Insane
Google69490f6862051cb8
google-site-verification: google69490f6862051cb8.htmlgoogle-site-verification: google69490f6862051cb8.htmlgoogle-site-verification: google69490f6862051cb8.htmlBasheer journalist sharfadi14

Basheer journalist sharfadi14.jpg6
Basheer journalist sharfadi 11 1
Maraba Da Zuwa Wannan
Shafi Mai Al-barka 1

☀ Zabi inda kake son shiga ☀
Menunks
→Home
→Akidojin Ahlussunnah
→Addinin musulunci (35)
→40 Hadith (50)
→Fadakarwa (120)
→Neman labarai (20)
→Shi'a Kafirci (50)
→Hadith (55)
→Khudubobi (24)
→Tarihin magabata (60)
→Raddi / Maida martani (99)
→Face book post (30)
→Monthly Archives (60)
→Tambaya da Amsa (20)
→Sahabban Annabi {s.aw} (50)
→Taskar maluman sunnah (25)
→Akidar Y'an Shi'a Dangane da Al'kur'ani
→Fassarar Usulussunnah (20)
→Sheik Ja'afar {Rahimahullah} (65)
→Sheik Abubakar Gumi {Rahimahullah} (30)
→Sheik Dr. Muhammad Sani R/Lemo
→Salafiyyah Network Nigeria (100)
→Adam Sani Abu-Umayrah (99)
→Salaf Ustaz (79)
→Malama Ummi Ahmad Katsina
→Malama Amina Saleh Mande
→Labarai (40)
→Nishadantarwa (10)
→Siyasar Nigeria (9)
→Vidio (33)
→Audio (66)
→Hotuna (120)
→Internet Cheat (90)
→Site Achieve
→Application (10)
→Games (8)
→About me (01)

Wannan shafin mallakarCoollogo com-1281358 3
Ne




SHAFI DON KARUWAR MUSULMI
Maraba da zuwa wannan 6angare na
sheik Abubakar mahmud gumi (Rahimahullah)
Sheik gumi
Wanda wannan 6angare ze dinga zuwa muku kai tsaye daga dan uwanku
Lawal Mamman Bilbis
1979895 464683747008234 2121258314242661027 n
Kuna iya bin M. Lawal Mamman Bilbis ta shafin facebook
Wanda ya tsara ya kuma shirya
Basheer journalist sharfadi {Abu Hafsat}
Asha karatu lafiya


Gaskiyar maganar cewa wai malam yace siyasa tafi sallah?
(FATAWOYIN SHIEKH ABUBAKAR GUMI)
.
Gabatarwa
.
Alhamdulillah, wassalatu wassalamu ala Rasulillah.
.
Da farko ina mai farawa da godiya ga Allah Wanda Shine Ya azurta mu da wannan katafaren malami a wannan nahiya tamu wanda karantarwar sa ta karade Nigeria dama duniya gaba daya wato margayi Mallam Abubakar Mahmud Gumi, malami da yayi kokari kwarai da gaske ganin an kadaita Allah a wajen bauta ya kuma kori Bid'ah da shirka a wannan nahiyar tamu.
.
Muna rokon Allah Ya saka masa da mafificin alkhairin Sa, Allah Ya kai rahama a kabarin mallam Ya kuma albarkaci zuri'ar da ya bari.
Bayan haka ina mika godiya da jinjina ga shehin malami wato Malam Musa Lawal Funtuwa wajen kokarin da yayi na tattaro wasu daga cikin fatawoyin da aka yiwa Malam a lokacin da yana raye.
.
Malam yayi kokari kwarai da gaske wajen tsara fatawoyin ta yadda kowa zai karanta kuma ya fahimta.
.
Muna rokon Allah ya saka masa da alkhairi.
.
Insha Allahu zamu cigaba da kawo maku fatawoyi da amsar su daya bayan daya kamar yadda malam ya rubuta.



