka har lahira, kuma ko shi Halifa Qaribun yasan kanada matsalar kwakwalwa, wanda ya kamata yasan yadda za'ayi a kaika dawanau tun kafin haukan naka yakai ka fara zagin annabawa kana tuhumarsu, abduljabbar nidai ina maka Addu'ar Allah ya baka lafiya ya rabaka da wannan cutar ta ta6in hankali da take damunka, su kuma jahilan da suke biye maka. Allah ya ganar dasu su fara zuwa makaranta suy karatu, don babu wani mai ilmi da hankalin da zai dauki wannan galmashoran mai dure duren ashariya da zagin sahabban Annabi wai da sunan malami.
.
Tofah dama ance duk yadda akai da jaki dai yaci kara, yanzu gaskiyar nan dana fada fa sai ka samu wasu jakunan sun fara tunkuyi koh? To jakunan kogo ayi ta tunkuyi lafiya, nidai babu jakin daya isa ya tunkuye ni na juya nace zan rama, ko shi kansa babban jakin naku na kogo be isa balle wasu karnukan farauta, saboda haka 'ya'yan mutu'a. Karnukan farauta haihuwar mutu'a kuy ta haushi lafiya.
.
Har yau dai
.
Angom Fatima ne Abban Sadiq
.
I.A.I

Back to posts
Comments:
[2016-02-24 21:46:57] Moh'd B. Ussaini :

To Maza Kaje Ka Tuba Domin Kayi Karya Gami Da Hahilci Bataimiye

[2016-07-01 22:33:04] ANAS AMEEN :

ALLAH YA SAWAKE AMEEN.

[2016-05-12 19:18:42] ummu aisha :

SLM

[2016-07-24 20:41:23] Aminu Rabiu Garun Gudinya Babura :

Ya Allah kaganar damu gaskiya katseratar da diga diganmu daga saba maka amin

[2016-07-30 18:45:55] MHD SANI :

Allah yasaka wa abduljabbar anyi masa kage kuma baze yafeba

[2016-09-17 05:21:32] ibrahimaliyusumaila@gmail.com :

kai arasa wanda za aiwa sharri sai abduljabbar

[2016-08-28 22:57:17] Shamsuddeen lawal anchau :

Tofa!

[2018-02-07 15:24:04] Zaharaddeen m.abubakar deen :

to allah yaimana jagora amin mudai sunnah sak.


UNDER MAINTENANCE

Share|

Kaima shiga a tattauna da kai
* No boards.

Online: Guests: 1


→Ra'ayin jama'a game damu

 IDAN KANA BUKATAR A TALLATA MAKA HAJAR KA A WANNAN SHAFIN DA SAURAN SHAFUKAN MU KANA IYA TUNTUBAR MU TA WADANNAN HANYOYIN KAMAR HAKA:


Email: bjournalist55@hotmail.com

Phone No: 09035830253

Facebook: Basheer Journalist Sharfadi

Address: Ittihad Computer Centre,  No 92 Daneji Kano


MAI TALLA SHI KE DA RIBA


*Bayanan ka*
Browser din da ka hawo Mozilla

Kasar da kake

Adadin Maziyarta 318808

Adadin Wadanda Sukayi Comment 65691

A Wadanda Suka Shiga Tattaunawar Mu 54


Follow @bjournalist55
→Yi Adding Dina Ta Facebook
→Yi Like Na Dakarun Sunnah Page
→Yi Like Dina Ta Facebook

*Shafuka Masu Alaka Da Mu*

→Basheer Sharfadi wordpress
Basheer Sharfadi Blog Spot
UP
→Home

Basheer Journalist Sharfadi (Abu Hafsah)
ISLAMIC DATE
  • phpimg2.php?it&ic=yellow



  • Click to Sms
    Click to Call


    Basheer journalist sharfadi3
    Coollogo com-1281358