Old school Swatch Watches
Google69490f6862051cb8
google-site-verification: google69490f6862051cb8.htmlgoogle-site-verification: google69490f6862051cb8.htmlgoogle-site-verification: google69490f6862051cb8.htmlBasheer journalist sharfadi14

Basheer journalist sharfadi14.jpg6
Basheer journalist sharfadi 11 1
Maraba Da Zuwa Wannan
Shafi Mai Al-barka 1

☀ Zabi inda kake son shiga ☀
Menunks
→Home
→Akidojin Ahlussunnah
→Addinin musulunci (35)
→40 Hadith (50)
→Fadakarwa (120)
→Neman labarai (20)
→Shi'a Kafirci (50)
→Hadith (55)
→Khudubobi (24)
→Tarihin magabata (60)
→Raddi / Maida martani (99)
→Face book post (30)
→Monthly Archives (60)
→Tambaya da Amsa (20)
→Sahabban Annabi {s.aw} (50)
→Taskar maluman sunnah (25)
→Akidar Y'an Shi'a Dangane da Al'kur'ani
→Fassarar Usulussunnah (20)
→Sheik Ja'afar {Rahimahullah} (65)
→Sheik Abubakar Gumi {Rahimahullah} (30)
→Sheik Dr. Muhammad Sani R/Lemo
→Salafiyyah Network Nigeria (100)
→Adam Sani Abu-Umayrah (99)
→Salaf Ustaz (79)
→Malama Ummi Ahmad Katsina
→Malama Amina Saleh Mande
→Labarai (40)
→Nishadantarwa (10)
→Siyasar Nigeria (9)
→Vidio (33)
→Audio (66)
→Hotuna (120)
→Internet Cheat (90)
→Site Achieve
→Application (10)
→Games (8)
→About me (01)

Wannan shafin mallakarCoollogo com-1281358 3
Ne




SHAFI DON KARUWAR MUSULMI
**WA YA KASHE HUSSAIN r.a??**
(1)

Assalamu alaikum, Kamar yanda muke ganin masu da'awar qaunar Ahlul Baiti r.a suna nuna baqin ciki a watan Al-Muharram bisa Kisan Imam Hussain Bin Ali r.a, yanada kyau mu waiwaya baya mu dubi Tarihi, mugani kuma mu Gane, SUWAYE SUKA KASHE IMAM HUSSAIN r.a, domin ana wasa da qwaqwalwar jama'a ana hada tatsunuyoyi gameda kisan Hussain r.a, don Haka zamu koma baya kadan tun daga tushen Wutar, Qissar da kanta zata fada mana suwayen sukai kisan, sannan Ahlul-Baitin dakansu zasu tabbatar mana da La'anannunda suka kashe Hussain r.a:

"Bayanda Akaiwa Yazid bin Mu'awiyah r.a Mubaya'a bisa shugabancin Musulmai, a shekara ta 60 bayan Hijirah, yana dan shekaru 34, amma da Abdullahi bn Zubair da Imam Hussain r.a basuyi masa Mubaya'a ba, bayan dukkansu suna Madinah ne!

Sai ya tura wajen Abdullahi bin Zubair akan yayi Mubaya'a, sai yace: "Ku jira dare yayi sai na fada maku ra'ayina", sanda dare yayi, sai ya fice daga Madinah ya gudu zuwa Makkah, bai yi Mubaaya'a ba!

Sai ya Aika wajen Hussain bn Ali r.a akan yayi masa Mubaya'a, sai Imam Hussain yace: "Bazanyi Mubaya'a ba a asirce, zanyi mubaya'a ne a idon mutane" sai suka Amince, bayanda dare yayi, sai yabi bayan Abdullahi bn Zubair r.a ya gudu zuwa Makkah.

Labari ya isarwa mutanen Iraaq cewar: Hussain r.a baiyi mubaya'a wa Yazid r.a ba, sai suka dinga turo masa wasiqu akan yazo su masa Mubaya'a, domin basu son Yazid r.a, kai hatta Mu'awiyah r.a basu sonsa, su Imam Ali r.a da Yaransa suke so! Suka dinga turo masa Wasiqu akan:

"Mun maka mubaya'a, Bamusan kowa baicinka, Yazid baida mubaya'a akanmu, mubaya'armu tana gareka"!

Suka dinga turo wasiqu, abu yayi yawa, har takaiga sun Turowa Imam Hussain r.a wasiqu kusan 500, dukkanta daga Mutanen Kufah suka iso!.

Da haka suka Yaudari Imam Hussain r.a, suka rudeshi suka Ha'inceshi! Domin iraqi (Kufah da Basrah) garine mai hauragiya da hayaniya, garine dake cike da tunbotsai! Duk wata fitina dake tasowa a duniyar Musulunci, Iraqice tushenta, ko kasamu tanada hannu ciki!

Bayanda Imam Hussain r.a yaga abun yayi yawa, sai ya Tura dan'uwansa Muslim bn Aqiyl bn Abi-Talib r.a, domin ya binciko gaskiyar Labari, ya kuma ga haqiqanin abinda ke wakana, shin wannan takardu gaskiya ne?

Sai Muslim bn Aqiyl r.a ya shirya ya kama Hanyar zuwa Iraqi domin cika Umarninda Hussain r.a ya bashi!

**Abinda zamu amfana dashi a wannan gajeren rubutu shine:

1: Yan-Iraqi sune suka rubutowa Hussain r.a wasiqa suka gaiyace shi.
2: Yan-Iraqi masoyan Imam Ali ne da kuma Ahlul Baiti r.a.

Anan zanci Birki, sai Allah ya kaimu Gobe zamuji ya ta kaya da Muslim bn Aqiyl bayanda ya isa Iraqi, meya faru?



** WA YA KASHE HUSSAIN r.a???**(2)

Assalamu alaikum wr, Yan uwa kada ku mance, wannan bayani da na dauko, nayi hakane da zimmar tabbatar da Amsar wannan Tambaya, ta Hanyar tarihi da kuma su Ahlul-Baiti din r.a!

A jiya, nayi bayani kan Yanda Yan-Shi'ar Kufah, Mabiya Imam Ali da Ahalinsa r.a suka dinga turo wasiqu ga Imam Hussain r.a da Mubaya'a da suka dinga masa, gamida kira da Gaiyatarsa garesu da sukai tayi! To sai Hussain r.a ya tura dan'uwansa Muslim bn Aqiyl don ya dubo gaskiyar labarin, zan ci gaba yau da yardar Allah:

"Bayanda Muslim bn Aqiyl ya isa zuwa kufa, sai ya dinga tambayan mutane yana bugun cikinsu, har ya tabbatar da cewa lallai Mutanen kufah babu wanda sukeso bayan Hussain bn Ali r.a, sai ya sauka wajen Haani'I bn Urwah, mutane suka dinga zuwa, jama'a jama'a da dai-daiku, suna yiwa Muslim bn Aqiyl mubaya'ar Hussain r.a.

A Hannu daya kuma: Nu'uman bn Bashiyr shine shugaban Kufah kamar yanda Yazid bn Mu'awiyah r.a ya nada shi, sanda ya samu labarin Muslim bn Aqiyl ya iso kufah kuma mutane suna zuwa sunai masa mubaya'ar Hussain r.a, sai yayi kamar baisan komai ba, yaqi nuna wani abu, har wasu daga wajensa suka fita zuwa wajen Yazid a sham suka bashi labarin abinda ke faruwa a kufah, kuma Muslim mutane na can na masa Mubaya'a, kuma Nu'uman be damu da wannan abu ba!

