Teya Salat
Google69490f6862051cb8
google-site-verification: google69490f6862051cb8.htmlgoogle-site-verification: google69490f6862051cb8.htmlgoogle-site-verification: google69490f6862051cb8.htmlBasheer journalist sharfadi14

Basheer journalist sharfadi14.jpg6
Basheer journalist sharfadi 11 1
Maraba Da Zuwa Wannan
Shafi Mai Al-barka 1

☀ Zabi inda kake son shiga ☀
Menunks
→Home
→Akidojin Ahlussunnah
→Addinin musulunci (35)
→40 Hadith (50)
→Fadakarwa (120)
→Neman labarai (20)
→Shi'a Kafirci (50)
→Hadith (55)
→Khudubobi (24)
→Tarihin magabata (60)
→Raddi / Maida martani (99)
→Face book post (30)
→Monthly Archives (60)
→Tambaya da Amsa (20)
→Sahabban Annabi {s.aw} (50)
→Taskar maluman sunnah (25)
→Akidar Y'an Shi'a Dangane da Al'kur'ani
→Fassarar Usulussunnah (20)
→Sheik Ja'afar {Rahimahullah} (65)
→Sheik Abubakar Gumi {Rahimahullah} (30)
→Sheik Dr. Muhammad Sani R/Lemo
→Salafiyyah Network Nigeria (100)
→Adam Sani Abu-Umayrah (99)
→Salaf Ustaz (79)
→Malama Ummi Ahmad Katsina
→Malama Amina Saleh Mande
→Labarai (40)
→Nishadantarwa (10)
→Siyasar Nigeria (9)
→Vidio (33)
→Audio (66)
→Hotuna (120)
→Internet Cheat (90)
→Site Achieve
→Application (10)
→Games (8)
→About me (01)

Wannan shafin mallakarCoollogo com-1281358 3
Ne




SHAFI DON KARUWAR MUSULMI
Assalamu Alaikum warahmatullah barkanku da zuwa wannan 6angare mai Al-barka wanda yake zuwa muku kai tsaye daga mimbarin
SALAFIYYAH NETWORK NIGERIA
Karkashin jagoran cin dan uwanku
Engr Abu Ameena bn khamis.
Inda zamu kawo muku shirye-shirye da suke gabatarwa a shafin face book
Wanda ya tsara kuma ya shirya
Basheer journalist sharfadi (Abu Hafsat)
------------------------
Kuyi can kasa domin bincike ko ku shiga folders din kasa domin download na karatukan
ASH-SHAIKHUL MUFASSIR, AL-MUJTAHID, ABU- SALIM, JA'AFAR MAHMUD ADAM KANO (RAHIMAHULLAH)
Dana
ASH-SHAIKHUL MUHADDITH, AL-ALLAMATUS SALAFIY, ABU ABDIRRAHMAN, MUHAMMAD AUWAL ADAM ALBANIY ZARIA (RAHIMAHULLAH)
10479728 700913979994039 6000318538069586816 n
10252134 697037893714981 2288116539476670114 n
Jaafar kjrAlbani ustralllia 1


