Google69490f6862051cb8
google-site-verification: google69490f6862051cb8.htmlgoogle-site-verification: google69490f6862051cb8.htmlgoogle-site-verification: google69490f6862051cb8.htmlBasheer journalist sharfadi14

Basheer journalist sharfadi14.jpg6
Basheer journalist sharfadi 11 1
Maraba Da Zuwa Wannan
Shafi Mai Al-barka 1

☀ Zabi inda kake son shiga ☀
Menunks
→Home
→Akidojin Ahlussunnah
→Addinin musulunci (35)
→40 Hadith (50)
→Fadakarwa (120)
→Neman labarai (20)
→Shi'a Kafirci (50)
→Hadith (55)
→Khudubobi (24)
→Tarihin magabata (60)
→Raddi / Maida martani (99)
→Face book post (30)
→Monthly Archives (60)
→Tambaya da Amsa (20)
→Sahabban Annabi {s.aw} (50)
→Taskar maluman sunnah (25)
→Akidar Y'an Shi'a Dangane da Al'kur'ani
→Fassarar Usulussunnah (20)
→Sheik Ja'afar {Rahimahullah} (65)
→Sheik Abubakar Gumi {Rahimahullah} (30)
→Sheik Dr. Muhammad Sani R/Lemo
→Salafiyyah Network Nigeria (100)
→Adam Sani Abu-Umayrah (99)
→Salaf Ustaz (79)
→Malama Ummi Ahmad Katsina
→Malama Amina Saleh Mande
→Labarai (40)
→Nishadantarwa (10)
→Siyasar Nigeria (9)
→Vidio (33)
→Audio (66)
→Hotuna (120)
→Internet Cheat (90)
→Site Achieve
→Application (10)
→Games (8)
→About me (01)

Wannan shafin mallakarCoollogo com-1281358 3
Ne




SHAFI DON KARUWAR MUSULMI
Assalamu Alaikim y'an uwa wannan 6angare dukkan rubutun dake ciki ze dinga zuwa muku ne kai tsaye daga dan uwanku
M. Salaf Ustaz
Kuna iya binsa ta shafin face book
Wanda ya tsara ya kuma shirya
Basheer journalist sharfadi (Abu Hafsat)
Asha karatu lafiya

→TA YAYA ZAKI YI WA MIJINKI BIYAYYA


SHIN RAGOWAR 'YA'YAN NASA BA AHLUL- BAITI BANE N0 1?
.
Shubuhuhin shi'a akan hadisin mayafi da warware su a bisa fahimtar malamai na kwarai.
.
Bissimillahir Rahamanir Rahim.
.
Daga cikin shubuhar da yan shi'a masu limamai goma sha biyu (12) suke yadawa akwai hadisin (MAYAFI) wato hadisin da aka karbo daga nana Aisha da umma salama (r.a) cewa, lokacin da Ayar nan dake cikin suratul Ali- imran ta sauko wato fadin ubangiji (swa) " Duk wanda yayi jayayya da kai dangane da abinda akayi maka wahayi bayan dalilai sun bayyanannu sun zo maka, to kace:- ku zo mukirawo 'ya'yan mu da 'ya'yan ku, da matayenmu,da matayenku, damu kanmu da kanku, sannan muyi addu'a ta la'anta akan masu karya " sai manzon Allah ya kirawo s. Ali da nana fatima da hasan da husaini (r.a) ya lulluba da mayafi tare da su, sannan yace "ya ubangiji wadannan iyalan gidana ne ka kawar da datti daga gare su,ka kuma tsarkake su iyakar tsarkakewa".
Yan shi'a masu limamai goma sha biyu (12) sukan kafa hujja da wannan hadisin cewa, s. Ali da nana Fatima da hasan da husaini (r.a) sune kadai ahlul-baiti, kuma ma'asumai ne basa kuskure. Hujjan su nan kamar yanda suke riyawa ita ce. Allah yafi da datti daga barinsu ya kuma tsarkake su.
Don haka sun zama ma'asumai a riyawarsu,
jawabi akan wannan hadisi shine, ta fuskoki kamar haka,
.
INALLAH YA YARDA ZANKAWO JAWABI AKAN WANNAN HADISIN A DARASI NA GABA.