A wannan Lokacine Yazid ya cire Nu'uman bn Bashir daga shugabancin Kufah, sai ya Turo Ubaidullah bn Ziyad a matsayin sabon shugaban Kufah, bayan ada ya kasance shugaba ne a Basrah, Sai aka Hada masa da Kufa ta dawo qarqashinsa, domin ya warware wannan Mas'alar.
Sai Ubaidullah bn Ziyad ya iso Kufah cikin dare, ya rufe fuskarsa, duk inda ya hadu da mutane sai ya musu sallama, suna amsawa suna cewa: "Wa'alaikumussalaam ya dan diyar Manzon Allah s.a.w" suna zaton cewa Hussain r.a ne, daga nan ya wuce Faada, sai ya tura Bawansa mai suna Ma'aqil domin ya binciki lamarin cikin gari, kuma ya gano waye babba cikin wannan lamari.

Sai wannan Bawa ya tafi a matsayin wani Mutum daga HIMS, kuma yazo da Diynari 3000 don bayardasu ga Hussain r.a, ya dinga Tambaya har aka nuna masa gidan Hani'I bn Urwah, sai ya shiga, ya samu Muslim bn Aqiyl a ciki, sai ya masa Mubaaya'a kuma ya bashi Diynari 3000 dinnan, ya dinga kai-komo wajensu har ya tabbatar da lamarin, daga nan ya koma wajen Ubaidullah ya bashi labari!

Bayan komai yayi daidai, mutane da yawa sukai mubaya'a wa Hussain r.a ta Hanyar Muslim bn Aqiyl, sai ya tura wa Hussain r.a akan YAZO, domin Lamari ya kankama, Sai Hussain r.a ya fito ya nufo Kufah! Ubaidullah bn Ziyaad yasan abinda Muslim bn Aqiyl ya aikata! Sai ya tura akawo masa Haani'I bn Urwah, sai akazo dashi"

Me zai faru bayan zuwan Urwah bn Haani'I faadar Ubaidullah?

Ya Batun Tasowar Imam Hussain r.a? Me zai faru a Hanya?

Shi kuma Muslim bn Aqiyl ya zata kaaya dashi?

Ya batun Yan shi'ar Imam Ali r.a na Kufah, me zasuyiwa Hussain r.a bayan isowarsa?

Sai ku biyoni a rubutu na gaba da izinin Allah don jin wadannan Amsoshin!

Wassalamu alaikum.



**WA YA KASHE HUSSAIN r.a??**(3)

Assalamu alaikum, a rubutuna da ya gabata, munji yanda ta kaya bayan Zuwan Muslim bn Aqiyl kufah, kuma munji Ubaidullah bn Ziyaad ya tura akawo masa Hani'I bn Urwah bayan ya tura bawansa ya gano sirrin, sai yasa akawo masa Hani'I bn Urwah, to yau zamuji abinda ya wakana:

"Bayanda aka kawo Hani'I bin Urwah, sai (Ubaidullah) ya tambayeshi: Ina Muslim bn Aqiyl? Sai yace: Ban sani ba!
Sai Ubaidullah ya kira bawannan nasa Ma'aqal yazo, sai yacewa bawansa: Kasan wannan? Sai yace: Eh, sai Hani'I ya fadi, yasan cewa an shirya masa yaudarane (zuwan wannan bawa da yayi) daga Ubaidullah, sai Ubaidullah bn Ziyaad yace masa: Ina Muslim bn Aqiyl? Sai yace: 'Na rantse da Allah, da ace ya kasance a qasan qafata da bazan dagata ba, sai Ubaidullah ya doke shi, yayi Umarni da a tsareshi.

Labarin abinda ya faru ya ishi Muslim bn Aqiyl, sai ya fito da rundunar mutane 4000, ya tsare Gidan sarautar Ubaidullah, mutanen Kufah suka fito tare dashi, a wannan lokacin, manyan mutane na wajen Ubaidullah, sai yace dasu: Ku kawar da mutane daga Muslim bn Aqiyl, kuma ya alqauranta masu kyaututtuka da kuma tsoratar dasu Rundunonin Shaam!

Sai shuwagabanni suka dinga kauda mutane daga Muslim bn Aqiyl, sai Uwa tazo ta janye danta, Uba yajanye dansa, wa ya janye qaninsa! Har saida ya zamana babu wanda ya rage taredashi baicin Mutane 30 daga cikin 4000!!!!

Rana bata fadiba sai ga Muslim bn Aqiyl shi daya Qwallin-qwal, dukkan mutane sun gudu daga gareshi, ya rage shi kadai yana yawo a unguwannin kufah, baisan inda zai tafi ba, sai ya bugawa wata mata qofa yar qabilar Kindah, yace: Inason ruwa ne, sai ta nuna bata sanshi ba, tace: waye kai? Yace: Nine Muslim bn Aqiyl, yabata labarin abinda ya faru, kuma mutane sun wulaqanta shi, kuma Hussain zai taho domin yace masa ya iso, sai tashigar dashi gidanta bisa kulawarta, tazomasa da abinci da ruwa!

Amma sai dai kash....... Danta ya je ya baiwa Ubaidullah labarin inda Muslim yake, sai ya tura mutane 70 su kamo shi, sukai kashe-kashe, aqarshe dai ya miqa wuya bayan sun amintar dashi, aka kaishi Gidan sarauta inda Ubaidullah ke ciki, sanda aka kawoshi, sai ya Tambayeshi:

Menene dalilin fitowarsa Kufah? Sai yace: Mubaya'ar dake wuyarmu ta Hussain bn Ali ce, sai yace: Ashe babu Mubaya'ar Yazid a wuyarka? Lallai zan kashe ka, sai Muslim yace: Barni nayi wasiya, sai yace: eh, yi wasiyar.
Sai ya waiga, sai yaga Umar bn Sa'ad bn Abi-waqqaas, sai yace dashi: Kaine mafi kusancin mutane dangantaka dani, zo nai maka wasiyyah, sai ya jashi gefen gidan, ya masa wasiyar: Ya turawa Hussain ya koma. Sai Umar bn Sa'ad ya tura wani mutum zuwa Hussain don ya fada masa cewa Al'amari ya qare,

KUMA MUTANEN KUFAH SUN YAUDARESHI!

Sai Muslim ya fadi Shahararriyar Kalmarssa:

"KA KOMA DA IYALANKA, KADA MUTANEN KUFAH SU RUDEKA, DOMIN MUTANEN KUFAH SUN QARYATAKA SUN QARYATANI, KUMA MAQARYACI BAIDA RA'AYI".

An kashe Muslim bn Aqiyl a ranar Arafah, Shi kuma Hussain ya fito daga Makkah ranar Tarwiyah kafin Kisan Muslim da kwana 1!

(Innaalillaahi wa innaa ilaihi raaji'in)!"

Abinda ya faru kenan da Muslim bn Aqiyl Allah ya masa Rahmah, yanzu a rubutu na gaba zamuji fitowar Hussain zuwa Kufah,

bayan ya samu labarin abinda ya faru da Muslim bn Aqiyl dan'uwansa!