→Sheik ja'afar (Rahimahullah) Audio


→Sheik Al-bani zaria (Rahimahullah) Audio







DAGA MIMBARIN SALAFIYYAH NETWORK NIGERIA
WASU DAGA CIKIN MAGANGANUN ASH-SHEIKH ALBANI ZARIA A LOKACIN RAYUWARSHI (PART 16)
.
Na sha gaya muku. Haka kawai 'yan siyasa suka hada kai da jami'an tsaron Nigeria a 'karkashin jagorancin Hafiz Ringim suka kama ni. Su sun san cewa 'karyane banyi laifin da suke tuhumata ba kuma kowa ya san cewa 'karya suke yi ni ba 'dan boko haram bane. Wallahi sun san cewa ni 'dan boko ne kuma daga cikin wayanda suka sa aka kamani har shi Hafiz Ringim 'din kakaf babu wanda yayi karatun boko zalla kamar yadda nayi. Amma ganin cewa ina harkar addini sai suka yi tunanin cewa ni bagidaje ne.
.
Tunaninsu shine; in sun kamani to almajirai na zasu fito shi kenan daganan sai su mayar da zariya ta zama maiduguri.
.
Kurkukun Kaduna kewaye ta suka yi da makamai da tankokin yaki. Garin nan na Zaria kuwa cika shi suka yi da makamai.
.
Da muka tashi mu kuma sai muka yi amfani da manhajin ahlussunnah wal jama'a. Abun da muka yi sai muka maka su a kotu sannan kuma muka dinga rubuce-rubuce a jaridu da other medias.
.
Ba'a dade ba kotu ta wanke ni, tace kuma sai sun biyani diyyar naira miliyan 'daya.
.
Yanzu me kuke tunani inda ace mun biye musu mun 'dauki makami? Me yiwa da har yanzu ana nan ana fafatawa a 'kasar zazzau.
.
Da yanzu an zubar da jinin da baza mu iya kare kanmu ba aranar lahira. Amman kunga babu rikice kuma Allah ya 'dora mu akansu.
.
Allah Muke roko da ya karemu daga sharrin mai sharri.
.
SOURCE: TAFSEER NO 91, 2013

Albani 16


DAGA MIMBARIN SALAFIYYAH NETWORK NIGERIA
WASU DAGA CIKIN MAGANGANUN ASH-SHEIKH ALBANI ZARIA A LOKACIN RAYUWARSHI (PART 15)
.
Sai ga sarkin zazzau yana barazana wai zai yi amfani da jami'an tsaro akanmu dangane da sallar jumma'a kafin rana ta yi zawali. Sarkin zazzau is not a custodian to any religion.
.
Sarkin zazzau yana ina aka fitar da filin coci anan anguwar bai iya securing ba? Namadi Sambo yana gomna aka fitar da wannan filin cocin bai iya kubutar da filin daga hannun kiristoci ba? Partrick Yakowa yazo yana mulki a cikin kwana hudu ya 'dauka yaba kiristoci filin kan cewa su gina cocin.
.
"Nii" 'din "Albaniy" ni na amshi takardan filin cocin a hannun kiristocin na saya ainihin filin cocin na mallaka makarantar Darul-Hadeethis-Salafiyyah. Ga filin nan kowa yana gani na kewaye shi na yi mishi fence.
.
Toh! Masarautat da bata iya hana ayi coci a 'karkashin mulkinta ba itace zata iya hana Sallah?
.
Toh Amma tsogalace domin idan akace yau "muu" su "Albaniy" mun 'dauki makami muna fada da gomnati, toh daga cikin wayanda zasu ci moriyar fadan to sune Sarakunan gargajiya domin za'a rinka gutsura musu kudin Security vote da gomnati zata rinka warewa kan rikicin.
.
Don haka matasa kada ku sake ku 'dauki makami akan kowa ballanta na gomnati. Duk aka yi muku ba daidaiba toh kuzo mun san hanyoyin daza mubi mu 'kwato muku hakinku insha'Allahu ta'ala.
.
(SOURCE: 2013 RAMADAN TAFSEER NO 91)