SHIN RAGOWAR "YA YAN NASA BA AHLUL-BAITI BA NE ?(002).
.
SHUBUHOHIN SHI'A AKAN HADISIN MAYAFI DA WARWARESU ABISA FAHIMTAR MALAMAI NA KWARAI.
.
1) Tabbas s. Aliyu, nana Fadima, hassan da husaini r.a, suna daga cikin mafiya kusanci da manzon Allah s.a.w.Amma basu kadai Ahlul-baiti ba a haduwar malaman sunnah da shi'a.
2) hakika wannan hadisi ya inganta inbanda wata ruwaya da imamu tirmizi ya fitar da ummu salama r.a tace " lokacin da manzon Allah s.a.w ya lullube s. Aliyu da fatima da hasan da husaini r.a, yakaranta wannan ayar ta cikin suratul Al-ahzab, sai nima (ummu salama) nace ya ma'aikin Allah nima ina cikin Ahlul-baiti ? Sai manzon Allah s.a.w yace " kedai kina cikin alheri".
malaman hadisi sun tabbatar da cewa " wannan ruwaya bata inganta ba". Saboda acikin isinadinsa hadisin akwai gibi kamar yadda lbn kathir yafada. Ruwayan da ta inganta daga ummu salama itace lokacin da tambayi manzon Allah s.a.w cewa nima shin ina cikin Ahlul-baiti? Sai yace! Tabbas kema kina cikinsu".
3) wannan aya ta cikin suratul Al-imran bacewa tayi manzon Allah s.a.w yakirayi dukkan Ahlul-baiti ba. A'a an umurce shine da yakirawo wadanda suka samu daga danginsa. Sai akace dai dai wannan lokaci s. Aliyu da nana fadima da hasan da husaini r.a sune iyaka wadanda zai kira. Ba wai don sune kadai Ahlul-baiti ba. Dalili kuwa shine sanannen abu ne cewa bayan su akwai wadanda suke da matsayi irin daya dasu ta bangaren nasaba agurin manzon Allah s.a.w ahaduwan malamai. Amma daidai wannan lokacin basa wannan gurin saboda wasu dalilai misali:- akwai ja'afar dan abi dalib da Akilu r.a yan uwan s. Aliyu r.a wanda matsayin su iri daya ne dana s. Aliyu tabangaren nasaba agurin manzon Allah s.aw.
Ita kuwa nana fadima r.a akwai yan uwanta da suke da nasaba iri daya, amma daidai wannan lokacin dukkan ninsu sun rasu ita kadai tai saura. domin yatabbata cewa "ya "yan manzon Allah s.a.w guda bakwai ne 7 maza uku 3 ;- Alkasin, Abdullahi da Ibrahim r.a.
Sai kuma mata hudu 4 ;- watau zainab da Rukayya da Umma kursum da Fadima yar autansu r.a. Hasan da husaini r.a kuwa suna da "yan uwa da suke ciki daya, watau zainab umma kursum wacce s. Ummar r.a ya aura, sai kuma muhsin wanda yarasu yana karami. Sannan kuma manzon Allah s.a.w yana da wasu jikoki ta bangaren "ya "yansa zainab da Rukayya r.a da suka haifa tare da s. Usman r.a da ibn abul as r.a. Kari akan haka, akwai Abbas da Abdulmudalib r.a wanda shi yafi kuwa kusanci da manzon Allah s.a.w bayan "ya"yansa amma alokacin bayanan .
Abin dai damuke so agane manzon Allah s.a.w yakira s. Aliyu da nana Fatima da hasan da husaini r.a ne awannan lokacin, don sun kawai wanda zai iya kira ba wai don sune kadai Ahlul-baiti ba. Idan yan shi'a suka to maiyasa manzon Allah bai kirayi matan sa ba a halin yana damar da zai kiraye su. Sai muce jawabi yagabata ahadisin umma salama cewa lallai matarsa suna daga cikin Ahul-baiti.
Amma bai kiraye su bane saboda basu da alaka da shi ta nasaba da jini, sai ta bangaren auratayya kamar yadda bayani zai zo nan gaba. Kari akan haka acikin ayar ba ce manzon Allah s.a.w yakirayi matarsa na aure ba. Kuma manzon Allah s.a.w ba zai iya lulluba tare da matansa ba acikin wannan bargo a halin akwai wanda ba muharramansu nabe aciki.
.
AKWAI CIGABA A DARASI NAGABA IN ALLAH YA YARDA.