Duk mai son ganin wannan qissah a sauqaqe sai yaje ya duba:

HIQBATUN MINAT-TARIYKH na Usman bn Muhammadul Khamiys! Wannan Qissah na shafi na 142-143 ne!

Sai mun hadu a rubutu na gaba in Allah ya nufa!

Wassalamu Alaikum.



**WA YA KASHE HUSSAIN?**(4)

Assalamu Alaikum, Yan'uwa barkanmu da saduwa awannan lokaci, a rubutunda ya Gabata munji yanda Aka Kashe Muslim bn Aqiyl r.a, da kuma aikewa da yayi wa Hussain r.a akan kada yazo Iraqi, ya komai kawai Munafuqai ne!

Yau da Yardan Allah zamuji yanda ta kasance:

"Sahabbai da dama sunyiwa Hussain r.a inkarin Fita zuwa Kufah, akan ya haqura da lamarinsu, kamar su: Abdullahi bn Umar r.a, Abdullahi bn Abbas r.a, Abdullahi bn Amru bnl Aas, Abu-Sa'I'd Al-khudriy, Abdullahi bn Zubair r.a da kuma dan Uwan Hussain r.a din Muhammad bn Hanafiyyah! Dukkansu sun Haneshi da zuwa kufa sanda sukaga himmatuwarsa na tafiya Iraaq (kufah), Amma Hussain r.a yaqi Karban Shawarar su, ya tafi zuwa Kufah. (Albidaayah wannihaayah: 8/161-168).

Bayanda Wasiqar Muslim bn Aqiyl da labarin kisansa ya isowa Hussain r.a, sai Yayi nufin juyawa ya koma Madina, amma sai Yan'Uwan Muslim (Aali Aqiyl) sukace lallai bazasu koma ba har sai sun dauki Fansar Muslim!

Imam Hussain r.a sai ya ci gaba da tafiyarsa zuwa Iraqi ya dauki Ra'ayin Aali-Aqiyl!

Sanda Ubaidullah bn ziuyad ya ji labarin Tahowar Hussain r.a sai ya tura Hur bn Yaziyd Attamiymiy da runduna ta mutum 1000 don su hadu da Hussain r.a a hanya, sai ya Hadu da Hussain r.a a kusa da Qadisiyyah.

Hurr yace da Hussain r.a: Ina zuwa ya dan Diyar Manzon Allah s.a.w?
Hussain: Iraaq.
Hurr: Lallai ina Umartarka da ka koma, kada Allah ya Jarabceni dakai, ka koma inda ka fito, ka ka tafi Shaam wajen Yaziyd, amma kada ka je Kufah!
Sai Hussain r.a yaqi yarda da hakan, sai ya dinga bin Hanyar Iraaq, shi kuma Hurr yadinga Tareshi yana Hanashi, sai Hussain yace dashi: Ka tafi ka bani wuri (Uwarka tayi asararka).
Sai Hurr bn Yaziyd yace: Na rantse da Allah, da waninka ne ya fadi haka gareni cikin Larabawa, da na Dau Fansa akansa da kan Mahaifiyarsa, sai dai mezance bayan Mahaifiyarka itace shugabar Matan Duniya!!!.

Hussain Ya iso KARBALA sai ya tambaya: Ya sunan wannan Wurin? Akace KARBALA, sai Yace: KARB (Baqinciki) BALAA'U (Balaa'I) kenan!

Bayan Rundunar Umar bn Sa'ad ta iso, sai yawa Hussain Magana akan ya Taho tare dashi zuwa iraq wajen Ubaidullah bn Ziyaad, sai Yaqi.

Sanda Hussain r.a yaga cewa Lallai lamarin megirma ne, sai yacewa Umar bn Sa'ad: Zan baka Zabi guda 3, ka zabi wacce kaso, sai Umar yace: menene su?, Hussain r.a yace:

1: Ka qyaleni na koma.
2: Ko kabarni in tafi wani gari daga garuruwan Musulmai.
3: Ko in Tafi wajen Yazid in samasa hannu a hannunsa (mubaya'a)!

Sai Umar bn Sa'ad yace: Kai ka aika wajen Yazid, ni kuma zan Aika wajen Ubaidullah bn ziyad, sai ya duba yanda lamarin zai kasance!
Amma Hussain be aikewa Yazid ba, shi kuma Umar bn Sa'ad ya aikewa Ubaidullah bn Ziyaad".

(Hiqbatun-Minattaari­ykh: 143-146).

A rubutu na gaba zamuji Yanda ta kasance bayan isan saqo ga Ubaidullah! Amma fa kada mu mance, Yazid har yanzu baida Masaniya akan halinda ake ciki, kuma Hussain be aika masa saqo ba!

Wassalamu alaikum.



**WA YA KASHE HUSSAIN r.a??**(5)

Assalamu alaikum, a rubutunda ya gabata, munji cewa Hussain r.a ya cimma Yarjejeniya da Umar bn Sa'ad (Commandan Ubaidullah) akan cewa: Shi Hussain zai je yayiwa Yazid Mubaya'a, zai tura dan saqo yaje ya fadawa Yazid din!

Sannan shi kuma Umar bn Sa'ad ya aikewa Ubaidullah da dan Aike bisa wannan Yarjejeniya! Sai shi Hussain yaqi ya Tura dan aike, shi kuma Umar ya tura nasa,

To zamuji yanda abin ya kasance:

"Sanda Dan Aike yajewa Ubaidullah bn Ziyaad, kuma ya bashi labarin abinda ya faru, kuma Hussain r.a yace:

'Ina baku zabi tsakanin abubuwa 3 (sai ya fada masa su), sai Ubaidullah yace ya Yarda da dukkan sharuddan, Hussain r.a yazabi duk wacce yaso, shi ya Yarda kawai!

To sai dai a wajen Ubaidullah akwai wani mutum da ake kira Shamr bn Zil-Jaushan, ya kasance cikin Manyan Makusanta ga Ibn Ziyaad, sai (Shi Shamr) din yace: A'a wallahi, dole sai ya sakko kan Umarninka, sai Ubaidullah ya karbi maganar sa, yace be yarda ba, dole sai Hussain r.a ya Karbi Hukuncina!

Sai Ubaidullah ya shirya aika Shamr bn Zil-jaushan, yace: Kaje (kada ka barshi) har sai ya sakko kan Hukuncina, idan Umar bn Sa'ad ya yarda da wannan Umarni shikenan, idan yaqi to kai ka Karbi jagorancin Rundunar!

Sai Shamr bn Zil-Jaushan ya fito, Labari kuma ya iso zuwa Hussain r.a, kuma lallai ba makawa dole ya sakko kan lamarin Ubaidullah bn Ziyaad, sai yace: Beyarda ba yace:

A'a wallahi, Bazan taba sauka akan hukuncin Ubaidullah ba har Abada!!!

Wadanda suke tareda Hussain r.a Mahaya doki 72, Rundunar Kufah kuma 5000 ne, sanda Rundunonin 2 suka tsaya, sai Hussain r.a yacewa Rundunar Kufah: "Ku bibiyi kawunanku ku lissafa, Shin kisan kamata ya dace daku? Alhali nine dan Diyar Annabinku, kuma akaf ban Qasa, babu wani dan Diyar Annabi baicina, kuma Haqiqa Annabi s.a.w yace min da dan'uwana: "Wadannan 2n sune shuwagabannin Matasan Aljannah"!