Al bani part


DAGA MIMBARIN SALAFIYYAH NETWORK NIGERIA
KUNDIN TARIHIN KWAMANDOJIN SALAFIYYAH KASHI NA 'DAYA (PART 1)
.
Wannan Shine Ash-Sheikh Abu Abdullahi, Muhammad 'dan Saalih 'dan Muhammadu 'dann Uthaymeen at-Tamimi.
.
Al-Uthaymeen kamar yadda aka sani mutumin 'kasar Saudiyyah ne wanda ya fito daga cikin 'kabilar Banu Tamim.
.
An haife shi ne a ranar ashirin ga watan Ramadan hijiriyya ta dubu 'daya da 'dari uku da arba'in da bakwai (1347) a garin Unayzah.
Yayi karatun shi a hannun manya manyan malaman duniya irin su Ash-Sheikh 'Abd ar-Rahman ibn Naasir as-Saa'di, Muhammad Amin ash-Shanqeeti da kuma Ash-Sheikh AbdulAzeez Bin Baz.
Uthaymeen ya kwashe sama da shekaru talatin da biyar yana karantarwa a masallacin Harami dake garin Makka. Kafin rasuwarshi, Malami ne a tsangayar Shari'a dake jami'ar musulunci na Imam Muhammad ibn Saud. Har ila yau memba ne na majalisar malamai na duniya, sannan kuma Shine babban limamin Masallacin Unayza.
.
Kadan daga cikin ayyukan da yayi ma duniyar musulunci sun kasance kamar haka;
.
Rubuta littafin Sifatu Salatin Nabiy, Sharh al-Aqeedat Al-Hamawiyyah, Sharh Usool al-Iman, Sharh Usool al-Thalaathah, Sharh Hadeeth Jibra'eel.
.
Allahu Akbar Kabiran! Komai yayi farko zai yi 'karshi. Ash-Sheikh Uthaymeen ya rasu a ranar laraba sha-biyar ga watan Shawwal, hijira na da shekara dubu 'daya da 'dari hudu da ashirin da 'daya (1421 AH). Ya bar duniya yana da shekara saba'in da biyar, sannan anyi jana'izar shi a garin Makka Saudi Arabia.
.
Duniyar musuluncin Nigeria baza ta taba mantawa da Ash-Sheikh Uthaimin ba domin ya karantar da manya-manyan malaman Sunnan 'kasarnan irin su Ash-Sheikh Abdulwahhab Abdallah Kano da kuma Ash-Sheikh Muhammad Auwal Adam Albaniy zaria (Rahimahullah) a 'karkashin tsarin koyon karatun irin na zaure.
.
Allah (SWT) muke roko da ya jikan Ash-Sheikh Uthaimin. Allah (SWT) muke roko da ya kai haske 'kabarinsa.
.
SOURCE: www.uthaimin.com

Bin uthaimin


TAMBAYAR 'YAR UWA KHADIJAT S HALLIRU RADDAH ZUWA GA SALAFIYYAH NETWORK NIGERIA
.
Assalamu alaikum yan uwana musulumai ina da tambaya ne akan dalilin da yasa ba'a saka karatutukan Mal Albaniy Zaria (Rahimahullah) a sunnah TV?
.
ALLAH YA JIKAN ASH SHEIKH MUHAMMED AUWAL ALBANIY ZARIA, SHEIKH JA'AFAR MAHMUD ADAM DASURAN WADANDA SUKA BIYO SU DA KYAUTATAWA. ALLAH YA DAUKAKA 'KUNGIYAR JAMA'ATU IZALATUL BIDI'A WA IKAMATUL SUNNAH DA MALAMANTA NA CIKI DANA WAJE!!!
.
Toh malama Khadijah, a gaskiya Salafiyyah Network Nigeria bata sani ba. Amma tunda akwai Sheikh Ibrahim Disina a wannan dandalin (shugaban sunnah tv) wata 'kila zai amsa miki wannan tambayar naki.
.
Hanzari ba gudu ba! An taba yima Ash-Sheikh Albaniy Zaria irin wannan tambayar na ki a tafseerin 'karshe da ya gabatar a rayuwarshi (2013). Amsar daya bada itace;
.
'' Sunnah TV gidan duk wani Ahlussunnah ne mai farar zuciya. Saboda haka ko ansa karatunshi ko ba'a saka ba tana wakiltar da'awar duk wani ahlussunnah ne don bashi da wani ilimin dazai karantar wanda malaman da ake sakawa a gidan Tvn baza su iya karantarwa ba. Ya 'kara dacewa daga cikin projects 'din da'awarshi akwai gidan television wanda insha'Allahu ta'ala ko yana raye ko baya raye za'a gina wanda anan insha'Allahu ta'ala za'a rinka jin muryarshi. Daga 'karshe ya rufe bayaninshi da cewa kowa yaje ya saka Sunnah TV a gidanshi domin shi kanshi ma'abocin kallon tashar Sunnah tv.
.
Don jin cikakken wannan bayanin toh ki nemi kaset 'din tafsirin 2013.
.
Subhanakallahumma wabi hamdika, ash-hadu anla'ila ha illa anta astagfiruka wa'atubu ilaik.