SHIN RAGOWAR "YA"YAN NASA BA AHLUL-BAITI BANE (003) ?
.
SHUBUHOHIN SHI'A AKAN HADISIN MAYAFI DA WARWARE SU A BISA FAHIMTAR MALAMAI NA KWARAI.
.
4) Ga wata tambaya ga "yan shi'a:
menene hukuncin ragowar "ya"yan manzon Allah s.a.w da jikokinsa, shin su ba ahlul-baiti bane? Menene hukuncin ragowar yan uwan s. Aliyu, ja'afar Akilu r.a ? Menene hukuncin Nana khadija r.a suma duk ba ahlul-baiti bane?
Idan yan shi'a suka ce suma ahlul-baiti ne. Sai muce to ai suma basa acikin wadanda manzon Allah s.a.w ya lullube da mayafin, ta yaya suka zama ahlul-baiti ? idan yan shi'a suka ce manzon Allah s.a.w baikiraye su bane saboda galibin su basanan.
.
Sai muce wannan ya zama martani ga "yan shi'a da suke iyakance Hassan da Hussaini da s. Aliyu da nana Fatima r.a amatsayin ahlul-baiti, ya kuma nuna tabbacin abinda muka gabatar cewa manzon Allah s.a.w yakirayi iyaka wadanda ya samu daman yakiraya awannan lokacin, ba wai don sune ahlul-baiti ba. Idan yan shi'a suka dage cewa lallai iyaka wadanda manzon Allah s.a.w ya lullube da wannan mayafin sune kadai ahlul-baiti.
Sai muce meyasa suke kawo sunayen wasu limamai guda tara 9 bayan sa daga cikin wadanda manzon Allah s.a.w ya lullube da wannan mayafin?
.
Idan yan shi'a sukace su ragowar limamai guda tara 9 anbasu hukuncine irin na iyayen su, saboda jikokin Hussaini r.a ne.
Sai muce, aibasu kenan jikokin Hussaini r.a ba, akwai jikokin sa da yawa wadanda yan shi'a mai limamai guda goma sha biyu 12 ba su yarda da su ba, kamar Zaidu dan Aliyu dan Hussaini da Isma'il dan muhammad dan Aliyu dan hussaini Allah yakara yarda agare su.
.
Meyasa yan shi'a basa kawo sunayen su amatsayin limamai? Kari akan haka meyasa yan shi'a suka dauki wasu daga cikin jikokin s. Hussaini r.a sukayi watsida jikokin s. Hassan r.a?
.
Kuma meyasa yan shi'a suka zabi Hassan da Hussaini r.a kadai daga cikin "ya"yan s. Aliyu r.a? Sukayi watsi da ragowar, alhali s. Aliyu yana da "ya"ya sama da talatin 30?
.
IN ALLAH YAYARDA ZAN KAWO CIGABA

AQIDUN SHI'A (018)
WALLAFAR MUHAMMAD BN YUSUF ALKAROFIYYAH ZARIA .

AKIDAR SHI'A IMAMIYYA NA KAFIRTA NANA AISHATU (R.A)

DUk yan shi'a zakaga baya kaunar nana A'isha kai har samu akayi wani dan shi'a yasanyawa magensa suna nana A'isha, kawai don ya wulakanta, kai kiyayya takai matuka don har cewa sukeyi tayi ridda, wa iyazubillah !

Wannan mummunar magana yana cikin littafin su mai suna
ASHIHABU-SAQIB FI BAYANI MA'ANA AN-NASIB na YUSUFU BAHARANY, shafi 236, inda yake cewa

" lallai nana a'isha tayi ridda bayan wafatin manzon Allah s.a.w kamar yadda mafi yawan sahabbai sukayi ridda ".

muna neman tsari daga Allah.
AKIDAR SHI' IMAMIYYA CEWA DA BA DON ALIYU R.A BA DABA A HALICCI MANZON ALLAH S.A.W BA.