Ya dinga zaburar dasu bisa barin Umarnin Ibn Ziyaad da kuma hadewa da Rundunarsa, sai Mutane 30 cikinsu suka dawo rundunar Hussain r.a, daga cikinsu akwai Hur bn Yaziyd Attamiymiy wanda ya kasance Comanda ne na rundunar farko ta Ubaidullah, sai aka ce dashi: kai kazo tare da mu shugaban runduna, amma Yanzu ka koma wajen Hussain?

Sai Yace: kaiconku! Wallahi ana bani tsakanin Aljannah ne da Wuta, Wallahi bazan taba zaban Wutaba, koda an yayyankanine an qonani!

Bayan haka, Hussain r.a Yayi sallar Azahar da La'asar a ranar Alhamis, shine ya jagoranci sallar, wacce dukka rundunar Ubaidullah da ta Hussain din suka bishi sallar.

Sanda Magriba ta gabato, sai (Rundunar Ubaidullah) suka gabato da dawakansu wajen Hussain, Hussain r.a yakasance tareda Takobinsa, yadanyi barci kadan, sanda ya gansu, sai yace: meye wannan? Sai akace: sune suka gabato, sai yace: kuje wajensu ku masu magana, ku tambayesu me suke so?

Sai mahaya dawakai 20 sukaje, cikinsu akwai Abbas bn Aliyu bn Abiy Talib, dan Uwan-Hussain, sai Sukai masu magana suka tambayesu: Me sukeso? Sai sukace: Kodai ya sauka kan Umarnin Ubaidullah, ko ayi Yaqi!
Sai sukace: Har sai mun fadawa Aba-Abdullah (Kuniyar Imam Hussain r.a kenan), sai suka koma wajen Hussain r.a suka fada masa, sai yace: Kuce masu su mana jinkiri a wannan daren har nayi sallah ga Ubangijina, gobe ma basu labari, domin inason inyi sallah ga Ubangijina t.a, sai Hussain r.a ya kwashe darensa gaba daya yana sallah ga Allah t.a, yana Istigfaari yana roqon Allah, shida wadanda yake taredasu r.a!

*References: Al-Bidaayah wannihaayah, Hiqbatun-Minattaariy­kh.

A rubutu na gaba zamuji yanda ta wakana bayan wayewar Gari!

Wassalamu alaikum.



**WA YA KASHE HUSSAIN R.A?**(6)

Assalamu alaikum wr, A jiya mun tsaya inda Rundunar Shamr Bn Ziljaushan, wacce Ubaidullah yaturo don yaqar Hussain r.a ta dunfaro su, sannan Hussain r.a ya nemi afuwa zuwa safiya domin yanaso ya gana da Ubangijinsa,

Haka Hussain Ya Kwana sallah da Roqon Allah, shida wadanda ke tare dashi! To yau zamuji abinda ya faru bayan wayewar Garin Jumu'ah:

"A safiyar Ranar Jumu'ah, yaqi ya kaure tsakanin bangarorin biyu, bayanda Hussain r.a yaqi yarda a tafi dashi wajen Ubaidullah a matsayin kaamamme, sai dai bangarorin 2 bazasui daidai ba,

Rundunar Hussain r.a sukaga lallai ba yanda zasuyi da wadannan, ahaka suka dinga Mutuwa gaban Hussain r.a daya bayan daya, har suka qare, ba wanda yayi saura cikinsu baicin Hussain r.a da Dansa Aliyu bn Hussain wanda bashida lafiya a wannan lokacin, haka Hussain r.a yayi yammaci ba wanda ya tunkaroshi, duk wanda ya matso sai ya juya gudun kada ya zama shine ya kashe Hussain r.a, har saida Shamr bn Ziljaushan yazo, sai yayiwa mutane Tsaaawa! Kaicon ku, Uwayenku sunyi hasararku, ku diran masa ku kasheshi! Sai sukazo suka tsare Hussain bn Ali r.a, sai Hussain r.a yadinga kutsawa Tsaksaninsu yana kashesu, har ya kashe adadi me yawa, domin yakasance kaman ZAKI ne, sai dai kash, Yawa ta rinjayi Jarumta!

Shamr ya musu tsaawa: Kaiconku! Me kuke jira???? Ku isa!!!! Sai suka isa ga Hussain r.a Suka Kasheshi!

INNAALILLAAHI WA INNAA ILAIHI RAAJI'UN!!!

Wanda ya Kashe Hussain r.a shine: SINAAN bn ANAS AN-NAKHA'IY, sai ya guntule kan Hussain daga Jikinsa! Wasu sukace SHAMR bn ZIL-JAUSHAN ne! Allah Ya La'ancesu!!!!

Bayan kashe Hussain r.a, sai aka dauki Kansa aka kai Kufah wajen Ubaidullah bn Ziyaad, sai ya dinga zungurinsa da sandarsa yana sanyata a bakinsa a wushiryarsa! Yakasance Hussain r.a yanada Wushirya kyakkyawa! Sai Anas bn Malik ya miqe yace: (Wallahi Ba lalatacce kamanka, haqiqa naga Manzon Allah s.a.w yana sumbatan wurinnan da kakesanya sandarka)!

WADANDA AKA KASHE TAREDA HUSSAIN r.a daga Iyalan gidansa:

-DAGA YAYAN ALIYU BN ABI TAALIB: Hussain r.a, Ja'afar, Abbaas, Abubakar, Muhammad da Uthmaan.

-DAGA YAYAN HUSSAIN: Abdullah, Aliyul-Akbar!

-DAGA YAYAN HASSAN: Abdullah, Alqaasim, Abubakr.

-DAGA YAYAN AQIYL: Ja'afar, Abdullah, Abdur-Rahman, Abullah bn Muslim bn Aqiyl, sai Muslim bn Aqiyl da aka kashe tun Farko a Kufah!

Sai Aun da Muhammad daga cikin Yaran Abdullahi bn Ja'afar!

A Jumlace Mutane 18 duk daga cikin Iyalan Gidan Manzon Allah s.a.w aka kashe a wannan Yaqi na Zalunci INNAALILLAAHI WA INNAA ILAIHI RAAJI'UN!

Akwai Abubuwa da dama da ake fadi gameda Kisan Hussain r.a, wanda ba Shakka ZUQl TAMALLO ce! Daga ciki akwai cewa wai anga sama tana Ruwan jini, bango ko ina ya cika da jini, ba dutsenda za'a daga face anga Jini, ko duk abinda aka yanka sai yazama jini gaba dayansa dasauransu, wannan ba shakka tsabar Qaryace, ba wata riwaya ingantacciya da ta tabbatar da haka!

Sai dai Ya tabbata cewa: Ummu salmah taji Kukan Aljanu sanda aka kashe Hussain r.a! (Fadaa'ilus-sahaabah­: 2/766 hadisi 1373).