Albani radda

ANYA MUTUMIN NAN NA 'KASAR AUSTRALIA (STEVE DAVIES) BAI GAYA MANA HAKIKANIN WAYANDA SUKA KASHE MANA MALLAM BA?
.
Tun bayan kashe Ash-Sheikh Albaniy Zaria (Rahimahullah),al'ummar duniya sun shiga cikin rudu sun yi jugun suna cewa shin su waye zasu iya aikata irin wannan ta'asa?
.
Wannan Rudun da suka shiga ciki ta samo asali ne kasantuwar nahiyoyin da suke tuhuma suna da yawa.
.
Hakan kuma bai wuce nasaba ga irin gaskiyar da mallam yake tsagewa akan gomnatin Nigeria da 'kasashen yamma da kuma dukkanin 'kungiyoyin musulunci tun daga Shi'a har zuwa boko haram da sauransu.
.
Kwatsam muna zaune sai jagorar 'yan Shi'a Zakzaky ya fito yace gomnati ne tayi kisan. Mun yi tunanin gomnati zata fito ta 'karyata Zakzaky amma sai tayi shiru kamar an shuka dussa
.
Ba'a dade ba kawai sai hukumar SSS (state security service) a 'karkashin jagoranci Merylyn Orga ta fito ta bayyana wasu yara 'yan boko haram da cewa su suka yi kisan.
.
Tun a wancan lokacin abun da ya shige mana duhu akan wannan rahoton na SSS shine; Shin inma har ya kasance 'yan boko haram 'dinne toh su waye suka turo su?
.
Shin me yasa har yanzu ba'a gurfanar dasu a gaban kotu ba?
.
Allahu Akbar! Kwatsam sai ga mutumin 'kasar Australia nan a 'karkashin jagorancin aikin da gomnatin Nigeria ta saka shi, ya fito ya gayama duniya cewa tsohon babban Hafsan Sojojin Nigeria Ihejirika da Ali Modu Sherriff na PDP su suke sarrafa (sponsoring) boko haram.
.
Allahu Akbar! Wa iz 'kataltum nafsan Fadda'ra'atum feeha wallahu Mukhri jum ma'kuntum taktumun.
.
Zakzaky Yace gomnatin Nigeria Ne. Gomnatin Nigeria tace 'yan Boko haram ne. Su Kuma Musulmai sunce suwa suka turo 'yan boko haram 'din? Shi kuma Wakilin Johnathan Steve Davies Yace Ihejerika da Modu Sherrif ne ke Sarrafa boko haram.
.
Shin anya wannan bai tabbatar mana da cewa Ihejirika bane da 'dan'uwanshi suka aikata mana wannan ta'asar ba?
.
Koma dai menene! Insha'Allahu Ta'ala mallam zai shako makasansa a ranar lahiri ya gabatar dasu a gaban Allah yace ya Allah ka tambayesu;
.
''ME NAYI MUSU SUKA KASHE NI?
.
Allah (SWT) muke roko da ya amshi Shahadar Mallam da 'dansa Abdullahi da matanshi Ummu AbdulBarri.
.
Mu kuma innamu tazo Allah kasa mu cika da kyau da imani.

Albani ustralllia


WANNAN KISAN KARE DANGIN DA KIRISTOCI SUKE MANA SUN SHIRYA SHINE TUN TSAWON SHEKARA SITTIN BAYA.
.
Daga: Engr Abu-Ameena Bn Khamis
.
Allahu Akbar! Wannan maganar ta fito ne daga bakin wani mash-hurin malamin addinin musulunci a lokacin da ya kawo ma Ash-Sheikh Albaniy Zaria Rahimahlluah Ziyara a cibiyar ilimi na Daruul hadeethis Salafiyyah dake zaria.
.
Prof Dauda Ojobi yace:-
.
'' A lokacin da yake cikin addinin kiristanci a shekarar 1954. 'Kungiyar kiristoci ta Nigeria ta gabatar da taruka a Jos kuma shine sakataran tarukan a lokacin.
Prof Dauda Ujobi yace daga cikin abin da suka cimma shine: Za su aika wasu daga cikin mutanen su
kiristoci kasashen musulmi a matsayin tubabbu kuma don su koyo ilimin addinin musulunci. Manufar su shine su dawo Arewa a matsayin masu kira ga addinin musulunci.
.
Za suyi iqirarin komai na zamani haramun ne ta hanyar haka zasu kawo hargitsi a arewa.
.
Ya 'kara da cewa ; Karshen manufar su kamar yadda suka cimma a taron shine ya zamana ba wani yankin Arewa da zai kasance yana cikin lumanar karantar da addinin musulunci ta hanyar tarwatsa kowa da kashe na kashewa.
.
Allahu Akbar! Shin yanzu kama jirgin shugaban kiristocin Nigeria dankare da kudi ze siyo makamai zai baku mamaki? Shin yanzu mene ne mafita?
.
Latsa wannan link 'din na 'kasa domin sauraren cikaken Bayanin