Kada kayi mamaki wannan maganar acikin addinin shi'a, domin har akwai masu cema s. Aliyu r.a shi Allah ne, da kuma masu cewa jibrilu yayi kuskure ne ,antorushi wajen Aliyu, amma saboda kamannin su yayi yawa da manzon Allah s.a.w sai ye kuskure yarinka zuwa wajen manzon Allah s.a.w , kaji wani dimuwa na yan shi'a. Ita ko waccan maganar na cewa ba don Aliyu r.a ba da ba'a halicci manzon Allah s.a.w ba, kaduba cikin ANSARUL- FADIMIYYA na muhammad almasa'udy, shafi na 98 a cikin yake cewa ba don Aliyu r.a ba, da ba a halicci manzon Allah s.a.w ba.

AKIDAR SHI'A IMAMIYYA WANDA YASABA MA SAYYADINA ALIYU R.A KO YA BI ALLAH SAI SHIGA WUTA

Wannan magana an ruwaito shi a cikin lattafin su mai suna KASHIFUL YAKEEN FI FALA'ILIL AMIRIL MUMININA shafi na 8 suka ce " lallai Allah zai shigar da wanda yayi ma Aliyu r.a da'a gidan Aljannah ko ya saba ma Allah, kuma lallai Allah zai shigar da wanda ya saba ma Aliyu r.a gidan wuta ko da yabi Allah".

Kai wannnan maganar yayi muni ! Allah ka raba mu da talalabiya amin.





Koma Saman Shafi

→Labarai

HASSADA MUGUN CIWO, ANIYARKA TABI KA ABDULJABBAR KA SANI HALIFA QARIBULLAH YAFI KARFINKA,(Imam Aliyu Indabawa)