Kuma ya Tabbata cewa Ibn Abbas yaga Manzon Allah s.a.w a Mafarki Yayi Gizo yayi Qura, yana dauke da wata Kwalba dauke da jini, yace Jinin hussain ne da wadanda Aka kashe taredashi! (Fadaa'ilus-sahaabah­: 1380).

wannan kenan a taqaice gameda KISAN HUSSAIN r.a! Kana iya duba:

(Hiqbatun Minat-tariyk, Albidaayah wannihaayah),

Abinda zamu dauka na Darasi anan shine:

1: Yazid bn Mu'awiyah r.a bashine ya kashe Hussain ba, ba shine yabada Umarnin kisan Hussain ba! Sannan ba'a kai masa kan Hussain r.a ba! Babu wata riwaya ingantacciya da tazo da wadannan qarairayi!

2: Ubaidullah bn Ziyaad L.A shine yabada Umarnin Kisan Hussain r.a, qarqashin Shamr bn Zil-Jaushan, sannan Sinan bn Anas An-nakha'iy Allah ya la'ancesu baki daya!

A rubutuna na 7: Zan tabo Zahirin Makasan Hussain r.a! Wannan na kawo Labarin ne a dunqule! Kuma zan kawo shawahid ne daga Littafan Masu baqaqen Zukata (Shi'a)! A qarshe kuma in kawo Matsayata akan Yazid bn Mu'ayiwah, da kuma Matsayar Malaman Ahlus-sunnah gameda shi!

Wassalamu alaikum wr.



**WA YA KASHE HUSSAIN?**(7)

Assalamu alaikum, Bayan jin yanda ta kasance a kisan Hussain bn Ali r.a!

Mun fahimci cewar Yazid bin Mu'awiyah beda Hannu a kisan Hussain r.a, kuma be bayarda Umarnin Kisan Hussain r.a ba!

Hakan baya Nufin Mun wanke Yazid, ko kadan ba haka bane, wallahi iya gaskiyar da na sani kenan!

Mutanen Kufah sune suka kashe Hussain r.a da Ahalinsa! Sannan YAN SHI'ARSA da SHI'AR MAHAIFINSA sune suka kasheshi!

Ba ni na fadi ba, Malaman Shi'ah ne!

Yanada kyau Musani Mutanen Iraaq (Kufah) Shi'ar Imam Ali ne r.a, sai dai basuda biyayya da daa'a, sai dai Imam Ali r.a yayi Allah wadai dasu! Kai Har cewa Imam Ali r.a MAQARYACI SUKAI!!! (Nahjul Balaagah: 1/187-189. 118-119).

*IMAM HASSAN bn Ali r.a na cewa:

(Wallahi mu'awiyah ya fiminku Alheri, suna kiran su Shi'ah ta ne, sun nemi kasheni, sun keta mutuncina, sun dibi dukiyata, wallahi inda ace Mu'awiyah zai qulla alqawarin kare jinina, da amintar da ni cikin iyalina, wannan yafi min Alheri da su yaqeni! Sai Ahalina sun wulaqanta da ya iyalaina, da ace na Yaqi Mu'awiyah, DASUN KAMA WUYATA SUN MIQANI GUNSA).

(Annadwah:3/308, Fi-rihaabi Ahlil-Bayt: 270).

Wannan zai fitomana da Zahirin Shi'a, Munafuqaine, Basuda Maraba Da Yahudawa! Musamman na Israa'ila!

Haqiqa Muhammad bn Ali bn Abi Talib (ibn Hanafiyyah), ya Hana Hussain r.a zuwa Iraqi yace masa:

(Ya kai Dan-Uwana, haqiqa kasan cin amanar mutanen Kufah ga mahaifinka da dan'uwanka (Hassan r.a), ina Ji maka tsoron kazamo kamar su (Mahaifinka da Hassan r.a, kaima su kasheka).) (Ku duba: Alluhuwf:39, Ashuraa:115, Majaalisul Fakhirah: 75).

Mawaqinnan FARAZDAQ ya cewa Hussain r.a sanda yaganshi zai tafi wajen Shi'arsa na Iraqi: (Zukatansu na tare da kai, Takubbansu na kanka -sunason kasheka-) -Majaalisul Fakhirah:79, Al-waa'ijul Ashjaan:60-.

Yasa zamuga Hussain r.a sanda yaje Kufah da yaga cewar lallai suna shirin Ha'intarsa a Khutubarsa yake cewa: (Idan har bakuyi (min mubaya'a) ba kuma kuka warware alqawarinku, kuma kuka cire mubaya'ata daga wuyarku, Wallahi wannan ba baqon Abubane gameda ku! Haqiqa kun aikata hakan ga Mahaifina da dan'uwana (Hassan) da kuma dan Ammina Muslim!

RUDADDE SHINE WANDA YA RUDU DAKU!)

*ku duba: Ma'aalimul-madrasata­in:3-71-72, Ma'aalis-sibtain:1/­375, Bahrul Uluwm: 194).

Kunji Khutbar Hussain a Kufah!

*Aliyu Zaynul Aabidiyn na cewa yana mai wofintar da Shi'arsu wadanda suka Qasqantar da Babansa suka kasheshi: (Ya ku Mutane, ina hadaku da Allah, shin kunsan kune kuka rubutawa Babana wasiqa kuka yaudareshi, kuka bashi Alqawari da mubaya'a kuma kuka kasheshi kuka qasqantar dashi, TIR dsa abinda kuka aikatawa kanku, tir da munin ra'ayinku, da wani ido zaku Kalli Manzon Allah s.a.w sanda zaice muku: (Kun kashe tsatsona ku keta hurumina baku cikin Al-ummata)!

Sai wurin ya kaure da koke koke sunata ihu suna sun halaka sai sukace: (Mu dukkanmu masu sauraronkane masu kare mutuncinka, bamu gujewa daga gareka kuma bamu fifita wani akanka, ka Umarcemu da Umarninka! Mu masu yaqi ne da Yaqinka, kuma masu zaman lafiya da zaman lafiyarka! Zamu kama Yazid kuma wlh zamu barranta daga duk wanda ya zalunceka ya zaluncemu! Sai YACE: Har Abada makirai mayaudara, An iyakance tsakaninku da abinda kuke fata, kunaso kuzomin ne kamar yanda kuka zowa Babana a baya? A'a na Rantse da Ubangijin Taurari, ciwon haryanzo bai bar radadi ba, an kashe Babana jiya da iyalansa tareda shi, kuma Radadin Manzon Allah s.a.w da Mahaifina bai barni ba! Radadinsa na zuciyata, dacinsa na maqoshina da maqogorona!)

*Al-Malhuf:86, Maqtalul Hussain: 83, Nafsul Mahmum:357*

Yasanya duk sanda Zaynul Aabidin yaga Shi'ar Kufah suna Kukan Mutuwar Hussain r.a sai ya tsawatar musu yace: (Kuna Jimami kuna kuka a domin mu (ahlul-baiti), to waye ya kashemu in ba ku ba?) *Malhuf:91, Nafsul Mahmum:363*

Wannan ya ishi duk me hankali dason gaskiya! Zanci gaba a rubutu na 8!



**WA YA KASHE HUSSAIN?**(8)

Assalamu alaikum! Yan'uwa a rubutuna da ya gabata, na soma kawo maganganun Ahlul-Baiti kai tsaye daga Littafan shi'a, wadanda ke tabbatar da kasantuwar Shi'ar Imam Ali da Hassan sune makasan Hussain,

zan ci gaba ayau insha-Allah!

