Teya Salat
Google69490f6862051cb8
google-site-verification: google69490f6862051cb8.htmlgoogle-site-verification: google69490f6862051cb8.htmlgoogle-site-verification: google69490f6862051cb8.htmlBasheer journalist sharfadi14

Basheer journalist sharfadi14.jpg6
Basheer journalist sharfadi 11 1
Maraba Da Zuwa Wannan
Shafi Mai Al-barka 1

☀ Zabi inda kake son shiga ☀
Menunks
→Home
→Akidojin Ahlussunnah
→Addinin musulunci (35)
→40 Hadith (50)
→Fadakarwa (120)
→Neman labarai (20)
→Shi'a Kafirci (50)
→Hadith (55)
→Khudubobi (24)
→Tarihin magabata (60)
→Raddi / Maida martani (99)
→Face book post (30)
→Monthly Archives (60)
→Tambaya da Amsa (20)
→Sahabban Annabi {s.aw} (50)
→Taskar maluman sunnah (25)
→Akidar Y'an Shi'a Dangane da Al'kur'ani
→Fassarar Usulussunnah (20)
→Sheik Ja'afar {Rahimahullah} (65)
→Sheik Abubakar Gumi {Rahimahullah} (30)
→Sheik Dr. Muhammad Sani R/Lemo
→Salafiyyah Network Nigeria (100)
→Adam Sani Abu-Umayrah (99)
→Salaf Ustaz (79)
→Malama Ummi Ahmad Katsina
→Malama Amina Saleh Mande
→Labarai (40)
→Nishadantarwa (10)
→Siyasar Nigeria (9)
→Vidio (33)
→Audio (66)
→Hotuna (120)
→Internet Cheat (90)
→Site Achieve
→Application (10)
→Games (8)
→About me (01)

Wannan shafin mallakarCoollogo com-1281358 3
Ne




SHAFI DON KARUWAR MUSULMI
Maraba da zuwa wannan 6angare na
sheik Abubakar mahmud gumi (Rahimahullah)
Sheik gumi
Wanda wannan 6angare ze dinga zuwa muku kai tsaye daga dan uwanku
Lawal Mamman Bilbis
1979895 464683747008234 2121258314242661027 n
Kuna iya bin M. Lawal Mamman Bilbis ta shafin facebook
Wanda ya tsara ya kuma shirya
Basheer journalist sharfadi {Abu Hafsat}
Asha karatu lafiya


Gaskiyar maganar cewa wai malam yace siyasa tafi sallah?
(FATAWOYIN SHIEKH ABUBAKAR GUMI)
.
Gabatarwa
.
Alhamdulillah, wassalatu wassalamu ala Rasulillah.
.
Da farko ina mai farawa da godiya ga Allah Wanda Shine Ya azurta mu da wannan katafaren malami a wannan nahiya tamu wanda karantarwar sa ta karade Nigeria dama duniya gaba daya wato margayi Mallam Abubakar Mahmud Gumi, malami da yayi kokari kwarai da gaske ganin an kadaita Allah a wajen bauta ya kuma kori Bid'ah da shirka a wannan nahiyar tamu.
.
Muna rokon Allah Ya saka masa da mafificin alkhairin Sa, Allah Ya kai rahama a kabarin mallam Ya kuma albarkaci zuri'ar da ya bari.
Bayan haka ina mika godiya da jinjina ga shehin malami wato Malam Musa Lawal Funtuwa wajen kokarin da yayi na tattaro wasu daga cikin fatawoyin da aka yiwa Malam a lokacin da yana raye.
.
Malam yayi kokari kwarai da gaske wajen tsara fatawoyin ta yadda kowa zai karanta kuma ya fahimta.
.
Muna rokon Allah ya saka masa da alkhairi.
.
Insha Allahu zamu cigaba da kawo maku fatawoyi da amsar su daya bayan daya kamar yadda malam ya rubuta.



(FATAWOYIN SHIEKH ABUBAKAR GUMI)
.
Fatawa ta (1)
.
TAMBAYA: Wai idan mutum ya riga yayi kalmar shahada wajen mutuwa, ko ya mutu ba zai ru6e ba?
.
AMSA:-
.
A'a, akwai dai wadanda akace ba su ru6ewa, su ne Annabawa, da masu karantar da mutane, da mai kiran sallah.
.
Dafatan Allah Ya sa mu daga cikin su.