HASSADA MUGUN CIWO, ANIYARKA TABI KA ABDULJABBAR KA SANI HALIFA QARIBULLAH YAFI KARFINKA,(Imam Aliyu Indabawa)
.
Wannan da kuke gani shine Dr kalifa qaribullah nasiru kabara, wanda ya kasance shine halifan dariqar qadiriyya, kuma muna girmama shi saboda halayensa na kawaici da sanin ya kamata, sai Allah ya jarrabe shi da wani taqadarin kani wanda ya addabe shi da hassada kullum cikin zaginsa yakeyi yana kushe shi yana aibata shi,
.
Asali abinda yasa yake masa wannan hassadar shine saboda halifa qaribullahi Allah yayi masa ni'imomi da baiwarwaki wanda shi kanin nasa bashi dasu, yafi shi duk wani abu da ake so, ta bangaren daukaka, da Ilmi da 'yaya da kudi da magoya baya da manyan mutane Sarakuna, uwa uba kuma yana da hankali wanda shi kanin nasa yayi rashinsa,
.
Sannan ga mukamin Halifa da yake rike dashi wanda shine yafi komai kona masa zuciya da motsa masa hassada, saboda shi a tunaninsa ai shine yafi cancanta daya gaji mahaifinsa ya zama halifan qadiriya saboda tunaninsa wai yafi Qaribu Ilmi shine yasa ya dade yana zagin Halifa karibu yana cutar da shi ta ko'ina yana nuna hassadarsa gare shi, dayake dama hassada ga mai rabo taki ce, shi kuma halifa Qaribu kullum sai kara gaba yakeyi har wasu kashashen ma suna bashi lambar yabo ta girmamawa amman duk da haka har yanzu Abdun jabberun yaki ya gane,
.
Ku duba Ko A haife qaribu ya haifi Audujanbiri amman saboda tantiranci da rashin tarbiya babu irin zagin da bayayi masa akwai Lokacin Audu janbiri yace,"qaribu wai babarsa da cikinsa ta shigo gidan malam wai qaribu ba dan malam bane wai shege ne kuma a duba dashi qaribun dashi Audu janbirin waye yake kama da malam kabara, kuma wai a cikin taron daruruwan mutane yayi wannan maganar, ba wannan kadai ba da dai sauran maganganu masu muni wanda shi kuma qaribun dayake yasan kanin nasa yana da ragaggen hankali baya biye ta tashi kullum hakuri yake dashi, lokacin da magoya bayan qaribu suka ga abin nasa fa ya wuce tunani ya koma tsantsar iskanci da rashin mutunci sai sukace suma dai dai suke da dan iska, inda duk lokacin da yazo wani taro ko maukibi sai suki su barshi ya shiga idan ma ya shigo sai su jefe shaidani, haka suka dinga yiwa dan banza daga karshe dayaga uwar bari da kansa yaje ya bawa halifa Qaribu hakuri akayi salhu tun daga lokacin abu ya danyi shiru,
.
Sai yanzu ya tsiro da wani iskancin, yana zagin Halifa qaribullah, dama tun asali kasancewarsa mutum mai neman Suna kota halin qaqa, amman hakan yaki samuwa yasa yake cin zarafi da cin mutuncin mutane sai kaji shi yana zagin babban malami wanda ya haife ya haife shi,
.
haka ya koma ta6o 'yan siyasa wanda duk gomnatin da take kai to sai yayi ta zaginta kenan har sai an bashi wani abun, misali lokacin mulkin kwankwaso na farko haka ya dinga bi yana zagin kwankwaso har sai da kwankwaso ya bashi fili a gwale filin mushe, wanda yanzu haka a cikin filin yayi gidansa yayi masallacin juma'a filin ma hakkin mutane, lokacin da kwankwaso ya tafi shekarau yazo sai ya koma 6angaren shekarau yana masa jagaliya da yaga shekarau baya bukatar tafiya da 'yan jagaliya irinsu sai ya dinga zagin shekarau har yake cewa idan yabi shekarau to shi dan zina ne, ana nan sai malam shekarau yayi masa wani babban Alkhairi wanda ya fito yace duk duniya ibrahim masu girma guda uku ne, da Annabi ibrahim da ibrahim inyass da ibrahim shekarau, lokacin da kwankwaso ya dawo be tafi dashi ba sai ya koma zagin kwankwaso ko lokacin da kwankwaso ya ta6a Annabi S.A.W sai ya dinga zagin kwankwaso har yace dashi ya zama kafiri, haka ya tara mutanensa har ya dauki sulke da kwalkwali ya saka a jikinsa , ya umarci 'yan jagaliyar yaransa suka rike makamai suka fito gari suna zanga zanga, amman yadda zakasan munafiki ne sai gashi lokacin da yake wa 'yan tijjaniya raddi yana siffanta Muhammadu Rabi'u kwankwaso da mai kishin musulunci,
.
Ba 'yan siyasa kadai ba, tuntuni shine yau ya ta6o 'yan izala gobe kaji ya ta6o 'yan tijjaniyya jibi ya ta6o 'yan qadiriya ko wani malami wanda bashi da dariqa, tun mutane suna biye masa har suka gane manufarsa suka gane cewa yana fama da ta6in hankali ta yaya zasu tsaya suna rigima da mahaukaci sai duk suka kyale karen yaje yayi ta haushinsa shi kadai, daya ga haka sai ya canza dabara akan ya samu masoya wanda zai dinga damfararsu 'yan kudaden su, haka yayi ya dinga tara karatu da sunan kishin Annabi da soyayyarsa nan ko babu abinda yake koyawa sai jahilci da dure duren ashariya, Kunji AMIRUL FASIKINA HUJJATUL JAHILINA kenan,
.