*Ummu Kulsum Bnt Aliy r.a Yar'uwar Hussain r.a tana cewa:

'Yaku Mutanen Kufah Tir daku! Meyasa kuka wulaqanta Hussain kuka kasheshi, kuka turmusa dukiyarsa kuka gajeta, kuka kama matansa, kuka wulaqantashi, tir daku Allah wadaranku, wace ruduce ta rudeku, kuma wani irin zunubine a bayanku kuka dauka? Wani jinine kuka zubar?

(Al-Malhuf:91, Nafsul Mahmum: 363).

*Zainab bnt Ali r.a tana cewa alokacinda taron Shi'arsu suka tareta da kuka: (kuna kuka ne kuna baqinciki? Tabbas wallahi, kuyi kuka dayawa kuma kuyi dariya kadan)

(Ma'al hussain fi nahdatihi:295).

MALAMAN SHI'A DA SUKA TABBATAR DACEWA LALLAI SHI'A ne ta kahe Hussain r.a:

1: JAWWADU MUHADDISIY: yace: (Dukkan wadannan sabubba sunkaiga Imam Ali ya dandani Daci 2 daga garesu, Imam Hassan ya fuskanci Yaudara daga garesu, an kashe Muslim bn Aqil bisa zalunci agabansu, An kashe Hussain r.a yana cikin Qishi a Karbala kusada Kufah a hannun Rundunar Kufah).

-Mausu'atul Aashuraa: 59-.

2: HUSSAINUL KURAANI: (Mutanen Kufah basu tsaya ga rabu da Hussain ba kadai, sai dai sun juya zuwa matsayi na 3, shine suka dinga fitowa karbala, suka yaqi Imam Hussain a.s, akarbala suka dinga shirya abindake faranta ran shedan, yake Fusata Allah)

-Fi rihaabi Karbala:60-61-

Ya sake cewa: Kuma zamu samu matsayi na daban dake nuna Munafurcin Mutanen Kufah,

Abdullahi bn Huzah attamiymi yazo gaban Imam Hussain yana ihu yana cewa: cikinku akwai Hussain? Wannan fa Abdullahi yana cikin mutanen Kufah, kuma yana cikin Shi'ar Imam Ali a.s a jiya, kuma tana yiwuwa yana cikin wadanda suka rubutawa Imam wasiqa, sannan yake cewa: Ya hussain kayi bushara da wuta)

-Fi rihaabi karbala:61-

3: MURTADAA MUTAHHARIY: (Babu kokonto cewa Kufah Shi'ar Imam Ali ce, kuma lallai wadanda suka kashe Imam Hussain Shi'arsa ce)

-Fi rihaabi karbala:61-.

Ya sake cewa: (don haka mu mun tabbatar da cewa wannan qissa me muhimmanci ce ta wannan fuska, kuma munce: Kisan Hussain a.s yakasance a hannun Musulmai ne, kai a hannun Shi'arsa ma bayan shekaru 50 da rasuwar Annabi s.a.w kawai, wannan lamarine me ban mamaki)

-Malhamatul Husainiyyah:3/94-.

4: KAAZIMUL IHSAA'IY ANNAJAFIY: (Rundunar da tazo yaqar Imam Hussain 300000 ce, dukkansu mutanen kufah ne, ba dan Sham cikinsu balle hijaaz balle Indiya balle pakistan balle sudan balle misra balle dan Africa, dukkansu yan kufah ne, sun hadu daga qabilu daban-daban).

-Aashuraa:89-.

5: HUSSAIN BN AHMAD ALBARRAAQIY ANNAJAFIY: (Qazwiyni yace: daga cikin abinda aka kama Mutanen kufah dashi shine: Sun kashe Hassan bn Ali a.s, sun Kashe Hussain bn Ali a.s bayan sun kirashi)

-Tariykhul kufah:113-.

6: MUHSINUL AMIN: (sannan Mutanen Iraaq sukaiwa Hussain Mubaya'a mutum 20000 suka shirya masa ha'inci, suka fito akansa, mubaya'arsa na wuyarsu, sai suka kasheshi)

-A'ayaanush-shiy'ah:­1/26-.

WAYE YA KASHE HUSSAIN?????
Mutane 2 sune sukafi shahara bisa kisan Hussain:

1: SINAAN BN ANAS Annakha'iy!
2: SHAMR BN ZHILJAUSHAN!

Sai kuma wanda ya Assasa ya kuma Umarci kisansa:-

UBAIDULLAH Bn ZIYAAD!
Da SHAMR BN ZHIL JAUSHAN (wanda ya kashe Hussain r.a) da UBAIDULLAH bn ZIYAAD (wanda yabada Umarnin kisan Hussain) dukkansu Shi'ar Imam Ali r.a ne! Malaman Shi'a sun Tabbatar da hakan:

1: UBAIDULLAH BN ZIYAAD: AT-TUSIY ya ambaceshi cikin littafinsa na AR-RIJAAL kuma ya lissafashi cikin Sahabban Imam Ali r.a
(Rijaalut-Tusiy:54).

2: SHAMR BN ZHIL JAUSHAN: NAMAAZISH-SHAHRUWDIY­ yace gameda SHAMR: yakasance ranar SIFFIN cikin Rundunar Imam Ali a.s.
(Mustadrakaatu ilmu rijaalil Hadiys:4/220).

Don Haka ga gaskiya nan daga Bakin Malaman Shi'ah, SHI'AR AHLUL BAITI SUNE SUKA KASHE AHLUL BAITI! Ya Allah ka tsinewa wadanda Suka Kashe Hussain r.a da sauran Ahlul Baiti! Ya Allah kamar yanda suka Zubda jinin Ahlul Baiti, Allah kasanya su dinga zubar da jinai-nansu har tashin Qiyamah!



*Koma Saman Shafi*

→Labarai

HASSADA MUGUN CIWO, ANIYARKA TABI KA ABDULJABBAR KA SANI HALIFA QARIBULLAH YAFI KARFINKA,(Imam Aliyu Indabawa)