Www.kiwi6.com/file/rkrkulz5cf
1521547 794375620604779 8651206884032405104 n





Kuna iya bin mu ta group dinmu na SALAFIYYAH NETWORK NIGERIA a shafin face book

Kuna iya bin Engr Abu-Ameena Bn Khamis ta shafin face book

koma saman shafi

→Labarai

HASSADA MUGUN CIWO, ANIYARKA TABI KA ABDULJABBAR KA SANI HALIFA QARIBULLAH YAFI KARFINKA,(Imam Aliyu Indabawa)

HASSADA MUGUN CIWO, ANIYARKA TABI KA ABDULJABBAR KA SANI HALIFA QARIBULLAH YAFI KARFINKA,(Imam Aliyu Indabawa)
.
Wannan da kuke gani shine Dr kalifa qaribullah nasiru kabara, wanda ya kasance shine halifan dariqar qadiriyya, kuma muna girmama shi saboda halayensa na kawaici da sanin ya kamata, sai Allah ya jarrabe shi da wani taqadarin kani wanda ya addabe shi da hassada kullum cikin zaginsa yakeyi yana kushe shi yana aibata shi,
.
Asali abinda yasa yake masa wannan hassadar shine saboda halifa qaribullahi Allah yayi masa ni'imomi da baiwarwaki wanda shi kanin nasa bashi dasu, yafi shi duk wani abu da ake so, ta bangaren daukaka, da Ilmi da 'yaya da kudi da magoya baya da manyan mutane Sarakuna, uwa uba kuma yana da hankali wanda shi kanin nasa yayi rashinsa,
.
Sannan ga mukamin Halifa da yake rike dashi wanda shine yafi komai kona masa zuciya da motsa masa hassada, saboda shi a tunaninsa ai shine yafi cancanta daya gaji mahaifinsa ya zama halifan qadiriya saboda tunaninsa wai yafi Qaribu Ilmi shine yasa ya dade yana zagin Halifa karibu yana cutar da shi ta ko'ina yana nuna hassadarsa gare shi, dayake dama hassada ga mai rabo taki ce, shi kuma halifa Qaribu kullum sai kara gaba yakeyi har wasu kashashen ma suna bashi lambar yabo ta girmamawa amman duk da haka har yanzu Abdun jabberun yaki ya gane,
.
Ku duba Ko A haife qaribu ya haifi Audujanbiri amman saboda tantiranci da rashin tarbiya babu irin zagin da bayayi masa akwai Lokacin Audu janbiri yace,"qaribu wai babarsa da cikinsa ta shigo gidan malam wai qaribu ba dan malam bane wai shege ne kuma a duba dashi qaribun dashi Audu janbirin waye yake kama da malam kabara, kuma wai a cikin taron daruruwan mutane yayi wannan maganar, ba wannan kadai ba da dai sauran maganganu masu muni wanda shi kuma qaribun dayake yasan kanin nasa yana da ragaggen hankali baya biye ta tashi kullum hakuri yake dashi, lokacin da magoya bayan qaribu suka ga abin nasa fa ya wuce tunani ya koma tsantsar iskanci da rashin mutunci sai sukace suma dai dai suke da dan iska, inda duk lokacin da yazo wani taro ko maukibi sai suki su barshi ya shiga idan ma ya shigo sai su jefe shaidani, haka suka dinga yiwa dan banza daga karshe dayaga uwar bari da kansa yaje ya bawa halifa Qaribu hakuri akayi salhu tun daga lokacin abu ya danyi shiru,
.
Sai yanzu ya tsiro da wani iskancin, yana zagin Halifa qaribullah, dama tun asali kasancewarsa mutum mai neman Suna kota halin qaqa, amman hakan yaki samuwa yasa yake cin zarafi da cin mutuncin mutane sai kaji shi yana zagin babban malami wanda ya haife ya haife shi,
.
haka ya koma ta6o 'yan siyasa wanda duk gomnatin da take kai to sai yayi ta zaginta kenan har sai an bashi wani abun, misali lokacin mulkin kwankwaso na farko haka ya dinga bi yana zagin kwankwaso har sai da kwankwaso ya bashi fili a gwale filin mushe, wanda yanzu haka a cikin filin yayi gidansa yayi masallacin juma'a filin ma hakkin mutane, lokacin da kwankwaso ya tafi shekarau yazo sai ya koma 6angaren shekarau yana masa jagaliya da yaga shekarau baya bukatar tafiya da 'yan jagaliya irinsu sai ya dinga zagin shekarau har yake cewa idan yabi shekarau to