Koda matasan suka fuskanci babu wata tsiya na karatu da ake karuwa da Abdun jabberun sai duk suka dinga watsewa suna karewa kamar hatsin guziri, daya fuskanci neman Sunan dayake har yanzu a kano ba'asan da wani Abdun jabberun ba, wanda ko a gwale filin mushe babu wanda yasan dashi, kuma gashi na cefane yana gagararsa sai ya tsiro da wani iskanci da zindikanci na zagin sahabban Annabi inda yaje ya kar6o kwangilar kudi wajen Iro jakin zariya L.A don ya samu magoya baya, lokacin daya fara zagin sahabbai irinsu sayyadi Mu'awiya A,S yana kawo hadisai ta karfin tuwo yana juya musu ma'ana malaman Sunnah sun zabura suna mayar masa da raddi wanda shi dama abinda yake so kenan ayi ta zancensa yayi suna a san dashi, bayan lokacin da malam Alqasim yayi buji buji dashi akan littafinsa muqaddimatul Khaziba, haka aka dinga fama dashi akan yazo a zauna ayi muqabala akan wannan mas'alar ta fi'atul bagiya, amman hakan yaki yuyuwa kullum ya zauna sai dai dure duren ashariya da tsine tsine da karya da cika baki da alfhari da ihu da kowayee, a haka yanzu zindiqancin nasa da iskancin nasa har yazo ya fara zaginsu sayyadi Abubakar yana karyatashi akan hadisin gadon Annabi, yana zagin sayyadi usman akan wai azzalumi ne a lokacin mulkinsa, yanzu da malaman Sunna suka gane cewar bamagujen dan shi'ar yanada ta6in hankali sai duk suka kyale shi, don idan banda me ta6in hankali babu wanda zai dinga zagin sahabbai yana tuhumarsu,
.
To sai rannan mai tatsinen a wani shirmen sa dayake yi wai da sunan karatu yana karanto wani soki burutsun littafinsa mai suna MUQADDIMATUL KHAZIBAH babi mai taken LA TASABBU AS'HABI sai yazo maganar akan wani Hadisi da Halifa Qaribullah ya rawaito akan Sayyadi Ali inda ya dinga ciwa halifa Qaribullah mutunci yana fada masa maganganu na 6atanci yana cewa zasu 6ata dashi akan imami, ba don komai yake haka ba wai don kawai halifa shi yana girmama sahabban Annabi baya zaginsu sannan yana fadar gaskiya a duk inda ta dace, ko a wani haukan karatun Amirul jahilina na baya naji wai har yana cewa wai qaribu yayi maja da 'yan izala yana kiransa da nasibi,
.
To janbiri idan ma izalar qaribu ya koma ai ya gano itace gaskiya ne, tunda gaskiya yake bi, kuma kowa yayi shaidar cewa qaribu malami ne me koyar da karatu wanda yakanyi tafsiri a gidan sarki, sannan a ranaku yakan karanta sahih muslim da Algunya da ishreniyya, ba kamar ka ba wanda babu abinda ka iya sai dai ka tara mutane kayi ta dura ashariya kana tsine tsine kana sheka karya kana hauka suna ihu kana koya musu ta'addanci kana cewa su dauki makamai suje masallacin da akai rikici a baya su kashe 'yan izala, kai saboda ci da qarfi irin na mai mai tatsine sai kaje ka rubuto hadisai da ayoyi kazo kayi ta karantasu da kyar kana kuskure a cikin ayoyin, mutumin da ko haddar simini daya bashi da ita a Qur'ani, kai ko Ayar Muhammadur rasulillah ma daya karanto akwai kusa kurai a cikinta, kai Abduljbbar wallahi jahili ne na karshe, na tabbata ko fatiha ma idan zai karanta sai an ci gyaransa, ayar suratul ma'ida IN TU AZZIBHUM FA INNAHUM IBADUK WA IN TAGFIR LAHUM FA INNAKA ANTAL AZIZUL HAKIM duk da rubuto ayar yayi amman shi jahilin sai cewa yayi FA INNAKA ANTAL GAFURUR RAHIM haka farkon raddinsa ga 'yan tijjaniya yace" ALLAZINA HUM IZA ASABATHUM sai ya sake cewa" ALLAZINA IZA ASABSATUM.. Kunji chakwakiya fa, haka a wani karatunsa yana karanta tarihin matan Annabi S.A.W wai ayar da take suratul Ahzab tana gargadi ga Matan Annabi itace" INKUNTUNNA TURIDNAL HAYATUD DUNYA WAZINATAHA FATA A LAINA UMATTI U KUNNA WA USARRIH KUNNA amman jahilin wai sai yace." FATA A LAINI UDALLIQUKUNNA WA USARRIH KUNNA, kuji jahili wanda beyi karatun Qur'ani ba, sannan ayar ta suratu Ahbaz yazo kan kissar Zainab da zaid ayar itace WAMA KANA LI MU'UMINUN WALA MU'UMINATUN IZA QADALLAHU WARA SULUHU AMRAN AY YAKUNA LAHUMUL KIYARATU MIN AM RIHIM WAYAY YA'ASILLAH WARA SULAHU FAQAD DALLA DALALAN MUBINA amman kasgin jahilin sai yace" FAQAD DALLA DALALAN BA'IDA kunji jahili wanda beyi karatun qur'ani ba. Idan nace zan dinga kawo kuskuren wannan hanfefen sai na kawo sunfi hamsin, don ko aya daya bazai iya ba ammn ya dinga wa Qur'ani Hawan qawara.
.
To wai wannan kuhungun jahilin kasgi, wai a fadar wasu wawayen shine malami kuma wai hanferen shine jagoransu, kai godiya ta tabbata ga Allah daya saka mabiya wannan zindiqin suka kasance wawaye mahaukata, tabbas kamar yadda suke fada na yarda Amirul jahilina shine mujaddadin wawaye na wannan zamani.
.
Abdun jabbarun sai dai kayi hakuri, na gaba yayi gaba na baya sai labari, halifa qaribullah yayi maka nisan da har abada bazaka ta6a kamo koda farcensa saba, sai dai ka cigaba da haukanka da zagin nasa idan bakayi wasa ba hassada itace zata sheke ka har lahira, kuma ko shi Halifa Qaribun yasan kanada matsalar kwakwalwa, wanda ya kamata yasan yadda za'ayi a kaika dawanau tun kafin haukan naka yakai ka fara zagin annabawa kana tuhumarsu, abduljabbar nidai ina maka Addu'ar Allah ya baka lafiya ya rabaka da wannan cutar ta ta6in hankali da take damunka, su kuma jahilan da suke biye maka. Allah ya ganar dasu su fara zuwa makaranta suy karatu, don babu wani mai ilmi da hankalin da zai dauki wannan galmashoran mai dure duren ashariya da zagin sahabban Annabi wai da sunan malami.
.
Tofah dama ance duk yadda akai da jaki dai yaci kara, yanzu gaskiyar nan dana fada fa sai ka samu wasu jakunan sun fara tunkuyi koh? To jakunan kogo ayi ta tunkuyi lafiya, nidai babu jakin daya isa ya tunkuye ni na juya nace zan rama, ko shi kansa babban jakin naku na kogo be isa balle wasu karnukan farauta, saboda haka 'ya'yan mutu'a. Karnukan farauta haihuwar mutu'a kuy ta haushi lafiya.
.
Har yau dai
.
Angom Fatima ne Abban Sadiq
.
I.A.I