HASSADA MUGUN CIWO, ANIYARKA TABI KA ABDULJABBAR KA SANI HALIFA QARIBULLAH YAFI KARFINKA,(Imam Aliyu Indabawa)
.
Wannan da kuke gani shine Dr kalifa qaribullah nasiru kabara, wanda ya kasance shine halifan dariqar qadiriyya, kuma muna girmama shi saboda halayensa na kawaici da sanin ya kamata, sai Allah ya jarrabe shi da wani taqadarin kani wanda ya addabe shi da hassada kullum cikin zaginsa yakeyi yana kushe shi yana aibata shi,
.
Asali abinda yasa yake masa wannan hassadar shine saboda halifa qaribullahi Allah yayi masa ni'imomi da baiwarwaki wanda shi kanin nasa bashi dasu, yafi shi duk wani abu da ake so, ta bangaren daukaka, da Ilmi da 'yaya da kudi da magoya baya da manyan mutane Sarakuna, uwa uba kuma yana da hankali wanda shi kanin nasa yayi rashinsa,
.
Sannan ga mukamin Halifa da yake rike dashi wanda shine yafi komai kona masa zuciya da motsa masa hassada, saboda shi a tunaninsa ai shine yafi cancanta daya gaji mahaifinsa ya zama halifan qadiriya saboda tunaninsa wai yafi Qaribu Ilmi shine yasa ya dade yana zagin Halifa karibu yana cutar da shi ta ko'ina yana nuna hassadarsa gare shi, dayake dama hassada ga mai rabo taki ce, shi kuma halifa Qaribu kullum sai kara gaba yakeyi har wasu kashashen ma suna bashi lambar yabo ta girmamawa amman duk da haka har yanzu Abdun jabberun yaki ya gane,
.
Ku duba Ko A haife qaribu ya haifi Audujanbiri amman saboda tantiranci da rashin tarbiya babu irin zagin da bayayi masa akwai Lokacin Audu janbiri yace,"qaribu wai babarsa da cikinsa ta shigo gidan malam wai qaribu ba dan malam bane wai shege ne kuma a duba dashi qaribun dashi Audu janbirin waye yake kama da malam kabara, kuma wai a cikin taron daruruwan mutane yayi wannan maganar, ba wannan kadai ba da dai sauran maganganu masu muni wanda shi kuma qaribun dayake yasan kanin nasa yana da ragaggen hankali baya biye ta tashi kullum hakuri yake dashi, lokacin da magoya bayan qaribu suka ga abin nasa fa ya wuce tunani ya koma tsantsar iskanci da rashin mutunci sai sukace suma dai dai suke da dan iska, inda duk lokacin da yazo wani taro ko maukibi sai suki su barshi ya shiga idan ma ya shigo sai su jefe shaidani, haka suka dinga yiwa dan banza daga karshe dayaga uwar bari da kansa yaje ya bawa halifa Qaribu hakuri akayi salhu tun daga lokacin abu ya danyi shiru,
.
Sai yanzu ya tsiro da wani iskancin, yana zagin Halifa qaribullah, dama tun asali kasancewarsa mutum mai neman Suna kota halin qaqa, amman hakan yaki samuwa yasa yake cin zarafi da cin mutuncin mutane sai kaji shi yana zagin babban malami wanda ya haife ya haife shi,
.
haka ya koma ta6o 'yan siyasa wanda duk gomnatin da take kai to sai yayi ta zaginta kenan har sai an bashi wani abun, misali lokacin mulkin kwankwaso na farko haka ya dinga bi yana zagin kwankwaso har sai da kwankwaso ya bashi fili a gwale filin mushe, wanda yanzu haka a cikin filin yayi gidansa yayi masallacin juma'a filin ma hakkin mutane, lokacin da kwankwaso ya tafi shekarau yazo sai ya koma 6angaren shekarau yana masa jagaliya da yaga shekarau baya bukatar tafiya da 'yan jagaliya irinsu sai ya dinga zagin shekarau har yake cewa idan yabi shekarau to shi dan zina ne, ana nan sai malam shekarau yayi masa wani babban Alkhairi wanda ya fito yace duk duniya ibrahim masu girma guda uku ne, da Annabi ibrahim da ibrahim inyass da ibrahim shekarau, lokacin da kwankwaso ya dawo be tafi dashi ba sai ya koma zagin kwankwaso ko lokacin da kwankwaso ya ta6a Annabi S.A.W sai ya dinga zagin kwankwaso har yace dashi ya zama kafiri, haka ya tara mutanensa har ya dauki sulke da kwalkwali ya saka a jikinsa , ya umarci 'yan jagaliyar yaransa suka rike makamai suka fito gari suna zanga zanga, amman yadda zakasan munafiki ne sai gashi lokacin da yake wa 'yan tijjaniya raddi yana siffanta Muhammadu Rabi'u kwankwaso da mai kishin musulunci,
.
Ba 'yan siyasa kadai ba, tuntuni shine yau ya ta6o 'yan izala gobe kaji ya ta6o 'yan tijjaniyya jibi ya ta6o 'yan qadiriya ko wani malami wanda bashi da dariqa, tun mutane suna biye masa har suka gane manufarsa suka gane cewa yana fama da ta6in hankali ta yaya zasu tsaya suna rigima da mahaukaci sai duk suka kyale karen yaje yayi ta haushinsa shi kadai, daya ga haka sai ya canza dabara akan ya samu masoya wanda zai dinga damfararsu 'yan kudaden su, haka yayi ya dinga tara karatu da sunan kishin Annabi da soyayyarsa nan ko babu abinda yake koyawa sai jahilci da dure duren ashariya, Kunji AMIRUL FASIKINA HUJJATUL JAHILINA kenan,
.
Koda matasan suka fuskanci babu wata tsiya na karatu da ake karuwa da Abdun jabberun sai duk suka dinga watsewa suna karewa kamar hatsin guziri, daya fuskanci neman Sunan dayake har yanzu a kano ba'asan da wani Abdun jabberun ba, wanda ko a gwale filin mushe babu wanda yasan dashi, kuma gashi na cefane yana gagararsa sai ya tsiro da wani iskanci da zindikanci na zagin sahabban Annabi inda yaje ya kar6o kwangilar kudi wajen Iro jakin zariya L.A don ya samu magoya baya, lokacin daya fara zagin sahabbai irinsu sayyadi Mu'awiya A,S yana kawo hadisai ta karfin tuwo yana juya musu ma'ana malaman Sunnah sun zabura suna mayar masa da raddi wanda shi dama abinda yake so kenan ayi ta zancensa yayi suna a san dashi, bayan lokacin da malam Alqasim yayi buji buji dashi akan littafinsa muqaddimatul Khaziba, haka aka dinga fama dashi akan yazo a zauna ayi muqabala akan wannan mas'alar ta fi'atul bagiya, amman hakan yaki yuyuwa kullum ya zauna sai dai dure duren ashariya da tsine tsine da karya da cika baki da alfhari da ihu da kowayee, a haka yanzu zindiqancin nasa da iskancin nasa har yazo ya fara zaginsu sayyadi Abubakar yana karyatashi akan hadisin gadon Annabi, yana zagin sayyadi usman akan wai azzalumi ne a lokacin mulkinsa, yanzu da malaman Sunna suka gane cewar bamagujen dan shi'ar yanada ta6in hankali sai duk suka kyale shi, don idan banda me ta6in hankali babu wanda zai dinga zagin sahabbai yana tuhumarsu,
.
To sai rannan mai tatsinen a wani shirmen sa dayake yi wai da sunan karatu yana karanto wani soki burutsun littafinsa mai suna MUQADDIMATUL KHAZIBAH babi mai taken LA TASABBU AS'HABI sai yazo maganar akan wani Hadisi da Halifa Qaribullah ya rawaito akan Sayyadi Ali inda ya dinga ciwa halifa Qaribullah mutunci yana fada masa maganganu na 6atanci yana cewa zasu 6ata dashi akan imami, ba don komai yake haka ba wai don kawai halifa shi yana girmama sahabban Annabi baya zaginsu sannan yana fadar gaskiya a duk inda ta dace, ko a wani haukan karatun Amirul jahilina na baya naji wai har yana cewa wai qaribu yayi maja da 'yan izala yana kiransa da nasibi,
.
To janbiri idan ma izalar qaribu ya koma ai ya gano itace gaskiya ne, tunda gaskiya yake bi, kuma kowa yayi shaidar cewa qaribu malami ne me koyar da karatu wanda yakanyi tafsiri a gidan sarki, sannan a ranaku yakan karanta sahih muslim da Algunya da ishreniyya, ba kamar ka ba wanda babu abinda ka iya sai dai ka tara mutane kayi ta dura ashariya kana tsine tsine kana sheka karya kana hauka suna ihu kana koya musu ta'addanci kana cewa su dauki makamai suje masallacin da akai rikici a baya su kashe 'yan izala, kai saboda ci da qarfi irin na mai mai tatsine sai kaje ka rubuto hadisai da ayoyi kazo kayi ta karantasu da kyar kana kuskure a cikin ayoyin, mutumin da ko haddar simini daya bashi da ita a Qur'ani, kai ko Ayar Muhammadur rasulillah ma daya karanto akwai kusa kurai a cikinta, kai Abduljbbar wallahi jahili ne na karshe, na tabbata ko fatiha ma idan zai karanta sai an ci gyaransa, ayar suratul ma'ida IN TU AZZIBHUM FA INNAHUM IBADUK WA IN TAGFIR LAHUM FA INNAKA ANTAL AZIZUL HAKIM duk da rubuto ayar yayi amman shi jahilin sai cewa yayi FA INNAKA ANTAL GAFURUR RAHIM haka farkon raddinsa ga 'yan tijjaniya yace" ALLAZINA HUM IZA ASABATHUM sai ya sake cewa" ALLAZINA IZA ASABSATUM.. Kunji chakwakiya fa, haka a wani karatunsa yana karanta tarihin matan Annabi S.A.W wai ayar da take suratul Ahzab tana gargadi ga Matan Annabi itace" INKUNTUNNA TURIDNAL HAYATUD DUNYA WAZINATAHA FATA A LAINA UMATTI U KUNNA WA USARRIH KUNNA amman jahilin wai sai yace." FATA A LAINI UDALLIQUKUNNA WA USARRIH KUNNA, kuji jahili wanda beyi karatun Qur'ani ba, sannan ayar ta suratu Ahbaz yazo kan kissar Zainab da zaid ayar itace WAMA KANA LI MU'UMINUN WALA MU'UMINATUN IZA QADALLAHU WARA SULUHU AMRAN AY YAKUNA LAHUMUL KIYARATU MIN AM RIHIM WAYAY YA'ASILLAH WARA SULAHU FAQAD DALLA DALALAN MUBINA amman kasgin jahilin sai yace" FAQAD DALLA DALALAN BA'IDA kunji jahili wanda beyi karatun qur'ani ba. Idan nace zan dinga kawo kuskuren wannan hanfefen sai na kawo sunfi hamsin, don ko aya daya bazai iya ba ammn ya dinga wa Qur'ani Hawan qawara.
.
To wai wannan kuhungun jahilin kasgi, wai a fadar wasu wawayen shine malami kuma wai hanferen shine jagoransu, kai godiya ta tabbata ga Allah daya saka mabiya wannan zindiqin suka kasance wawaye mahaukata, tabbas kamar yadda suke fada na yarda Amirul jahilina shine mujaddadin wawaye na wannan zamani.
.
Abdun jabbarun sai dai kayi hakuri, na gaba yayi gaba na baya sai labari, halifa qaribullah yayi maka nisan da har abada bazaka ta6a kamo koda farcensa saba, sai dai ka cigaba da haukanka da zagin nasa idan bakayi wasa ba hassada itace zata sheke ka har lahira, kuma ko shi Halifa Qaribun yasan kanada matsalar kwakwalwa, wanda ya kamata yasan yadda za'ayi a kaika dawanau tun kafin haukan naka yakai ka fara zagin annabawa kana tuhumarsu, abduljabbar nidai ina maka Addu'ar Allah ya baka lafiya ya rabaka da wannan cutar ta ta6in hankali da take damunka, su kuma jahilan da suke biye maka. Allah ya ganar dasu su fara zuwa makaranta suy karatu, don babu wani mai ilmi da hankalin da zai dauki wannan galmashoran mai dure duren ashariya da zagin sahabban Annabi wai da sunan malami.
.
Tofah dama ance duk yadda akai da jaki dai yaci kara, yanzu gaskiyar nan dana fada fa sai ka samu wasu jakunan sun fara tunkuyi koh? To jakunan kogo ayi ta tunkuyi lafiya, nidai babu jakin daya isa ya tunkuye ni na juya nace zan rama, ko shi kansa babban jakin naku na kogo be isa balle wasu karnukan farauta, saboda haka 'ya'yan mutu'a. Karnukan farauta haihuwar mutu'a kuy ta haushi lafiya.
.
Har yau dai
.
Angom Fatima ne Abban Sadiq
.
I.A.I