shi dan zina ne, ana nan sai malam shekarau yayi masa wani babban Alkhairi wanda ya fito yace duk duniya ibrahim masu girma guda uku ne, da Annabi ibrahim da ibrahim inyass da ibrahim shekarau, lokacin da kwankwaso ya dawo be tafi dashi ba sai ya koma zagin kwankwaso ko lokacin da kwankwaso ya ta6a Annabi S.A.W sai ya dinga zagin kwankwaso har yace dashi ya zama kafiri, haka ya tara mutanensa har ya dauki sulke da kwalkwali ya saka a jikinsa , ya umarci 'yan jagaliyar yaransa suka rike makamai suka fito gari suna zanga zanga, amman yadda zakasan munafiki ne sai gashi lokacin da yake wa 'yan tijjaniya raddi yana siffanta Muhammadu Rabi'u kwankwaso da mai kishin musulunci,
.
Ba 'yan siyasa kadai ba, tuntuni shine yau ya ta6o 'yan izala gobe kaji ya ta6o 'yan tijjaniyya jibi ya ta6o 'yan qadiriya ko wani malami wanda bashi da dariqa, tun mutane suna biye masa har suka gane manufarsa suka gane cewa yana fama da ta6in hankali ta yaya zasu tsaya suna rigima da mahaukaci sai duk suka kyale karen yaje yayi ta haushinsa shi kadai, daya ga haka sai ya canza dabara akan ya samu masoya wanda zai dinga damfararsu 'yan kudaden su, haka yayi ya dinga tara karatu da sunan kishin Annabi da soyayyarsa nan ko babu abinda yake koyawa sai jahilci da dure duren ashariya, Kunji AMIRUL FASIKINA HUJJATUL JAHILINA kenan,
.
Koda matasan suka fuskanci babu wata tsiya na karatu da ake karuwa da Abdun jabberun sai duk suka dinga watsewa suna karewa kamar hatsin guziri, daya fuskanci neman Sunan dayake har yanzu a kano ba'asan da wani Abdun jabberun ba, wanda ko a gwale filin mushe babu wanda yasan dashi, kuma gashi na cefane yana gagararsa sai ya tsiro da wani iskanci da zindikanci na zagin sahabban Annabi inda yaje ya kar6o kwangilar kudi wajen Iro jakin zariya L.A don ya samu magoya baya, lokacin daya fara zagin sahabbai irinsu sayyadi Mu'awiya A,S yana kawo hadisai ta karfin tuwo yana juya musu ma'ana malaman Sunnah sun zabura suna mayar masa da raddi wanda shi dama abinda yake so kenan ayi ta zancensa yayi suna a san dashi, bayan lokacin da malam Alqasim yayi buji buji dashi akan littafinsa muqaddimatul Khaziba, haka aka dinga fama dashi akan yazo a zauna ayi muqabala akan wannan mas'alar ta fi'atul bagiya, amman hakan yaki yuyuwa kullum ya zauna sai dai dure duren ashariya da tsine tsine da karya da cika baki da alfhari da ihu da kowayee, a haka yanzu zindiqancin nasa da iskancin nasa har yazo ya fara zaginsu sayyadi Abubakar yana karyatashi akan hadisin gadon Annabi, yana zagin sayyadi usman akan wai azzalumi ne a lokacin mulkinsa, yanzu da malaman Sunna suka gane cewar bamagujen dan shi'ar yanada ta6in hankali sai duk suka kyale shi, don idan banda me ta6in hankali babu wanda zai dinga zagin sahabbai yana tuhumarsu,
.
To sai rannan mai tatsinen a wani shirmen sa dayake yi wai da sunan karatu yana karanto wani soki burutsun littafinsa mai suna MUQADDIMATUL KHAZIBAH babi mai taken LA TASABBU AS'HABI sai yazo maganar akan wani Hadisi da Halifa Qaribullah ya rawaito akan Sayyadi Ali inda ya dinga ciwa halifa Qaribullah mutunci yana fada masa maganganu na 6atanci yana cewa zasu 6ata dashi akan imami, ba don komai yake haka ba wai don kawai halifa shi yana girmama sahabban Annabi baya zaginsu sannan yana fadar gaskiya a duk inda ta dace, ko a wani haukan karatun Amirul jahilina na baya naji wai har yana cewa wai qaribu yayi maja da 'yan izala yana kiransa da nasibi,
.