Back to posts
Comments:
[2016-02-24 21:46:57] Moh'd B. Ussaini :

To Maza Kaje Ka Tuba Domin Kayi Karya Gami Da Hahilci Bataimiye

[2016-07-01 22:33:04] ANAS AMEEN :

ALLAH YA SAWAKE AMEEN.

[2016-05-12 19:18:42] ummu aisha :

SLM

[2016-07-24 20:41:23] Aminu Rabiu Garun Gudinya Babura :

Ya Allah kaganar damu gaskiya katseratar da diga diganmu daga saba maka amin

[2016-07-30 18:45:55] MHD SANI :

Allah yasaka wa abduljabbar anyi masa kage kuma baze yafeba

[2016-09-17 05:21:32] ibrahimaliyusumaila@gmail.com :

kai arasa wanda za aiwa sharri sai abduljabbar

[2016-08-28 22:57:17] Shamsuddeen lawal anchau :

Tofa!

[2018-02-07 15:24:04] Zaharaddeen m.abubakar deen :

to allah yaimana jagora amin mudai sunnah sak.


UNDER MAINTENANCE

Share|

Kaima shiga a tattauna da kai
* No boards.

Online: Guests: 3


→Ra'ayin jama'a game damu

 IDAN KANA BUKATAR A TALLATA MAKA HAJAR KA A WANNAN SHAFIN DA SAURAN SHAFUKAN MU KANA IYA TUNTUBAR MU TA WADANNAN HANYOYIN KAMAR HAKA:


Email: bjournalist55@hotmail.com

Phone No: 09035830253

Facebook: Basheer Journalist Sharfadi

Address: Ittihad Computer Centre,  No 92 Daneji Kano


MAI TALLA SHI KE DA RIBA


*Bayanan ka*
Browser din da ka hawo Mozilla

Kasar da kake

Adadin Maziyarta 429317

Adadin Wadanda Sukayi Comment 65691

A Wadanda Suka Shiga Tattaunawar Mu 54


Follow @bjournalist55
→Yi Adding Dina Ta Facebook
→Yi Like Na Dakarun Sunnah Page
→Yi Like Dina Ta Facebook

*Shafuka Masu Alaka Da Mu*

→Basheer Sharfadi wordpress
Basheer Sharfadi Blog Spot
UP
→Home

Basheer Journalist Sharfadi (Abu Hafsah)
ISLAMIC DATE
  • phpimg2.php?it&ic=yellow



  • Click to Sms
    Click to Call


    Basheer journalist sharfadi3
    Coollogo com-1281358

    Duck hunt