Back to posts
Comments:
[2016-02-24 12:46:57] Moh'd B. Ussaini :

To Maza Kaje Ka Tuba Domin Kayi Karya Gami Da Hahilci Bataimiye

[2016-07-01 13:33:04] ANAS AMEEN :

ALLAH YA SAWAKE AMEEN.

[2016-05-12 10:18:42] ummu aisha :

SLM

[2016-07-24 11:41:23] Aminu Rabiu Garun Gudinya Babura :

Ya Allah kaganar damu gaskiya katseratar da diga diganmu daga saba maka amin

[2016-07-30 09:45:55] MHD SANI :

Allah yasaka wa abduljabbar anyi masa kage kuma baze yafeba

[2016-09-16 20:21:32] ibrahimaliyusumaila@gmail.com :

kai arasa wanda za aiwa sharri sai abduljabbar

[2016-08-28 13:57:17] Shamsuddeen lawal anchau :

Tofa!

[2018-02-07 06:24:04] Zaharaddeen m.abubakar deen :

to allah yaimana jagora amin mudai sunnah sak.


UNDER MAINTENANCE

Share|

Kaima shiga a tattauna da kai
* No boards.

Online: Guests: 1


→Ra'ayin jama'a game damu

 IDAN KANA BUKATAR A TALLATA MAKA HAJAR KA A WANNAN SHAFIN DA SAURAN SHAFUKAN MU KANA IYA TUNTUBAR MU TA WADANNAN HANYOYIN KAMAR HAKA:


Email: bjournalist55@hotmail.com

Phone No: 09035830253

Facebook: Basheer Journalist Sharfadi

Address: Ittihad Computer Centre,  No 92 Daneji Kano


MAI TALLA SHI KE DA RIBA


*Bayanan ka*
Browser din da ka hawo Mozilla

Kasar da kake United States

Adadin Maziyarta 246309

Adadin Wadanda Sukayi Comment 65691

A Wadanda Suka Shiga Tattaunawar Mu 54


Follow @bjournalist55
→Yi Adding Dina Ta Facebook
→Yi Like Na Dakarun Sunnah Page
→Yi Like Dina Ta Facebook

*Shafuka Masu Alaka Da Mu*

→Basheer Sharfadi wordpress
Basheer Sharfadi Blog Spot
UP
→Home

Basheer Journalist Sharfadi (Abu Hafsah)
ISLAMIC DATE
  • phpimg2.php?it&ic=yellow



  • Click to Sms
    Click to Call


    Basheer journalist sharfadi3
    Coollogo com-1281358