Koma saman shafi

→Labarai

KUNGIYAR IZALA TA KANO TAKAIWA SHUGABAN DARIKAR KADIRIYYA NA YAMMACIN AFRIKA ZIYARA

KUNGIYAR IZALA TA KANO TAKAIWA SHUGABAN DARIKAR KADIRIYYA NA YAMMACIN AFRIKA ZIYARA
A yammacin jiya lahadi ne 13/11/1435=7/9/2014 kungiyar Izala reshen jihar kano karkashin jagorancin Sheikh Dr. Abdullahi Sale Pakistan da gangamin 'yan majalisar zartarwarsa da Shugabannin kungiyar na kananan hukumomi 44 suka kaiwa gidan Kadiriyya ziyarar girmamawa. Tawagar wacce ta samu tarbar Shugaban Darikar Kadiriyya na Afrika ta Yamma, "Sheikh Karibullah Dr. Nasiru Kabara" tare da manyan hadimansa. A lokacin da yake gabatar da jawabinsa, Shugaban Izala na jihar kano, ya bayyana wannan ziyara a matsayin makamanciyar wacce magabatan mu suka yiwa Juna a shekaru sama da ashirin da suka gabata, inda Marigayi Sheikh Dr. Nasiru Kabara yayi tattaki har garin Kaduna ya ziyarci Sheikh Abubakar Mahmud Gumi, daga baya shima yayi ramakonta. Ya bayyana makasudin wannan ziyara don sabunta 'yan uwantakar dake tsakanin mu ce, da kuma kara samun fahimta da sassauta harshe ga juna, da samun cikekken hadin kai akan koyarwar alkur'ani da Hadisan Manzon SAW bisa fahimtar magabata Sahabbansa da wadanda suka biyo bayan su. Ya bayyana rashin hadin kan musulmi da irin kalubalen da muke fuskanta a zamantakewar mu na wannan lokaci, zubar da jini da koma bayan kasuwanci da sauran al'amura. Da yake maida jawabinsa, Shugaban Darikar Kadiriyya Khalifa Sheikh Karibullah, ya bayyana farin cikin sa da wannan kasaitacciyar ziyara. Ya yiwa Allah godiya da ya nuna masa wannan rana data tunatar dashi makamanciyar ta data faru ga magabatansa. Ya yaba matuka da irin wannan yunkuri da Dr. Abdullahi Saleh Pakistan yake yi na sassauto da damuwa da kuma hadin kan musulmi, yace musulmi ba za suyi kima da kwarjini ba har sai sun dunkule wuri guda. Sheikh Karibullah ya gabatar da kyautar litattafai ga Jagoran na Izala a matsayin tukwicin yaba wannan ziyara. Daga cikin wadanda suka rufawa Shugaban na Izala baya har da Shugaban kwamitin Yada labarai na kasa na Kungiyar, kuma kakakin ta a jihar Malam Ali Dan Abba da kuma Shugaban majalisar Dattijan kungiyar Sheikh Abdulwahhab Abdullah. Allah ya sanya albarka da alkhairi a cikin wannan ziyara mai cike da darussa.
Back to posts
Comments:
[2014-09-08 18:02:43] sunusi :

Allah ya hada mana kan malumanmu Allah ya taimaki musulunci

[2015-01-24 12:51:16] Aminuadam :

To Allah ya kara hadin kan a kauda kalmar kafurci,

[2016-08-04 16:30:15] Iliyahussaini3 @gmail :

Allah yakawo mana hadinkai mai dawwama har abada domin shine kashin gadon bayanmu mu matasa daliban Ilmi.


UNDER MAINTENANCE

Share|

Kaima shiga a tattauna da kai
* No boards.

Online: Guests: 1


→Ra'ayin jama'a game damu

 IDAN KANA BUKATAR A TALLATA MAKA HAJAR KA A WANNAN SHAFIN DA SAURAN SHAFUKAN MU KANA IYA TUNTUBAR MU TA WADANNAN HANYOYIN KAMAR HAKA:


Email: bjournalist55@hotmail.com

Phone No: 09035830253

Facebook: Basheer Journalist Sharfadi

Address: Ittihad Computer Centre,  No 92 Daneji Kano


MAI TALLA SHI KE DA RIBA


*Bayanan ka*
Browser din da ka hawo Mozilla

Kasar da kake

Adadin Maziyarta 508578

Adadin Wadanda Sukayi Comment 65691

A Wadanda Suka Shiga Tattaunawar Mu 54


Follow @bjournalist55
→Yi Adding Dina Ta Facebook
→Yi Like Na Dakarun Sunnah Page
→Yi Like Dina Ta Facebook

*Shafuka Masu Alaka Da Mu*

→Basheer Sharfadi wordpress
Basheer Sharfadi Blog Spot
UP
→Home

Basheer Journalist Sharfadi (Abu Hafsah)
ISLAMIC DATE
  • phpimg2.php?it&ic=yellow



  • Click to Sms
    Click to Call


    Basheer journalist sharfadi3
    Coollogo com-1281358