(FATAWOYIN SHIEKH ABUBAKAR GUMI)
.
Fatawa ta (1)
.
TAMBAYA: Wai idan mutum ya riga yayi kalmar shahada wajen mutuwa, ko ya mutu ba zai ru6e ba?
.
AMSA:-
.
A'a, akwai dai wadanda akace ba su ru6ewa, su ne Annabawa, da masu karantar da mutane, da mai kiran sallah.
.
Dafatan Allah Ya sa mu daga cikin su.


Koma saman shafi

→Labarai

Shawarwari 52 daga bakin Marigayi Sheikh Jafar Mahmoud Adam Kano zuwa ga ma'aurata.

Sheik Ja'far mahmud Adam

Da sunan ALLAH mai gamammiyar rahama mai jinkai, tsira da aminci su tabbata ga Annabin rahama, da alayansa, da sahabbansa, da duk wadanda suka bi tafarkinsu har ya zuwa ranar tashin al-kiyama.
.
Bayan haka,
.
shakka babu, a wannan zamani 'yan mata da zawarawa kai harma da matan aure suna cikin zullumi da tsoro da rashin kwanciyar hankali, saboda yadda aurensu yake yawan mutuwa, bayan kuma, an dauki dogon lokaci ana soyayya a tsakani.
.
Ga wasu Shawarwari wadan da idan mata sukayi la'akari da su insha ALLAH za'a samu kyautatuwar zaman aure. Muna addu'ar ALLAH ya bada ikon kiyayewa.
.
1- Aurenki ya zama domin neman yardar
ALLAh kikayi ba dan tara abin duniya ba.
2- Kada ki zama mai kwadayi wajen zaben
mijin Aure.
3- Ki zabawa 'ya 'yanki uba ta hanyar Auren
wanda ki ka yarda da addininsa da dabi'unsa
harma da dangantakarsa.
4- Ki zama mai riko da addini a gidan
mijinki.
5- kada ki zama mai kauracewa shimfidar
mijinki. Hakan na da matukar hadari a
rayuwa aure.
6- Ki zama mai hakuri da halayyar mijinki.
7- Ki zama mai matukar biyayya ga mijinki.
8- Ki zama kwararriya wajen iya kwalliya
kala-kala.
9- Ki zama kwararriya wajen iya girki kala-
kala.
10- Ki zama kin iya barkwancin magana
wajen baiwa mijinki dariya.
11- Kada ki zama mai rainuwa a cikin duk
abinda mijinki ya baki.
12- Ki dinga wanke bakinki da safe da yamma
da kuma lokacin kwanciya barci.
13- ki zama mai tsaftar jikinki, gidanki,
abincinki, da sauransu.
14- Ki dinga girmama Iyayan mijinki da 'yan
uwansa da abokansa.
15- Kada ki zama mai satar kayan mijinki.
16- Kada ki zama mai satar fita unguwa.
17- Ki guji Leke a gidan mijinki, dan yana
daga cikin abinda yake raba Aure a tsakanin
Hausawa.
18- Ki dinga godewa mijinki a cikin abinda ya
baki.
19- ki kiyaye abinda mijinki ya fi so.
20- ki kiyaye abinda mijinki ya fi sonci da
safe, rana, dakuma dare.
21- Ki dinga yabawa mijinki kwalliyarsa.
22- Ki dinga yawan neman shawarar mijinki
akan duk wani al'amari da zaki yi.
23- Kiyi kwalliya ki tsane tsaf kafin dawowar
mijinki.
24- Ki dinga sanya turaren wuta a dakinki,
kuma ki kasance mai sanya turare a jikinki a
duk lokacin kwanciya.
25- Lallai ki yi kokarin gama aikace-aikacenki
kafin dawowar mijinki.
26- Kada ki bari mijinki ya dawo ya sameki
gaja-gaja, ki sani kazanta tana haifar da
kiyayya.
27- Ki zama mai yawan canza zanen kunshin
kafarki da kuma zanen kitso.
28- Kada ki ce mijinki sai ya saya miki abinda
ba shida ikon saye.
29- Lallai ki yi amfani da ilimi wajen yanke
dukkan wani hukunci.
30- Ki yi shiru a duk lokacin da mijinki yake
yi miki fada ko Nasiha.
31- Kada ki zama Al-mubazzara mara tattali.
32- Kada ki tara kayan wanki da yawa a daki,
naki ko na mijinki suna wari.
33- Ki tanadi kayan kwalliyar gida bayan na
zuwa unguwa.
34- Ki kula da yanayin da zai nuna miki cewa
mijinki yana cikin Nishadi ko Damuwa.
35- Kada ki ringa baiwa kawayanki labarin
sirrin dake tsakaninki da mijinki.
36- Idan zaki yiwa mijinki magana kiyi masa
da tattaunsan harshe, da murya mai karya
zukata.
38- Ki zama kin iya kallo mai nuna alamun
sha'awa ko soyayya.
39- Idan kika samu sabani da mijinki ki bashi
hakuri ko da kuwa kece da gaskiya.
40- Ki zama mai tattali a cikin dukkan abinda
kika mallaka a gidan mijinki.
41- Kada ki zama mai kwauron baiwa dangin
mijinki abinda ya umarceki da a basu.
42- Kada ki zama mai yin dare wajan girki.
43- Kada ki zama uwar adashi ba tare da
sanin mijinki ba.
44- kada ki zama mai yawan fada da
makwabtanki.
45- Kada ki kasance mai yawan zagi ko
Ashariya.
46- Kada ki ringa baiwa Iyayanki Labarin
laifin da mijinki yake miki.
47- Ki zama mai hakuri da juriya da halayyar
Iyayan mijinki da 'yan uwansa.
48- Idan mijinki ya yi miki laifi kada ki nuna
masa bacin ranki a gaban iyayanki ko 'yan
uwansa.
49- Kada ki ringa daga murya sama idan
kuna sa-in-sa da mijinki.
50- Kada ki ringa baiwa 'yan uwan mijinki
labarin laifukansa.
51- kada ki ci wani abu da mijinki baya son
warinsa misali tafarnufwa.
52- Ki dinga yiwa mahafiyar mijinki Ihsani da