To janbiri idan ma izalar qaribu ya koma ai ya gano itace gaskiya ne, tunda gaskiya yake bi, kuma kowa yayi shaidar cewa qaribu malami ne me koyar da karatu wanda yakanyi tafsiri a gidan sarki, sannan a ranaku yakan karanta sahih muslim da Algunya da ishreniyya, ba kamar ka ba wanda babu abinda ka iya sai dai ka tara mutane kayi ta dura ashariya kana tsine tsine kana sheka karya kana hauka suna ihu kana koya musu ta'addanci kana cewa su dauki makamai suje masallacin da akai rikici a baya su kashe 'yan izala, kai saboda ci da qarfi irin na mai mai tatsine sai kaje ka rubuto hadisai da ayoyi kazo kayi ta karantasu da kyar kana kuskure a cikin ayoyin, mutumin da ko haddar simini daya bashi da ita a Qur'ani, kai ko Ayar Muhammadur rasulillah ma daya karanto akwai kusa kurai a cikinta, kai Abduljbbar wallahi jahili ne na karshe, na tabbata ko fatiha ma idan zai karanta sai an ci gyaransa, ayar suratul ma'ida IN TU AZZIBHUM FA INNAHUM IBADUK WA IN TAGFIR LAHUM FA INNAKA ANTAL AZIZUL HAKIM duk da rubuto ayar yayi amman shi jahilin sai cewa yayi FA INNAKA ANTAL GAFURUR RAHIM haka farkon raddinsa ga 'yan tijjaniya yace" ALLAZINA HUM IZA ASABATHUM sai ya sake cewa" ALLAZINA IZA ASABSATUM.. Kunji chakwakiya fa, haka a wani karatunsa yana karanta tarihin matan Annabi S.A.W wai ayar da take suratul Ahzab tana gargadi ga Matan Annabi itace" INKUNTUNNA TURIDNAL HAYATUD DUNYA WAZINATAHA FATA A LAINA UMATTI U KUNNA WA USARRIH KUNNA amman jahilin wai sai yace." FATA A LAINI UDALLIQUKUNNA WA USARRIH KUNNA, kuji jahili wanda beyi karatun Qur'ani ba, sannan ayar ta suratu Ahbaz yazo kan kissar Zainab da zaid ayar itace WAMA KANA LI MU'UMINUN WALA MU'UMINATUN IZA QADALLAHU WARA SULUHU AMRAN AY YAKUNA LAHUMUL KIYARATU MIN AM RIHIM WAYAY YA'ASILLAH WARA SULAHU FAQAD DALLA DALALAN MUBINA amman kasgin jahilin sai yace" FAQAD DALLA DALALAN BA'IDA kunji jahili wanda beyi karatun qur'ani ba. Idan nace zan dinga kawo kuskuren wannan hanfefen sai na kawo sunfi hamsin, don ko aya daya bazai iya ba ammn ya dinga wa Qur'ani Hawan qawara.
.
To wai wannan kuhungun jahilin kasgi, wai a fadar wasu wawayen shine malami kuma wai hanferen shine jagoransu, kai godiya ta tabbata ga Allah daya saka mabiya wannan zindiqin suka kasance wawaye mahaukata, tabbas kamar yadda suke fada na yarda Amirul jahilina shine mujaddadin wawaye na wannan zamani.
.
Abdun jabbarun sai dai kayi hakuri, na gaba yayi gaba na baya sai labari, halifa qaribullah yayi maka nisan da har abada bazaka ta6a kamo koda farcensa saba, sai dai ka cigaba da haukanka da zagin nasa idan bakayi wasa ba hassada itace zata sheke ka har lahira, kuma ko shi Halifa Qaribun yasan kanada matsalar kwakwalwa, wanda ya kamata yasan yadda za'ayi a kaika dawanau tun kafin haukan naka yakai ka fara zagin annabawa kana tuhumarsu, abduljabbar nidai ina maka Addu'ar Allah ya baka lafiya ya rabaka da wannan cutar ta ta6in hankali da take damunka, su kuma jahilan da suke biye maka. Allah ya ganar dasu su fara zuwa makaranta suy karatu, don babu wani mai ilmi da hankalin da zai dauki wannan galmashoran mai dure duren ashariya da zagin sahabban Annabi wai da sunan malami.
.
Tofah dama ance duk yadda akai da jaki dai yaci kara, yanzu gaskiyar nan dana fada fa sai ka samu wasu jakunan sun fara tunkuyi koh? To jakunan kogo ayi ta tunkuyi lafiya, nidai babu jakin daya isa ya tunkuye ni na juya nace zan rama, ko shi kansa babban jakin naku na kogo be isa balle wasu karnukan farauta, saboda haka 'ya'yan mutu'a. Karnukan farauta haihuwar mutu'a kuy ta haushi lafiya.
.
Har yau dai
.
Angom Fatima ne Abban Sadiq
.
I.A.I