Back to posts
Comments:
[2015-02-02 12:00:14] Aliyu Musa :

Masha Allah, Allah Yasaka Da Alkhairi

[2015-09-08 18:43:51] MAMAN AMIR :

Allah ya saka da alheri

[2015-12-19 06:15:09] Tambaya :

Dan Allah malam mene sunan littafinnan me raddi kan littafan shi'a wanda malam khamis almisriy ke gabatarwa a gidan radion nagarta???

[2016-08-30 05:28:58] Saifullahi adamu bawa dan musa :

Allah yasaka da alkeari yakuma sa muringa daukan shawarar da'ake bamu.

[2016-12-15 04:43:43] Samaila abdullahi mubi :

Mungode allah kare addininmu da malamanmu


UNDER MAINTENANCE

Share|

Kaima shiga a tattauna da kai
* No boards.

Online: Guests: 2


→Ra'ayin jama'a game damu

 IDAN KANA BUKATAR A TALLATA MAKA HAJAR KA A WANNAN SHAFIN DA SAURAN SHAFUKAN MU KANA IYA TUNTUBAR MU TA WADANNAN HANYOYIN KAMAR HAKA:


Email: bjournalist55@hotmail.com

Phone No: 09035830253

Facebook: Basheer Journalist Sharfadi

Address: Ittihad Computer Centre,  No 92 Daneji Kano


MAI TALLA SHI KE DA RIBA


*Bayanan ka*
Browser din da ka hawo Mozilla

Kasar da kake

Adadin Maziyarta 508893

Adadin Wadanda Sukayi Comment 65691

A Wadanda Suka Shiga Tattaunawar Mu 54


Follow @bjournalist55
→Yi Adding Dina Ta Facebook
→Yi Like Na Dakarun Sunnah Page
→Yi Like Dina Ta Facebook

*Shafuka Masu Alaka Da Mu*

→Basheer Sharfadi wordpress
Basheer Sharfadi Blog Spot
UP
→Home

Basheer Journalist Sharfadi (Abu Hafsah)
ISLAMIC DATE
  • phpimg2.php?it&ic=yellow



  • Click to Sms
    Click to Call


    Basheer journalist sharfadi3
    Coollogo com-1281358