Back to posts
Comments:
[2016-02-24 12:46:57] Moh'd B. Ussaini :

To Maza Kaje Ka Tuba Domin Kayi Karya Gami Da Hahilci Bataimiye

[2016-07-01 13:33:04] ANAS AMEEN :

ALLAH YA SAWAKE AMEEN.

[2016-05-12 10:18:42] ummu aisha :

SLM

[2016-07-24 11:41:23] Aminu Rabiu Garun Gudinya Babura :

Ya Allah kaganar damu gaskiya katseratar da diga diganmu daga saba maka amin

[2016-07-30 09:45:55] MHD SANI :

Allah yasaka wa abduljabbar anyi masa kage kuma baze yafeba

[2016-09-16 20:21:32] ibrahimaliyusumaila@gmail.com :

kai arasa wanda za aiwa sharri sai abduljabbar

[2016-08-28 13:57:17] Shamsuddeen lawal anchau :

Tofa!

[2018-02-07 06:24:04] Zaharaddeen m.abubakar deen :

to allah yaimana jagora amin mudai sunnah sak.


UNDER MAINTENANCE

Share|

Kaima shiga a tattauna da kai
* No boards.

Online: Guests: 2


→Ra'ayin jama'a game damu

 IDAN KANA BUKATAR A TALLATA MAKA HAJAR KA A WANNAN SHAFIN DA SAURAN SHAFUKAN MU KANA IYA TUNTUBAR MU TA WADANNAN HANYOYIN KAMAR HAKA:


Email: bjournalist55@hotmail.com

Phone No: 09035830253

Facebook: Basheer Journalist Sharfadi

Address: Ittihad Computer Centre,  No 92 Daneji Kano


MAI TALLA SHI KE DA RIBA


*Bayanan ka*
Browser din da ka hawo Mozilla

Kasar da kake United States

Adadin Maziyarta 474047

Adadin Wadanda Sukayi Comment 65691

A Wadanda Suka Shiga Tattaunawar Mu 54


Follow @bjournalist55
→Yi Adding Dina Ta Facebook
→Yi Like Na Dakarun Sunnah Page
→Yi Like Dina Ta Facebook

*Shafuka Masu Alaka Da Mu*

→Basheer Sharfadi wordpress
Basheer Sharfadi Blog Spot
UP
→Home

Basheer Journalist Sharfadi (Abu Hafsah)
ISLAMIC DATE
  • phpimg2.php?it&ic=yellow



  • Click to Sms
    Click to Call


    Basheer journalist sharfadi3
    Coollogo com-1281358